Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 36

Sponsored links

“Koma waye I’ll surely get you! Yanzu dama ba Dad bane yayi kidnapping dina ba?,God bless the unknown girl,da badan ke ba da yanzu ina chan thinking Dad ne yayi kidnapping dina,ze kuma sakeni at any time,ashe kasheni ake kokarin yi,Allah yasa inganki in fadamiki kin taimakeni”…..

Ya fada yana daukan bindiga daya sannan ya fita daga parlourn……

Yana zuwa get me gadi ya taso da sauri,buga masa bindigar dake hannunsa yayi,nan da nan me gadi ya zube a gurin,bude get din yayi ya fita a guje…..

Gudu ya shigayi ganin isolated area ne,har Allah ya taimakesa ya karaso titi,motoci ya shiga tsaidawa amma duk wanda ya tsayar sai suki tsayawa ganinsa da bindaga gashi ba kayan yan sanda ko sojoji a jikinsa,yana cikin wannan halin ya hangosu daga chan nisa sun tawo a guje……

Tsayawa yayi a tsakiyar titi yanda dole a tsaya mishi…..

Wani uban burki ta taka saura kadan tabi ta kansa,ita sam bata lura da mutum a tsaye ba….

Bude motar yayi ya shiga ganin sun kusa karasowa batareda ya kalli me driving din ba yace

“Dan Allah ja mu tafi,kasheni suke sanyi”…..

Taka motar tayi a guje ta yanki wata hanya sannan ta nufi gidan alhaji ganin yafi kusa da nan…….

Duk da irin gudun da take shekawa hankalinta nakan tukin sosai,saboda yanda take over speeding yasa bata bin hanyar da mutane kebi sosai koda it takes following a long way ne….. Daga sama,kamar wacce aka kwace steering a hannunta taji motar ta kwace mata,daganan bata kara sanin meya faru ba……

 

Tinda aka kirata a waya aka sanar mata me wayar yayi accident kasancewarta last person data kirashi,gashi takira har sau uku,taji komai baya mata dadi,ta rasa Deen wani kalan yaro ne marajin magana,badan Allah yana karesa ba da yanzu ya dade da mutuwa,koda yake dole sai lokacin mutum yayi zai mutu,if she can recall ce mata yayi baya abuja,sai gashi an kirata tazo ‘Nisa Premier Hospital’ anyi accident dame wayar……

Tinda tazo hospital din take kuka ganin doctors din sunki cewa komai sai kai kawo kawai sukeyi,itama kasa zama tayi ta dinga zagaye gurin……

 

Tana cikin wannan halin call ya shigo wayarta,kallon screen din tayi,ganin me kiran yasa ta dauka da sauri tana fadin

“Jamila na rasa meyasa Deen bayaji,kinganni a Nisa,kira kawai akayi wai sunyi accident shi da wata”

“ Subhanallah! Accident kuma?,I hope it’s not fatal?”…. Jamila ta fada on the other side

“I don’t even know,tinda nazo Doctors din basu ce komai ba,sun dai cemin I should calm down”….

 

“Toh shidawa sukayi accident din,naji kince da wata?”

 

“Haka naji fah,I was shocked,bansan wacece ba wallahi”…..

 

“Oh Allah,to Allah ya tashi kafadunsu duka,harna tausaya musu wlh”….

 

“Ameen” Ta fada jin tadan samun relief,dama ance ‘a problem shared is a problem solved’….

 

“Ai banga ta zama ba,I’ll be on my way tomorrow Insha Allah”…..

 

“ Toh Allah ya kaimu,tinda kin guji Nigeria,sai irin wannan dalilan ke kawo ki”….

 

“Hmmm mubar zancennan pls,I’ll call you later”…. Jamila ta fada tana kashe wayar…..

 

Tsaye khaleel da sameer suke a gaban burnt building din fatima zainab,idan akwai abinda yafi shock toh khaleel yashiga,he couldn’t believe what his eyes just saw,like how can someone be this wicked?… Anya wasu suna tinanin kiyama kuwa?, Yanzu akwai wanda ze iya kona mutum dama?,shi besan tsanar da mama take yiwa abun sansa ya kai hakaba,gsky baze kyale ba dan in aka cigaba da tafiya a haka tabbas wataran saidai a kirasa ace masa fatima zainab ta mutu,so dole ya dau mataki……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button