Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 27

Sponsored links

Zaro wayarsa yayi ya sake gwada number Deen,cikin ikon Allah ko sai gata tana ringing amma harta katse baa dauka ba,sake gwadawa yayi ko Allah zesa a dace,kamar a mafarki ko yaga andaga wayar……

 

“Who is disturbing my sleep” Deen ya fada daga daya bangaran dan daga wayar kawai yayi batareda ya duba suna ba….

 

“ Amma dai wallahi kaji tsoron Allah Deen,muna nan a cikin tashin hankali muna nemanka,kai ashe kanachan hankali kwance har complain kake an dame ka”…. Sameer ya fada rai a bace ganin ashe Deen dinma yana lafiya

 

Jin muryar sameer yasashi cewa “Bangane kuna cikin tashin hankali ba, kai ba mun aikaka UK ba,toh meye hadinka da abinda ke faruwa a naija?”……

“Dude nashigo fa,tin jiya nashigo nake ta nemanka harji nayi kamar kafi komai wuyar gani a duniyar nan,dan iska ayita kiran wayarka kuma baka dagawa,nafi one week ina kiranka fah”……

 

Dariya Deen yayi yace “Ta ina zan iya daga waya,ina wata farauta,gashi nima an farautoni ansamin takunkumi,amma a sannu zan nuna musu ni din”?

“Ban gane kana farauta ba?Kodai ka fara biye biyen mata ne bamu sani ba?”….

“A’a ya’yan shegu nafara tarawa,idan na gama zan tattarosu in kawo muku”….

“Kai mutumina meyayi zafi haka,ya kamata dai ka chanja hali dan kanasa mom da dad a cikin damuwa”… Sameer ya fada yana dariya,samun Deen dayayi a waya yasasa jin kamar bashi da wata damuwa…….

“Kai bar mom da dad su suke damun kansu,I’m not a kid for God’s sake!”…..

“Toh munji,yanzu kana ina?,there’s something I really want to discuss with you?”…..Sameer ya fada on a serious note

“Kai sanin inda nake yanzu hadari ne a gareka,let’s discuss through phone okay?”….

Numfasawa sameer yayi da yakejin soyayyar fatima zainab ta dirar masa lokaci daya yace”I’m in love”…

Fashewa da dariya Deen yayi yace “sai kamin bayanin kaine ka fara biye biyen matan shine kake going through corners”…

“I’m so damn serious bro”…..

 

“Toh inform her mana,ya kana abu haka kamar wani coward”……

 

“Ba haka bane,the problem is bansan ‘WACECE ITA’ ba…..

 

Saida gaban Deen yafadi jin hakan,ya dai daure yace “How can you fall in love with someone you don’t know?”….

 

“I’ve seen her before,but the issue is khaleel ma yana santa”….

 

A take ran Deen ya baci jin yarinyar ma wai su biyu suke so,tsaki yaja yace “Kaji wani shirme,ya zaayi ace kana takara da wanchan gayen akan mace,gsky ba girmanka bane,wai ba kacemin yanada budurwa bama,toh wani nonsense ne yasashi son abinda kakeso”…..

 

“Sunyi breakup da waccan yarinyar ne,shine dan yaga inason wannan yace shima yana so”…..

Tsaki Deen ya karaja yana fadin”Ni wlh takaici kuke bani daga kai harshi,who is she da zakuna irin haka akanta,kilama ba wata abar azo a gani bace,ga mata nan birjik sai wacce ka zaba,kabar masa kawai dan ba girmanka bane takara dashi”…..

 

“Naso inyi hakan but I love her so much,har wani cika baki yake wai it’s a game muga wanda zeyi winning,kaga idan na hakura sai ya dauka yayi defeating dina ya renani”…..

 

“Oh haka ma yace?,shidin banza,barshi ze san bashi da wayo,na kuma maka alkawarin saikayi winning game din,dole ya hakura ya bar maka,mark my words!”………

 

Wani mashahurin farin ciki ne ya lullube sameer,dama abinda yake jira kenan yaji,yasan kuma tinda Deen ya masa alkawari to tabbas ze cikamasa dan shi baya saba alkawari!!……

 

Parking motar yayi a parking space din gidan ya fito da sauri ya budemata kamar yadda ya saba,fitowa tayi a hankali ta nufi ciki,karo sukayi da mama da fitowarta kenan daga sashen alhaji….. Fatima zainab bata wani yi mamakin ganinta ba dan tasan dama bazata hakura da alhaji ba…..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button