Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 41

Sponsored links

Kuka takeyi sosai tana ganin abun kamar almara,ace wai ita alhaji zesa a kama?, a lokacin daya fita daga part dinta dariya tayitayi dan tasan asirin data masa bai isa ace ya sakesa ba wallahi,sai kawai ta cigaba da harkokin gabanta kamar komai bai faru ba,tuno da alwashin fatima zainab yasa cikinta ya kada,mikewa tayi da sauri ta nufi toilet,sai kuma ta dawo ta zauna tana bawa kanta assurance din ba abinda fatima zainab zata iyayi tinda tasan ta gama da alhaji,zama tayi ta dora kafa daya kan daya sannan ta kunna tv……

 

Tana nan a kishingide kamar daga sama taji an daki kofar part dinta,kafin ma ta motsa wasu kattin mata suka baibayeta alhaji na biye dasu,a take ya basu umarnin suyi arresting dinta, ba bata lokaci suka aiwatar da umarninsa…

Su husnah najin alamun yan sanda suka fito da sauri,turus sukayi ganin daddy ne da kansa yasa a kama mamansu,hakuri suka shiga bashi amma ko kulasu beyiba dan sam baya cikin nitsuwarsa, shikadai yasan mutuwar Fatima Zainab abinda ze haifar masa…..

 

Basu nufi ko ina da mama ba sai police station,abu kamar almara sai gashi an saka mama a cell ana jibgarta akan ta amsa lefin ita ta kona fatima zainab harta mutu sannan ta fito musu da gawarta…

 

Ba karamin fita hayyaci mama tayi ba,har takai ta kawo bata gani sosai,ganin suna neman hallakata yasa tayi accepting ita ta kona ta amma batasan inda gawar fatima zainab yake ba,jibgarta suka cigaba dayi wai saita amince zata nuna musu gawar……..

Babu irin neman dabe yiwa fatima zainab a gidannan ba amma shiru kamar wacce ta bace,gajiya yayi ya hakura ya dawo part dinsa ransa fess ko banza ya san ya kullawa mama kullalliya,shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi karami saboda wataran kai zaka rufta ciki,ita yanzu tanaji tana gani tasan fatima zainab bata kone ba amma shedu duk sun nuna ta kone kuma ba yanda ta iya…….

 

Shigowarsa part dinsa yaji karar motar yan sanda,ko dar be jiba dan yasan mama akazo kamawa and she deserves it,saima zaman tinanin inda fatima zainab taje yakeyi, yasan dai da kafafuwanta ta fita kuma zata dawo…..

Sameer ne ya fito daga bedroom din khaleel da sauri yace

“Khal ba karar motar yan sanda nakeji a gidannan ba? I hope all is well?”….

Daga kai kawai khaleel yayi sannan yace

“Yes,karka damu,it’s nothing serious”…..

“Bangane it’s nothing serious ba? Kasan dai nima kamar family nake, ko haryanzu kanajin haushina ne da bazaka fadamin ba?”…….

Sameer ya fada da fuskar rashin jindadi

 

“Nop sam,you’re a family of course,kuma duk abunda ya faru ya wuce,nasan you don’t mean it,kawai long story ne!”…..

Khaleel ya fada dan harga Allah har cikin zuciyarsa ya yadda da sameer…….

“Toh ka fadamin meyake faruwa pls,wa kuma sukazo kamawa?”……

“Well mama aka kama for an attempted murder that only me knows it’s attempted,but everyone thought it’s committed already,can you believe wifey taso konawa?”…….

Zaro ido sameer yayi ya dafe kirji jin wani mugun abu daya taso masa da khaleel yace wifey,da sauri ya maze yace

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button