Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 178

Sponsored links

Yayanta ne ya katseta da fadin, “Sai hakuri Bushirat, kuka baya daya da ga cikin mafita, ki daure ki sanar mana abinda ke faruwa domin musan makamar rikewa wajen yimiki magani. Shin garin aya wadan nan abubuwan masu alaka da aljanu ke zagaye da ke? Minene kuka sani ke da Zawjata-almilk da mu bamu sani ba? Mi kuke boye mana da Jasrah har taji kuna sa’insa a shekaran jiya?”.

Idanu Tajwar Eshaan ya bude da sauri ya zubama Iffah idanunsa da suka kada jazur, amma ita sam taki kallonsa ga fuskarta kicin-kicin kamar yanda tashin take, Malikat Bushirat kam kuka ta sake fashewa da shi. Kafin a hankali ta motsa lips dinta wajen fadin, “Ni na jama kaina Akhi. Ni na siyama kaina komai. Komai kuma ya farane a dalilin HAIHUWA. a dalilin neman haihuwa da tsananin bukatar samuwarta. Buri da kwadayin gani da son haihuwar magaji shine silar labarin zamana a wanna masarautar da ma duk abinda na aikata a tsahon shekaru arba’in da a yau nake girbar abinda na shuka tun daga nan duniya……..

Duk wanda ya sanni tun a kuruciya yasan ni yarinya ce mai yawn kirinki, nayi rashinji matuka, dan a fada biyar da za’ai dani cikin yara to da wahala ka samu daya a ciki da nake da gaskiya. Tun ina karamata na

 

kasance mutum mai son gain kowa ya zama a karkashin ikona. Hakan yasa ban yarda da abota da wanda muke shekaru daya ba ko ko sukafi gidanmu arziki. Duk kawayena na girmesu, na kuma fisu wayo, gidanmu kuma yafi nasu komai. Hakan yasa dole sukemun biyayya da bin abinda nake so koda ace su basa son sa. Mahaifiyarmu na yawan mun fada akan wannan halayyar, hakama mahaifinmu. Nakan nuna naji na dan wani lokaci amma da kura ta lafa sai na koma gidan jiya. A haka na taso da wannan rayuwar har girma. Kowa yasan Bushirat boss ce a cikin kawaye, idan kuma kana son ka zauna lafiya tilas ne kamun biyayya. Gidanmu gidane na manyan mutane, masu ilimi kuma Alhamdullah munada dukiya. Ina alfahari da hakan, amma kuma inada buri na kai da kai. Kasancewata kyakykyawa nayi samari kala-kala, duk da dokar mahaifinmu shike zabama kowace yarinya a gidan mu miji, a nawa bangaren babu wannan ra’ayin. Sai dai na shanye ban taba sanarma kowa ba. Duk wanda zai zo gurina sai nayi duk yanda zanyi na bibiyi nasabarsa da nauyin aljihunsa, idan ka kasance baka da ko sisi zan tattaraka na watsar, tare da kashedi mai girma na ka fita a hanyata. Wasu sukan barni cikin sauki, wasu ko saina yi jan ido kona hada musu tuggu a wajen yayuna sun kore su. A haka na kammala karatuna na boko, wanda na taso naga anayi a gidanmu kam shima na samu gwargwadon iko wat ilimin addini. Sai dai sam bana maida hankali garesa, dan ni salla ma sai mahifiyarmu tamun jan ido. Da girmana da hankalina nasha daukar azumi na karya batare da an sani ba, kawai dan inajin wata kaina sama can. A haka wata rana naji Akhi kazo ma da baba batun wai Miran Haysam mai jiran gadon karagar mulkin Shahan-shan ya baka zabin nema masa matar aure. Kai kuma kayi tunanin dubawa a cikin yarn gidanmu amma har yanzu baka gama yanke hukunci tsakanin ni da Hubba ba. Abinda ya girgizani shine, jin Abie kai tsaye ya furta (“Uhm-uhm Muhammad, ajiye maganar Bushirat gefe, bata jin magana, sakata a babban gida irin wannan zai iya zubar mana da kimar mu da nuna gazawar tarbiyyar da muka baku. Yarinyace mai kaudi da hange, ina tsoron al’amarinta.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button