Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 22

Sponsored links

Kamar wacce aka tasa daga bacci haka taji,sai a sannan taga shashancin datayi,ace tana tsaye namiji rungume da ita a haka ta kasa taking action saima wani nitsuwa datayi,batayi tinanin sabon wayo datakeso ta masa zeyi working out ba,karatun ta kama cikin daddadar muryarta da dole mutum ya tsaya ya saurara….. Take ko taga ya nitsu ya saki nasa karatun yana sauraran nata,and at that moment she manipulated him………..

Zaune yake a office dinsa,kallo daya zaka masa kasan akwai abunda yake damunsa,har dan rama yayi a wannan kwanakin,he has never been this bothered all his life,ga ayyuka sun balakin masa yawa shiyasa ko fita nan da chan baya iyawa,sai abubuwan suka taru suka masa yawa,gashi kiran duniya yayiwa khaleel amma yaki dagawa,a rana saiya kira khaleel kusan sau 30 amma shiru baa picking,ya rasa waze gayawa damuwarsa yaji sanyi a ransa,Deen dayake tinanin ze iya gayawa shima tin jiya yake kiran wayarsa baya dagawa…. Gabadaya dai abun duniya ya ishe Sameer….

 

Ganin zaman fa baze fisshesa ba yasa shi mikewa,ture duk wani aiki dake gabansa yayi ya fita… Motarsa ya shiga ya nufi gidan khaleel……..

 

Parking yayi a daidai cottage din khaleel,fita yayi daga motar ya nufi entrance din gidan,dogo ne sosai sameer,bashida jiki sosai amma yana da broad chest,kyakkywane san kowa kin wanda ya rasa,duk kyawunsa amma be kama kafar khaleel ba…..

 

Yafi 5mins yana knocking amma shiru ba amsa,hakanne yasa ya murda kofar,luckily ko ya sameta a bude…… Shiga yayi yana bin falon da kallo,ganin ba kowa yasashi karasawa sama ya nufi bedroom din khaleel….. Murda kofar kawai yayi ya shiga daidai fitowar khaleel daga wanka,da sauri khaleel ya koma cikin bathroom din a guje thinking fatima zainab ce ta dawo😹…… Mamaki ne ya kama Sameer ya daga murya yace “Man meye na guduwa kamar kaga dodo”……. Jin muryar sameer yasasa fitowa da sauri,yace “kai wallahi na dauka dodon ne”….

Fashewa da dariya sameer yayi yace“Ikon Allah akwai dodo a gidannan dama?,kai amma ka bada maza wallahi,jifa yanda ka zura a guje kamar mace”…

 

Karasowa inda sameer yake yayi yana fadin “bazaka kane bane wlh,kaidai kawai abar kaza cikin gashinta”… A ranshi ko cewa yake ai koda kudi bawanda zeji wannan labarin,dan shi kansa yasan ya tafka abun kunya……

 

“Kai ni duk bama wannan ba,I have a very serious case,before then meyasa baka picking calls dina?” Sameer ya tambayi khaleel yana zama bakin gado…..

 

“Wallahi bansan inda na wurga wayar bane,nima na dan shiga wani serious case ne har na batar da wayar bansani ba,amma dai yanzu Alhamdulillah everything is alright”……

“Ah toh masha Allah,ya kamata dai kayi tracking wayarka kodan hotline dinka dake ciki”

“Hakane,I’ll do that today Insha Allah,wayarma tana gidan nan nasani”…..

“Well let’s get back to issues din daya kawoni”

“Ina jinka” khaleel ya fada yana nodding….

“I saw a green snake in this house”….

Zaro ido khaleel yayi yace “Green snake kuma?”…

 

“Yes her eyes are so gorgeous,banga fuskarta ba amma nasan tabbas kyawunta me tada fitina ne,meanwhile she’s beautiful and wicked,daga gani kuma fitsararriya ce,can you believe har marina tayi kuma nakasa uttering even a word?,this is why I called her a green snake”……

Ai khaleel ji yayi gabansa ya fadi,karde karde,karfa ace Fatima zainab ce Sameer ya rikice haka akanta,amma sai ya daure yace “wai kana nufin a gidannan ka ganta,can you describe her?”

“Told you I only saw her gorgeous eyes,she’s all covered fa,harda hand gloves wlh”

“Kace she’s all covered toh how did you see her eyes?”……

“I mistakenly hit her shades,ashe da rabon zanga those attractive eyes”…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button