Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 3

Abban Sojoji Chapter 3

Sponsored links

‘Yan kame-kame ta shiga yi hankali a tashe tana wurwurga ido, ” wannan d’an daudun daga ina kuma aka samo shi?” Daya daga cikinsu ya tambaya yana kallon ta , hantar cikinta ce ta ji ta kad’a , su duka sauraren ta suke yi su ji mai zata ce?

 

Motsi ta soma yi da lips dinta alamar tana so ta ce wani abu “Amm… Amm..” Duk ta bi ta dabarbarce. Jin muryar Azumi yasa Sehrish sauke ajiyar zuciya, karasowa ta yi tana fadin “Afuwan y’an samari ban yi maku bayani game da sabon d’an aikin da aka kawo domin ya rinka taya ni aiki ba.”

Kasa kunne suka yi suna sauraron ta , dafa kafadar Sehrish ta yi tare da cewa “Sunan shi tukur daga yau zai rinka taya ni aikace aikacen cikin gidannan ,’

 

Ta kare maganar tana kallon kowannan su tabe baki yyi ba tare da sunce komai ba dama haka ta yi tsammani , don haka taci gaba da cewa “tukur bari na gabatarka maka da kowannan su saboda ka kiyayi zama dasu ,”ita dai ba ta ce komai ba saboda a rud’e take ,

 

Azumi ta soma gabatar mata da su daga na farko “Wadannan biyun da ka ke gani sune tagwaye in ka lura komai nasu iri d’aya , suna da son zolaya musamman idan abun mugunta ne sun fi auki a nan na farkon sunansa Jahan shine babba sai twin brother dinsa Ayaan”

 

Tana gama wa dasu ta matsa na kusa dasu tace “wannan kuma sunan shi Kanal yusif sarkin tsafta , bai cika son surutu ba kuma baya son kallo , na gefensa kuma shine Khaleed bai da matsala shi indai za ayi masa abunda ya ke so ba tare da ya tambaya ba ,

Duk Sehrish na sauraron wannan bayanin na azmi , bayan ta kammala da na hannun damarta ta koma other side din taci gaba da cewa “wannan Junaid kenan sarkin murmushi, duk yadda za’a bata mai rai baya fushi sai in an kuresa , yana da son wasa faran faran da jama’a, burinsa a bashi kulawa a bangaren ci kuwa ba’a magana ,” karasa maganar tayi tana y’ar dariya , shima dariyar yake yi haka zalika wasu daga cikinsu sun d’an murmusa ,

 

Sehrish tagane sa shine wanda ta fara zuba ma abinci mai kyakkyawan murmushin nan

 

“n6a kusa da shi kuma fawan kusan halinsu daya da Junaid , sai jabir da irfan basu da matsala in dai ba tsokanarsu akayi ba.”

Murmushi sehrish tayi taji dadin wannan gabatarwar , sai dai ranta na bata cewa wadannan kananun ne , akwai sauran mutun goma daga cikin sojojin da basa nan , su kuma koya zasu kasance !?

 

A tare da azmi suka yi saving dinsu abincin har suka kammala kowannnen su ya kama hanyar makwancinsa , tattara plates din da kulolin sukayi a tare suka kakkauda komai izuwa ma’ajiyarsa ,

 

daga nan sehrish tayi ma azmi sallama ta koma bedroom dinta , tana mai jin dadin fara kasancewarta a wannan awesome family din Babbar damuwarta shine , da tazo a matsayin namiji a maimakon mace batasan ya abun zai kasance ba ranar da asirin ta ya tonu.

Tunda samu gadon nan ta haye ta soma minshari bata kara sanin meke wakana ba sai da tajiyo kwankwasar kopar da azumi take yi mata ,

 

A firgice ta farka tana neman mayafin da take nad’e kanta da shi , can ta hangosa kasa ashe anan tayi wurgi dashi, daukowa tayi ta hanzarta daure kanta dashi, sannan ta tashi ta nufi kofan ta bude mata, fara’a azmi ta sakar mata ” am sorry na Katse maka bacci ko naga ana kiran sallah ne raina ya bani baka yi ba nasan an sha gajiyar tafiya ga aikin da mukayi da dare ,”

 

Cikin y’ake sehrish tace “a’a wlh naji dadi da ki ka tashe ni saboda banyi sallah ba amma ynx zanje na yi,

 

Azumi tace “ok in ka kammala karfe 7 ka fito akwai aikin breakfast na jiran mu” reeshi ta amsa da “toh ” sa’annan tajuya ciki”

Cikin sauri ta shiga toilet, sai da tafara cire gashin bakin da aka sa mata ta tura sa cikin aljihun wandon ta, sannan taje bakin fanfo ta daura alwala , ta fito tana yarfa hannun ta, hijabi ta dauko ta zura sannan ta shimfid’a kafet, ta soma yin sallar,

 

Bayan ta kammala sallar wata irin hamma ta rinka ji, ga bacci bai ishe ta ba ga kuma yunwa don jiya da daddare bata nemi abincin ba gashi available

 

Agogon dake manne jikin bango ta kalla akwai sauran lokaci don haka sai ta baje saman sallayar taci gaba sharar bacci, ba ita ta tashi ba sai wurin karfe 9 na safe hankali a tashi ta wartsake, ganin cewa wannan ce rana ta biyu da fara aikinta gashi zata fara bada matsala, cikin hanzari ta cire hijab dinta ta hada da kafet din sallan ta adana su a saman gadonta, sannan ta zaro gashin bakinta da take likawa ta manna sa a fuskarta, ta gyara nad’in mayafin kanta ta fi ce,

A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce “barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,”

 

Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce ” karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan”

 

Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ?

 

Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu,” azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button