Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 58

Sponsored links

Haka rikici kala kala suka dinga shiga tsakanin mami da dad, shi kuma ya dage sai ita har Allah yasa sukayi graduating akasa aurensu nan da one month, ba karamin tashin hankali mom tashiga ba lokacin da akace itama saita fito da miji a aurar dasu tare, a kuma lokacin tagane lallai san dad take dagaske, tayi kokarin bin duk yanda zatabi ta rabasu amma Allah beyi ba har takai dad ya gane ya kuma fita sabgarta gabadaya, yayita cewa mami tayi hankula da kawarta ita kuma ta nuna mishi ko zancen bataso dan mom tafi karfin kawa a gurinta saidai yar uwa, kyaleta yayi ya cigaba da shirye shiryen aurensu, babu yanda mom ta iya hakan ya sata fito da wani a cikin samarinta badan tana so ba, lefe nagani na fada dad ya kawo hakan ba karamin tadawa mom hankali ya sakeyi ba dan wanda ta aura be kama ko kafar dad a arziki ba, haka aka sha shagulgulan biki na kece raina musamman ta bangarensu mami da dad sannan aka mika ko wacce dakinta……..

 

Sosai mamaki ya kama mami da dad ganin yanda suke balakin zaman lafiya kamar basu bane koda yaushe cikin fada lokacin courtship hakan kuma baya rasa nasaba da yanda dad yake nitsar da mami akan boye sirrin gidanta ma kowa har mom, haka mom zatayita bugar ruwan cikin mami akan zamanta da dad itako tayita ce mata Alhamdulillah daga nan ba kari, ganin kamar baza tayi nasara ba ya sata hakura tajira sanda opportunity ze zo mata dan ta riga taci alwashin raba su…..

 

Wani abu daya fara dagawa mom hankali shine rashin haihuwa, ace antafi shekara biyu da aure amma shiru kakeji, ita ko mami watansu tara da aure ta samu ciki, wata tara na zagayowa kuma ta haifo santalelan yaronta son kowa kin wanda ya rasa, ranar suna yaro yaci suna Saifuddeen……..

Haka yaro ya taso cikin gata da kulawar iyayensa, gashi da farin jini da shiga rai kowa yanaso ya daukeshi, gashi kuma kyakkyawa bubulbul dashi gwanin sha’awa……

Saida Deen ya shekara biyar sannan Allah ya azurta su mom da samun haihuwa, ta haifo yar ta mace dataci sunan mahaifiyarta hameeda, sosai mami ke san hameeda har takai tace hameeda bata da wani miji sai Deen tin suna yara, haka deen da hamida suka taso cike da kaunar juna gwanin sha’awa….

 

Lokacin da deen ya kai shekara goma mom ta sake bullo da wani abu, taso tayi hakuri ta share kawai saidai zuciyarta ta kasa tinda shaidan ya riga ya buga mata ganga…. Wata kawa ta hadu da ita data zama musabbabin fara bin bokanta, aiki na farko da aka fara mata shine akan mahaifin hameeda ya zamana ko ce mishi tayi karya fita na sati haka ze zauna be fita ba, sosai taji dadin harkar ganin yanda take juya baban hameeda da komai nasa, abu na biyu data sa aka mata shine hargitsa zaman lafiyan dad da mami da ze kaisu ga rabuwa, shiru shiru taji mami batace mata koma ba, sai ta hau bugar ruwan cikinta akan babu abinda yake faruwa tsakaninta da dad ne, ita kuma mami tace babu, a lokacin kuma ta fara fuskantar chanji sosai daga gurin dad saidai sam bata bari abun ya dameta ba, in ya fara fada babu gaira ba dalili ko kulasa batayi……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button