Hausa Novels and Stories

Idon Naira 10

Sponsored links

Inna Karima ce ta kunnawa zainab din gas ta dafa mata aka Bata inda ta juye mata takai mata kafin suka kashe komai tareda rufewa itada Inna Karima kowa ya nufa makwancinsa.

Sallar ishai tayi ta kwanta take bacci ya dauketa Dan Dama ita data kwanta sai bacci sbd aikin datake wuni yi jikinta a gajiye yake Koda yaushe.

A gida akan tabarma take kwana saida maryamah tayi aure umma ta saida katifar maryamah babba ta siya mata wata Yar yololuwar katifa data gama sidewa Amma dadinta takeji ko ahakan ita,.

Ganin wannan babbar katifar baisa ta hau akai ta kwanta ba sbd gudun laifi ko zaqewa dakuma shakkar yiwa maryamah laifi da haka a kan tiles ta shimfida daddumar sallah tayi kwanciyarta har safe.

Qarfe 7 Inna Karima Tazo ta tadata suka fito Dan fara aikin gidan.

Shara tafara mai kyau

Ya goge komai cikin tsoro tsoron kada ta fasa ga jikinta dake faman Yar rawar fargabar kada tayiwa maryamah laifi da yanayin aikin.

Fes tayiwa koina saidai Kam yau saida bayanta ya amsa wahalar aikin daya bambamta Dana gidansu data saba,

Palo uku manya Manya da dakuna biyu da kitchen da corridors biyu da toilets ta share tai mopping takuma wanke Bayan goge gogen datai.

Kowanne gurin datai aikin girmane dashi Babu qaramin guri,.

Jin tayi bayanta ya riqe qyam kamar bazata iya miqewa daidaiba Amma haka ta miqe ta share babbar harabar gidan da kusan mota hudu yake dauka.

Ko data gama ayyukan tas bayanta da qugunta sun mata nauyi daqyar take iya miqewa tsaye daidai haka ta zauna kitchen taci abincinta da Inna Karima ta Bata Tana gamawa tayi wanke wanke tasake tsaftace kitchen din ta nufi dakinta

Daqyar tayi wanka ta saka kaya tazo ta Dan kwanta take baccin wahala yafara daukan kenan saiga Kiran Inna Karima akan taje ta tattaro kayan dining idan su masu gidan sun gama breakfast.

Haka ta tashi taje tattara gurin tasake gyarawa Takoma kitchen tayi Wani wanke wanken tafara Taya Inna Karima aikin abincin Rana.

Wunin ranar ma Kam Bata sake samun zama ba sallah kawai ake barin taje tayi tadawo

Da yamma ma saida takuma sharar harabar gidan sbd karatun daren da akeyi.

Da daddare data kwanta tsamin da jikinta yayi ko bacci mai dadi data saba samu Bata samuba ranar.

Washe garima duk aikin datai a jiyan haka ta maimaitashi Dan haka ranar jikinta har kasa daka yayi da zazzabi ta kwana.

Haka aikin yakasa karban jikinta kusan kwanaki hudu kullum da zazzabi take kwana Amma harta Dan fara sabo da aikin jikin ne dai bai sababa sbd aikin yafi karfin shekarunta ga makaranta har lokacin maryamah batace mata komaiba akai ita Kuma Bata cika ganintaba kota ganta bazata iya Mata magana ba sbd shakka da tsoron Mata laifi.

Idan tace tana Bata gaji da zaman gidan matuqa ba ta yi ƙarya,

don kuwa duk aikin da ta ke yi a gidan Umma bai kai nan ba sbd ko gyaran ɗakunan da take yi a can girman falukan wannan gidan na Maryamah shi ne matsayin girman ɗakunan gidan Umma kaf ɗinsu

Duka gidan dakin Alh Asad ne kawai ba itace take sharewaba Amma kaf gidan itace mai share koina ta gyara

Har aikin kitchen da Inna Karima yakamata tayi kusan duk itace take Rabi sbd Maryamah wasu lokutan tafison aikin zainab na abinci hardai na marmari.

Sati biyu da zuwanta gidan ta fara sabawa da duk wasu bautan da ta ke yi

Umma kuma a satin ta haɗa komi nata ta ɗaga zuwa Cameron bayan ta zo har gidan Maryamah sun yi sallama da juna tayiwa zainab nasihar biyayya ga Yar uwarta tareda tunatar da ita batada kowa sai su Dan haka ta zauna ta Taya Yar uwarta aikin gidanta Tunda idanma batayiba batada gurin zuwa.

Zainab ta sha kuka sosai duk da cewa babu shaƙuwa tsakaninta da Umman amma sai tafiyar nata ya ɗaga hankalinta sosai sbd koba komai tafi Jin sanyi agurin umman tun rasuwar Abbansu sbd lokuta da Dama umman na Mata wasu abubuwan kulawa sabanin maryamah dako kallon fuskar juna basayi sosai,

Kwata kwata Babu shaquwa ko kusanci ko wata qauna a tsakaninsu Dan haka takejin da umman zata taimaketa da ta tafi da ita ko bautarce ta yarda acan tayiya yi Mata har tsufa yafi Mata zaman Nan din.

Bayan tafiyar umma da sati uku maryamah tayi barin cikinta Dan haka gidan duk suka shiga damuwa musamman maigidan gabaki dayama dauketa yayi sukai tafiya wata qasar aka bar su zainab masu aiki.

Bayan tafiyarsu ne zainab tasamu Takoma makaranta shima saida aka Kira Alhaji Asad din daga makarantar Yana can suka sanar Masa ta Dena zuwa shinefa yayi waya drivern gidan na kaita wata Rana Kuma da qafa take zuwa tadawo da qafa duk nisan kuwa sbd driver ganin yakeyi Mai aikice ita Amma tasamu shigar da ake kaita makaranta da mota Dan haka Wani lokacin yake shareta ya dauki motar ya tafiyarsa nasa sabgogin.

Karatunta da aikin gidan ya taru ya hade mata gabaki daya rayuwarta Aiki ya firgitata ga kadaici,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button