Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 84

Sponsored links

“She is indifferent!”….

Mami ta fada tana bin bayanta da kallo….

“She really is! Kiga fa magana kamar ana forcing dinta, koya suke coping da ita a gida?”….

“Maybe bata da surutu ne kawai, ni kuma tashiga raina wallahi, yanda kika san ince tayi zamanta a gidannan”…..

“Ta shiga ranki ko tashiga rai na? Ji nake kamar na tafi da ita UK, jinta nake kamar baby tee wallahi”.

“Same wallahi, baby tee kam ai talkative ce”……

“Gaskiya kam, ai kwata kwata yanayinsu ba daya ba”……

“That’s true!”……

Tinda suka tafi yake zaune going so deep in thoughts, bini bini ya dago ya kalli time yana tinanin abinda sukeyi yanzu, ya sukayi da ita? Ta farka? Taci abinci? Yasan zasu tambayeta wacece ita kuma kila ta fada musu yanda yaga tana hira dasu, ga Umm da mugun siyasa sai ka saki baki kana bata labari baka sani ba, kota musu fashe fashe data farka? Lots of things dai, haka ya cigaba da tinani tinani har aka kira sallar magrib yayi alwala yayi sallah……

 

Yana idar da sallah ya dora daga inda ya tsaya, wani abune ya shiga fadomasa ya danji tsoro ya kamasa dan yasan tsap zata aikata, kar taje ta gudu daga gidan a sake kai mata hari dan yasan sameer baze bar kasar ba idan ya koma beganta a gidan ba..

 

Ji yayi inaaa baze iya zama ba dole sai yaje ya ganta koya samu nitsuwa, besha wahala wahala wajan gano hanyar dazebi ya fita ba, dama ya dauko abun a mota, wani powder ne dayake sumar da mutane instantly kamar dai wanda ya sakawa wa’yenda sukayi kidnapping dinsa, shine kuma wanda sameer ya shakawa fatima zainab…….

 

Saida ya bari dare ya karayi yanda yasan su Mami sunyi bacci dan suna bacci da wuri, yanda ze samu yaje ya ganta batareda sun sani ba tinda sunfara tinanin sonta yake shida bata ishesa kallo ba kawai tausayinta yake ganin mutane dayawa na harinta, bacin wannan he has nothing to do with her…..

 

Fitowa yayi ya labe ya musu barin powder kamar yanda ya tsara, a take suka sume duka kuma…

 

Fita yayi da sauri ya nufi inda yabar motar sameer dama key din na jikinsa, shiga yayi me gadi da besan wainar da ake toyawa ba ya bude masa gate batareda yasan waye a ciki ba….

Har karfe tara juyi takeyi a gado ta kasa bacci dukda tafi awa daya da cemusu zatayi bacci, sai yanzu take dana sani da bata cemusu zata tafi ba su kuma basu nuna mata komai akan hakan ba, yanzu gashi dare yayi babu abunda yake sata bacci a kusa, gabadaya sai taji kanta na mugun mata ciwo, lokaci daya idonta ya rikide yayi ja jijiyoyin kanta suka tashi, mikewa tayi da sauri tana tinanin mafita dan dole sai tasha abinnan inba hakaba babu kwanciyar hankali komai kuma ze iya biyowa baya, yanke shawarar ta gudu daga gidan tayi deep down tanajin batasan rabuwa dasu amma ina gwara ta tafi ta nemi mafita da tazo tana dana sani daga baya……

Cikin sanda ta fita parlour taga ko ina tsit alamun duk yan gidan sun kwanta, dadi taji tana mamakin yanda suke bacci da wuri kamar ita bada wurin take bacci ba…….

Me gadi ne ya taso da sauri yace;

“Hajiya wani abun zaa siyo miki ne, ga isa shi ake aika”….

“No, sako zan karba yanzu zan dawo”…

“Toh shikenan hajiya a dawo lafiya”…

Batace komai ba ya bude mata gate ta fita….

Tafiya ta hau yi batareda tasan inda ta nufa ba har tazo wani pharmacy dake few walks away from the house ta shiga, ta masa bayanin abinda takeso ya bata, daukowa yayi ya mika mata,ta karba tace;

“Zan kawo maka kudin gobe”…..

Baya bada bashi amma sai yaji ta masa kwarjini sosai da har ya kasa mata musu yace;

“Ba matsala hajiya”……

A 360 yake driving saida ya karaso street din su mami sannan yayi slowing down kasancewarsa highly secured area, yanzu sai a taresa ana interrogating dinsa…..

 

Kamar ance juya yaga kamar ita yake hangowa a cikin pharmacy din dake dan nesa da gidan mami, parking yayi a daidai gaban pharmacy din though bashida tabbacin itace, fitowa yayi ya jingina da motar yana jiran ta fito yagani inba ita bace ya karasa gidan Mami…….

Tinda ta fito daga pharmacy din ya gane itace hakan yasa ya gyara tsayuwarsa tambayoyi fal ransa kan abinda ya fito da ita a darennan…..

Itama tun kafin ta karaso ta hangosa, saida taji gabanta ya fadi batasan dalili ba, kodai ganin ya hadarai ne oho, ta kuma samu kanta da boye abinda ke hannunta a cikin hijabi, itama ta hade rai tana jin dama akwai wata hanyar da zata bi ta gudu…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button