Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 83

Sponsored links

Komai Iffah bata iya tace ba, sai dai Daneen Ammarah na iya jiyo sautin murmushinta harta gama kwarzantata.

“Mamy dama na kiraki ne na shaida miki ina ɗan son na fito zama waje ɗayan ya isheni, daga nan sai na ɗan leƙama ɗakin karatu kozan samo abin ɗebe kewa”.

“Hakan kam yana da ƙyau Ibnati. Dan haka ki shirya kawai, hadimanki na sashenki za’a sanar da su su tsumayi fitowarki”.

“Nagode Mamy, ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsohon rai mai amfani da albarka”.

Cikin jin daɗi Daneen Ammarah ta amsa da Amin tana mai saka mata albarka itama.

A yau kam Iffah ta ƙara tabbatar da tsantsar ƙarfin ikon mulkin wannan daula. Dan tunda ta baro hawa na ƙarshe hadiman sashin na Shahan-shan ke faman zubewa gabanta batare da dubi da ƙanƙantar shekarunta ba, matsayinta kawai suke kalla. Duk sai taji zuciyarta babu daɗi ganin kusan duk shekarunsu zai iya kaiwa dai-dai dana Hanash, wasu ma sun girme masa. (Nace Iffah danma Tajwar Eshaan yayi sauyi ne da matasa kikaga hakan, da har sa’an kaka da Babiy sai kin gani kuwa). Kamar yanda Daneen Ammarah ta faɗa tako samu hadiman na zaman jiranta. Ta gane hakanne ta hanyar zuwa da sukai suka zube a gabanta da sanar mata matsayinsu. Batare da damuwa ba duk ta bisu da kallo, su biyar ne cif kuma duk yara ƴammata matasa, za’a iya samun sa’aninta dama wanda suka girme mata kamar su Fariha.

“Ina buƙatar zuwa books room ne akwai wani tsari akan hakan?”.

Da sauri ƴar babbar dake ta gabanta sosai ta girgiza kai. “Ga Zawjata-almilk babu wani dokar yin hakan ALLAH ya ƙara miki lafiya”.

“Okay zamu iya tafiya”.

Iffah ta amsa mata kai tsaye. Hadima ɗaya ce tai gaba sosai Iffah na biye da ita cikin takunta na nutsuwa da wasu kan iya gani su fassara da abinda zuciyarsu ta basu. Bayanta Hadimai huɗu na biye da ita cikin taka tsantsan da nuna girma da ƙarfin ikonta a bayyane……

Duk ta inda suka gitta kwarjininta dake ɓoye shekarunta kansa a bata girma irin wanda ya dace ga Zawjata-almilk da suka isa a masarautar. Hadimai kam sai zubewa suke bisa gwiwunsu sakamakon sanarwar da ɗan kazagin da Iffah bata farga da shi ba sai da suka fara tafiya taji shelanta tahowarta da yake yi. A yau kam ta ƙara jinjinama girman wannan katafariyar masarauta mai

abubuwan kallo matuƙa. Sai dai ga mai kallo bazai taɓa fahimtar hakanba a yanda take faman basarwa kai kace ita ɗin tun fil’azal jinin sarauta ce. Ba wani nisa bane zuwa books room ɗin, hakan ya sakasu isowa cikin ƙanƙanin lokaci dan ma tafiya ce ta ƙasaita….

Cikin ƙankanin lokaci labarin fitowar Zawjata-almilk ya karaɗe masarautar. Hadimai ƴan leƙen asiri dake watse ta ko’ina sun gama kai labari ga iyayen gidansu. Da yawa mamaki ya kamasu tare da gane lallai yarinyar tazo da tsageranci. Inba tsageranci ba wace Zawjata-almilk ce ta taɓa fitowa bayan kaita turakar Shahan-shan da kwana ɗaya kacal. Wasu kuma kai tsaye fassara wannan fita suke da gatsali, acewarsu Iffah nason tabbatar musu tafi ƙarfin iyawarsu, ƙarfin ikon su kuma ba komai bane dan ta gagaresu.

★Malikat Bushirat kanta isowar wannan labari a kunenta sai da tai wani tsamm na nuna mamaki, sai dai bata ce uffan ba kasancewarta mace mai tsananin jin kai da izza. Tana son Iffah, kuma ƙarfin halin yarinyar na kawatar da ita. Sai dai hakan ba yana nufin zata dama damawarta ne a yanda taso ba ko ƙetare tsarin zama a masarautar musamman ga Zawjata-almilk irinta da ƙa’ida komai sai da umarnin Malikat zatayi sa. (Kamar dai ita dake mahaifiya ga Tajwar Eshaan. A ƙa’ida dole komi Iffah zatayi sai ta nema izinin mahaifiyarsa kafin ta aiwatar). Jin al’amarin ya cigaba da caccakar zuciyarta ta sallami duk hadimanta. Kamar ƙiftawar ido suka ɓace kuwa. Rai a ɓace ta ɗaga waya tai kiran Jasrah da ita bama tasan wainar da ake toyawa a masarautar ba kasancewar a ɗan tsakanin nan tana fama da laulayin ciki ne sama-sama.

Duk da a halin rashin jin daɗi da take ciki bazata iya ƙin amsa kiran ƴar uwar tata da takema kallon uwa a yanzu ba. Haka ta kimtsa cikin dauriya ta nufi sashen Malikat Bushirat ɗin. A tsaye ta sameta cikin yanayin ɓacin rai da ya kasa ɓoyuwa a kan fuskarta. Sai duk taji itama nata ran a jagule…

“Akia kina lafiya kuwa? Miya ɓata miki rai haka har fuskarki ta kasa ɓoye wa?”.

Malikat Bushirat ta zuƙa kakkaurar iska ta fesar tana mai kallon ƴar uwar tata. Cikin ɗacin murya tace, “Yarinyar nan ce”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button