Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 106

Sponsored links

Wata irin daddagewa da fashewa da kuka da Miran Arshaan yay ne ya katse mata tunaninta. Ta zubama drama din tasa ido dan ya wani daddagene ya fashe da kuka yana duban Miran Jasim kai kace dada duniya har zuciyarsa ne. “Jasim! Jasim Akhi mu zakama haka? Kai da kanka zakaci amanar dan uwanmu ka zama jagoran shirya halakashi. Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un.…. Mi kake bukata ne? Miye dan uwanmu bai mana na gata ba a wannan duniyar? Ya rikemu tamkar yanda Abie (Tajwar Abdul-majeed) zai rikemu, amma mu mu kasa rike jininsa daya tilo a duniya da bashi goyon bayan mulkin da ALLAH ya daura masa. Dama na jima ina zargin kana kwadayin mulkin nan ne,ban tabbatar da hakan ba sai randa aka samu kayan tsafin daka saka a kujerar da adalin shugabanmu yake zama, kaki zuwa kuma wajen meeting da ga karshe ma bakin cikin an ganoka ka nema halaka iyalinka” ya sake fashewa da kuka.

Wata irin mahaukaciyar shaka Miran Jasim da jikinsa ya hau kakkarwa ya kaima Miran Arshaan da kyar kuwa aka bangaresa yana fadin sai ya kashe Miran Arshaan din.

rufamin asiri amma yana so muyi aiki tare. Ya dan mun maganganu dai da yawa. A ranar ya kawo min maganganu masu rudarwa, mafi girma a cikinsu nunamin video cewar adalin shugabanmu ne ya halakamin iyayena da tsafin maciji kamar yanda naga alamar saran maciji a jikin Zawjata-almilk da ta rasu, ya kuma sanar min nima na tsira zanyi ba dan haka nima nayi takaina. Nazo mu hada hannu mu yakesa dan baza’a hukuntashi ba. Ni a lokacin maimakon cemasa wani abu ma rudani na shiga da tashin hankali akan iyayena,dan haka bamma gama saurarensa ba, ganin bana a hayyacina ya tashi ya fita. Sai kuma A ranar 9 ga watan 2 dai nanma na samu kiransa misalin karfe takwas a dare. Nayi matukar mamakin hakan, dan bai boyemun ba ya sanar min aiki fa yake son miyi tare kamar yanda ya a waccan ranar amma zai sanar min abu. Ban katsesa ba nace ina saurarensa.Yasanar min magana bazata yiwu ta wayar landline ba, amma ga number dinsa na kirashi direct video call. Har lokacin ban kawo komai a raina ba, duk da dai inajin toro ganin shiga uncle dinsa ne, idan na fadama wani bama za’a yarda dani ba. Dan haka nabi umarninsa na kira din dan bangama sanin yanda akeyi anan din ba. Tun daga wannan ranar ban sake fahimtar komai ba da ga yanda yake bibiyata sai da nakai madara ga adalin shugaban wannan kasa ya sha. Daga nan na fara fahimtar makirci ne musamman yanda ya dage akan sai an kaini kurkuku. Bayan an kainin kuma ya bini har can yana fadamin maganganun banza harda na rashin da’a”. Ta fashe da kuka mai cin rai, wanda a yanzu kam da gaske kukan take, dan kalmar KARUWA da Miran Jasim ya ce zai maidata na mata radadi har yanzu a cikin rai.

Dolene yanda Iffah ke bayanin yasa kaji hawaye yazo maka, kuma ko kai waye sai kaji ka yarda da ita. A nan din ma fa rudewa kotun ta sake yi, yayinda Miran Jasim ke hargowar sai ya batar da ita, sai ya shafe babin rayuwarta baki daya ita da Miran Arshaan da sukaci amanarsa. Babuma wanda ke saurarensa sai ALLAH wadai da ake jifansa da shi da tausayin Iffah da gaba daya yau kowa ya fahimci an mata makirçin ashe ,Dama can wasu da yawa tunma a ranar data aikata suke fadin bayin kanta bane, tayi kankanta da aikata laifin ita daya. To sai gashi yau kam komai ya fito filin ALLAH. Kotun tai bala'”in daukar turiri har sai da Tajwar Eshaan da kansa ya tsawatar. Dan danan kowa ya nutsu kotun tai tsitt. Ya dauka tsahon mintuna uku babu alamar zai ce wani abu, kafin ya nisa da kyar cikin maganar nan tasa a fuse kamar wanda akaima dole. Da kyar ya iya danne zafi da radadin da zuciyarsa ke masa kanjin wai uncle dinsa yama matarsa magana ta rashin da’a,amma ta boye masa.

 

 

 

“Alamu da kalaman Jasim in Abdul-majeed Aliy Qutb sun tabbatar da duk abinda aka sanar anan game da shi ya aikata. Sai dai duk da haka wannan kotu mai adalci zata bashi damar sanar damu dalilinsa na aikata duk wannan a zama na gaba. Za’a tsaresa a kurkukun da Zawjata-almilk tai rayuwa har zuwa ranar da kotu zata sake bukatar ganinsa a gabanta. Wannan kotu kuma ta wanke Zawjata-almilk da ga zargi, tare da bada damar kawo bokan da yay sihirin gaban shari’a shima. Tanada damar shigar da kara itama a karan kanta game da amfani da ita da Jasim yayi. Daga karshe ni Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ina shigar da kara nima bisa yunkurin kashe min MATA da akayi har karo biyu ta hanyar yimata allurar guda da jefata cikin ruwa…” da ga haka ya mike anutse cike da salon nan nasa yayinda ya bar jama’ar kotu gaba daya a yanayin mutuwar zuune da kalamansa na karshe. Malikat Haseenat kam murmushi ta saki mai sanyi da kayatarwa, hakama Daneen Ammarah. Yayinda zuciyar Malikat Bushirat ke bugawa da wani irin sauri-sauri a cikin kirjinta dake yin kamar zai bude.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button