Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 21

Sponsored links

Daddy na shiga ciki khaleel ya dauki bindigar daya cillar ya fita, fita daga gidan yayi a kafa yanajin kansa kamar ze fita, abun ya masa yawa wai shege da hauka, ga fatima zainab be ganta ba ga lamarin daddy da besan a ina zeyi categorizing dinsa ba, tayaya baze shiga damuwa ba, sai ya rasa me zai dafa yaji dadi…………

Yana cikin wannan hali kiran sameer ya share wayarsa wanda rabon su da yin waya sun dade, dauka yayi ya kara a kunne……

Sameer na ajye wayar ya tura masa address din, sai ya zauna zaman jiran zuwan khaleel, yana abuja tun wanchan lokacin amma ba wanda ya sani, yana zaune shi kadai yanaji kamar damuwar duniya akansa aka sauke, tin bayan yusuf yace su hadu washegari da rana be kara samun nitsuwa a rayuwa ba saboda yusuf din bezoba kamar yanda ya fada, haka yayita sintirin zuwa gurin kullum amma har rana me kamar ta yau Yusuf be zoba,!sai ya rasa waye me gaskiya tsakanin Deen da Yusuf, hakan sai ya dagula masa lissafi kawai ya mayarda giya abin shansa, haka ze zauna yayita sha tin safe har dare yayita maye abinsa shi kadai, at first ya dauka competition yakeyi da khaleel sai yanzu yagane santa yakeyi da gaske, ganin kamar illata kansa zeyi without any action ya sashi yanke shawarar kiran khaleel dan yasan dole ya samu information akanta a gurinsa…..

Yana zaune khaleel ya shigo parlourn da sallama, kallon parlourn yayi disgustingly yace;

“Kaidai anyi kazami wallahi, daga zuwa harka bata guri?”…….

Tana kwance a bedroom din mami sun sata a tsakiya kamar yanda sukayi randa bata da lafiya, a lokacin tara na dare ya wuce, likimo tayi kamar me bacci saidai idonta ko alamar bacci babu, so take suyi bacci ta tashi ta gwada fecewe, har karfe goma shiru sunata dan hirarsu Umm nata shafa mata kai daga bayanta, lokacin harta fara fita hayyacinta saboda batasha regulars dinta ba tin safe, tasan kuma in bata sha ba ba zaman lafiya, tsap saita birgice musu, ita kuma bataso ta kara creating wani scene din dan bataso ta daga musu hankali ganin yanda suka damu da lamarinta sosai…….

Around 11 taji tsit lokacin sunyi nisa a bacci, tashi tayi sadap sadap ta fita daga dakin, fitilolin parlourn duka a kashe sai ko ina yayi duhu, tafiya ta cigaba dayi dan zata iya gane kofar fita….

Ji tayi tayi karo da wani abu kamar dutse, janyewa tayi da sauri ta cigaba da tafiya, sake karo tayi da abu sai kuma taga ko ina na parlourn yayi haske……

Kallon nighties din dake jikinta Deen yayi, gashi ba dankwali a kanta sai gashinta ya zubo gwanin sha’awa, sosai ta mishi kyau har tsigar jikinsa na tashi, lumshe ido yayi cikin husky voice dinsa da yanayin daya fara shiga yace;

Sameer ya fada yanajin ba dadi a ransa na yanda ya zargi Deen da daukanta, ashe tana tareda khaleel be sani ba, kenan kuma Yusuf karya ya dinga masa, inba karya yake ba meyasa ya nemesa ya rasa toh?….

“Wow zakace ma? Ince maka wifey ta bata kacemin wow?”……

“Sorry nigga, wallahi I was just shocked ne, ya kamata mu nemota duk inda take gaskiya, karka damu I gat you”..,,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button