Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 15

Sponsored links

Haka *BOKA* *ZALIMU* ya bada umarni a cigaba da hukunta shi har na tsawon kwana uku 👌

Farin Bafulatani mai Ba’kar Zuciya, Sarkin Matsafan Duniya (Boka Zalimun) Baban AYUSHH

Shi a fad’ar sa daka ta6a Ayush gwara ka ro’ki mutuwarka,

Domin duk duniyan nan ba wanda yake so sama da d’iyarsa Ayush, ko cinyaka ce ta cije ta saiya zaro hannunsa ta cikin madubi ya mur’kushe ta 😳😳

(Anya kuwa d’aukar fansar Junaid zaiyu akan d’iyar Bara’atu kuwa 🤔).

___________________________

Ihun da Mommy tayi ne ya jawo hankulan kowa na gidan,

Ayush tana cikin cusa abinci sai da ta razana daga zaune ta mi’ke tsaye, sarkin tsoro har jikinta ya Fara 6ari tayi cikin toilet da gudu ta danna sakata!

Ayush! Ayush!! Ayush!!! Cikin sassanyar murya ake kiran sunan nan, ita kuwa Ayush tana kwance akan carpet kuka yaci ranta taji ana kiran sunanta kamar daga sama, dakatar da kukan tayi tana sauraron kiran da ake mata, sautin zazza’kar murya ne yake dukan kunnenta a hankali take d’ago da kanta wani irin hajijiya ne yake d’iban ta a haka ta tashi zaune!

Da dara-daran idanuwanta wad’anda sukayi jawur ta d’agosu ta kalli yanda sautin sunanta yake fitowa, cikin firgici taja da baya ta zaro manya-manyan idanuwanta waje tsoro ne ya kuma bayyana akan fuskarta, baki na kakkarwa ta ambaci “Umaa” abunda ya fito daga bakinta kenam tana kallon gurin da wata zankad’edd’iyar mata take tsaye, tana sanye da fararen kaya daga sama har ‘kasa ta rufe doguwar suman kanta da farin mayafi, da murmushi a kan fuskarta…

Ayush ce ta sake motsa baki tana fad’in “Umaanah” tana kuka kuma tana had’awa da dariya tayi farin cikin ganin mahaifiyar ta a wannan Daren misalin karfe 2:00

Itama Uman da murmushi a fuskarta cikin sanyayyar murya tace “Yarinyata nazo gareki ne domin na tunasar da ke abunda kika manta a baya,

ki kasance mai taimakon al’umma idan kika fuskanci suna cikin wani irin hali, kada ki dubi girman laifin da mutum yayi miki idan ya bu’kaci taimakon ki kawai ki taimake shi kema wata rana idan kika shiga wani hali Allah zai taimake ki, kada ki tsani bawa! kada ki cutar da bawa!! kada ki bari ata sanadiyarki a cutar da bawan Allah, Ayush d’iyata! ‘Dan uwanki yana bu’katar taimakon ki kije ki taimake shi kada ki damu Allah yana tare da mai hakuri, kije ki, ki je ki taimake shi……..!

Tana kaiwa karshen maganar ta 6ace 6attt.

A firgice Ayush ta tashi zaune tana fad’in “Umaa! Umaana!! Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, mafarki Ayush tayi kwanciyar da tayi tana kuka ashe bacci 6arawo yayi awun gaba da ita, zuwan da mahaifiyar ta tayi acikin mafarki ta zo mata.

Ta waiwaya ko Ina bata ga kowa ba ga hawayen da ya bushe mata akan fuskar “tabbas mafarki nayi, Uma tazo mun” a lokacin ta fara tariyo maganganun mahaifiyar tatan lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka, Junaid ne ya fad’o mata a rai “Uma mutumin da ya rabaki da rayuwarki shi kike so na taimaka?” Kuka ne ya kwato mata sai wani tunani yazo mata a cikin zuciyarta take fad’in “Mahaifiyar shi ta taimake ni, ba don ita ba bansan Ina zan nufa ba, shin itama tana raye ne ko ta mutu? Tabbas suna bu’katar taimako a wannan halin” ta mi’ke tsaye cikin sauri lokaci guda kuma ta tsaya cakk

Alamar ta tsaya tunanin wani abu “amma meyasa naga shi wannan mutumin a manne da jikin gini ba tare da an d’aure shi ba, kuma jikinsa a faffashe kamar ma ya mutu”… ‘Kirjinta ne yayi wani irin bugawa ta zabura da gudu ta nufi hanyar d’akin takawa d’aya biyu taji kamar an ri’ke ‘kafarta ta doku a ‘kasi danma carpet ne mai gashi da tunin taji ciwo,

Tana shirin d’agowa kunnuwanta suka jiyo mata kukan mujiya 🦉🦉 mai firgitarwa a tsorace ta kalli saman cilling yanda ta jiyo kukan kenam, wutar nepa gidan ne ya d’age sai duhun daya biyo baya ko hannunta bata iya gani wani irin tsoro ne yabi jikinta,  kamar daga sama tajiyo wata ‘katuwar murya ana cewa “AYUSHHHH KADA KI KUSKURA KI TAKA ‘DAKIN NAN, WANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA ZAKI TAIMAKA? TO LALLAI KEMA ZAI KASHE KI KAMAR YANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA, KIYI TUNANI SHI BA MASOYINKI BANE MAKIYINKI NE, YANA NEMAN AHALINKU NE DOMIN YA GAMA DA RAYUWAR KU GABA DAYA HAHAHAHA, HAHAHA, HAHAHAHA haka ta ringa jiyowa dariya marar dad’in ji,

Jikinta ne ya hau 6ari murya na kakkarwa tace “waye Kai?”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button