Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 59

Sponsored links

Abu ne ya isa mom ta sake komawa a mata sabon aiki akan su mami dan bataga alamun na farko yaci ba, ba bata lokaci aka sake wani aikin akansu dayafi wanchan sai ga mami tana kuka tana gayamata itafa ta kasa gane kan dad kwana biyunnan gabadaya ya chanja mata, magana kadan fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba gashi ko dansa be kyale ba, wani irin farin ciki mom taji a ranta kamar ta tashi ta taka rawa, saidai ta daure ta shiga bawa mami shawara cikin tausayawa akan tace ya saketa kawai, amsa mata kawai mami tayi badan zata iya ba…….

Haka suka cigaba da zaman wahala na tsawon shekaru biyu batareda kowa ya sani ba in banda mom, har a lokacin kuma maganar saki bata taba shiga tsakaninsu ba…….

Ita kuma mom ji take kamar tayi hauka dan bata da wani buri illa taga sun rabu amma kamar mayu sunki rabuwa gashi sun riga sungama plan ita da kawarta kan yadda zatasa baban hameeda ya saketa ita kuma ta auri dad idan ta rabasu da mami……

Ganin lokaci na kara gudu ba wani maganar rabuwa tsakanin mami da dad yasa suka sake shawara ita da sabuwar kawarta, set up suka yiwa mami sukasa daddy ya kamata da wani a daki, nan rikici me karfi ya barke tsakanin mami da dad, kullum bashi da aiki sai ci mata mutunci akan ta kawo masa kwarto gida, ya dena cin abincinta ya dena kwana da ita amma kuma yaki sakinta, mami da taga she’s dying in silence tace wallahi sai ya saketa, shi kuma ya dage baze saketa ba saboda yasan karuwanci takeso taje tayi gwara suyita zama a haka har su mutu dan shi ko aure baze iya karawa ba saboda gani yake kamar duka mata haka suke………..

Mami data rame ta lalace saboda damuwa taga bazata iya jurewa ba taje ta fadama iyayenta, ba bata lokaci baffa yasa a kirasa ya tarasu duka su biyun ya musu fada sosai, sannan yace dad ya saketa kawai saboda aure baya yiwuwa da zargi tinda tace ita bata aikata ba shi kuma yace da idonsa ya gani, sai cewa yayi shi yana sonta baze iya sakinta ba, baffa kuma yace be isaba dan baze yarda yarsa ta cigaba da zama cikin wahala ba da sunan aure, hakuri yayita basa wai ya hakura koda tayi din dagaske ya yafe mata kuma insha Allah ze gyara baze kara mata cin mutunci ba, ganin ya dage yasa baffa sake musu nasiha me ratsa jiki sannan yace su tashi su tafi………

Saidai inaa dad be chanja zani ba dukda yayi kokarin ganin yayi hakan amma kamar zugashi ake sai yaji ya kasa, haka mami ta sake jurewa na tsawon wani shekarar lokacin deen na sha uku ya kuma fara gane akwai sabani sosai tsakanin iyayensa……….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button