Hausa Novels and Stories

Auren Fari Complete Hausa Novel 2

Sponsored links

Eh ke fa..

Maza shirya kada motocin su kare, wani paper lace ne milk dinkin riga da skirt ta dauka. Har zata fita taga hajiyar ta shigo da sauri ta miko mata takalma ungo wurin amarya na roko miki wannan kuma gyale ne sanya maza ki wuce.

Ko hoda bata shafa ba.

Tana zuwa ta fada mota. Ko da a ka sauke su. Fiddausi kanwar amarya na ganin ta tace yauwa umaima zo Ku shiga da kayan nan. Ta ce to ta shiga aiki. Dai dai lokacin da sukayi tsaya da mota kamar ance ya daga kai kawai ya hango ta rungume da lemuka.

Da sauri ya fito sai kuma ya yi turus daya tuna inda yazo.

Muje ko?

Ya rungume hannu a kirji tare da jingina da mota ya ce kuje ina zuwa …duk suka kalleshi sai kawai yayi sauri ya fiddo waya yasa a kunne hakan yasa suka fahimci waya zaiyi. Suna wucewa ya mayar da ita aljihu, ta fito tana ta faman kakkabe kakkaben kaya yayi murmushi watau yau bata son abinda ka taba kayan jikin ta.

Sam bata lura dashi ba ta zo zata wuce sai kawai taji an fizgeta anyi bayan motoci, ta dago da karfi sai kawai ta ganshi. Ta fizge hannun ta tare da ingijeshi kana hauka ne zaka kama ni? Zai yi magana ta juya abinta kayan data fasa dauka kenan ta shiga ciki duk an zazzauna ta hango kujera can tsakiya ta isa ta janyo zata zauna ashe biye yake da ita kawai ya harbar da kujerar ji kakeyi *timmm* ya wuce abinsa duk aka juyo hankalin kowa ya dawo kanta ta wunkura da karfi zata isa gunsa fiddausi ta gani gaban ta. Sannu umaima ke nake nema zo muje ki taya my serving wani takaici ya turnuke ta ta bishi da kallo dai dai lokacin da ya hau gun anguna ya zauna ya juyo yana hararar ta.

Kunya duk ta baibaiye ta. Shine ya bude t├áro da addu’a ya bada tarihin ango don haka bata nan suna can suna shirya abinci.

Fiddausi tace kamata yayi mu fara kaiwa haka .

Umaimah tayi karaf Anty fiddausi kawo in faro daga sama wurin angwaye.

Yawwa Allah ya yi miki albarka umaimah dama kowa baison zuwa saman cen, ta dauki ture ta fara shiryawa. Zuwa na uku da zatayi ta debi cocktail juice da farfesun kayan ciki ta tafi tana isa kamar zata ajiye bisa yanda ta faro daga farko kawai sai ta antaya mishi duka ajiki har turen jikake rikichaaaa …… Duk Wanda ke high table din tsaye ya mike hankali tashe……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button