Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 26

Sponsored links

“I don’t care so far as I’ll be with you, let’s just go far away from all the wicked people, mu gudu muje muyi aure muyi rayuwarmu mu biyu abunmu, I promise to take very good care of you, if it takes giving you the world completely I’ll do”……..

“Na amince!”…..

Ta fada with a devilish smile saboda faduwa ce tazo daidai da zama, dama tana tinanin yanda zata gudo daga gurin mayen chan sai gashi Allah ya kawo mata, khaleel ko tasan sai yanda tayi dashi dan in tace yes ko uwarsa bata isa ta chanja ba…….

“Wayyo am I dreaming? Naji dadi sosai wallahi, I knew we’ll someday get along that’s why I’ve always been patient”…..

“I don’t know how it happens but I think I’m in love with you!”…….

 

Kamar saukar aradu haka Deen yaji wannan kalaman nata, tun da suka fara zancen yake gefensu basu sani ba wai su masoyya, harsu zancen guduwa yanaji yace zega yanda zaayi tabi saurayi su gudu, ji yayi kamar ya shakota yanda take wani kashe masa murya, ransa in yayi dubu ya baci a inda yake a tsaye, daurewa yayi yanaso yaji inda zancen nasu ze kare sai kawai yaji wani abu kamar saukar dalma, wai she’s in love with him?!!!…

“Wani country kikeso mu tafi? I don’t know if you have any in mind?”…..

 

Zatayi magana kenan taji khaleel ya kwallara ihu, ko kafin ta fahimci abinda ke faruwa khaleel ya sake sakin wani ihun dayafi wanchan saboda yanda yaji kamar anbuga masa guduma akai gashi he wasn’t prepared bare ya kare kansa, daga sama kawai yake jin bugu….

 

 

Juyowa tayi da sauri daidai lokacin sukayi ido hudu da Deen daketa naushin khaleel ta baki ta hanci ta ko ina, idanuwannan nasa sunyi jawur ga muscles dinsa da suka fito rado rado kana gani kasan ma’abocin karfi ne da cikar halitta…Gashi dai dukan khaleel yake amma idonsa na kanta…..

Sandarewa tayi a tsaye tana kallon Deen da sai jibgar khaleel yake ta kasa yin komai……

Sake kaiwa khaleel da bakinsa ze zubar da jini naushi yayi yana fadin;

 

 

“Ashe dama duka danginku mugayene azzalumai? Na dauka soyayyar tsakani da Allah kake mata ashe kaima wani abun kake nema a gurinta kamar ubanka Ibrahim?! Ubanka be kyaleta ba kai baka kyaleta ba kasheta kuke sonyi ne? Toh kunyi naku kungama a sannu kuma zanyi maganinku gabadaya! Kaje ka gayawa ubanka ni Saifuddeen nasan abinda kuke shiryawa kiris ya rage na tarwatsaku duka, sannan zan baka last warning ka fita harkarta dan ko a mafarki bazaka taba samunta ba, she doesn’t deserve a useless stupid person like you!!”………

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button