Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 14

Sponsored links

Jimm yayi na tunani, sai kuma ya sauke numfashi. “Okay! okay inaga bara na tura miki adireshin inda nake a yanzu haka sai mu haɗu nan in ba damuwa ko”.

“Ya dai kasance babu abinda zai shafi mutuncina a wajen sir”.

“Wannan shike ƙara samun naji ke ta daban ce Iffah”.

Baki ta sake ƙyabewa. Amsa garesa kuma tace “humm” kawai.

Kallon baki da hankali mai haɗi da tsoro tun daga ƙarƙashin zuciya yake mata tun bayan gama masa dogon jawabin da tayi. Tasan zataga fiye da hakan ga kowa bama shi kawai ba, dan haka bataji komai ba sai ma murmushi data sakar masa. Bata san mi yake tattaunawa da zuciyarsa ba, amma tanaji a ranta yana auna shekarunta da maganganun da kowa zai auna da wautarta ne kawai. Ilai kuwa sai ta tsinkayi muryarsa da irin amsar datai tunanin samu.

“Nikam Iffah shekarunki nawa?”.

“Ashirin a kwashe biyu sir”.

Ta faɗa tamkar bata fahimci alaƙar tambayar tasa ba. Kansa ya jinjina da cije lips nashi, kansa tsaye yace “Nama tunaninki mai kama da mafarki uziri. Amma zan baki shawara data dace da waɗanan shekarun naki na ƙuruciya. Ƙoƙarin ya kamata kiyi wajen cinye jarabawar share fagen shiga jami’a da ke tunkaroki kamar yanda nasan burinki. Tunaninki kuma ya zam tamkar baki taɓa yinsa ba, sannan na kasance na farko kuma na ƙarshe da kika faɗawa. Hakanne zai baki damar cigaba da ƙyaƙyƙyawar rayuwar da kika fara da ke da ahalinki har nima na cigaba da saka rasan samunki matsayin uwar ƴaƴana wata rana dan ALLAH Iffah”. Ya ƙare maganar da haɗe hannaye alamar roƙo.🙏🏻

“Ƙyaƙyƙyawar rayuwa ta daɗe da yankewa a cikin rayuwata data ahalina. kuma irinta nake hangowa da son daƙilewa ga ƴan baya ciki harda ƴaƴan da kaima a karan kanka zaka iya haifa wataran Sir. Sannan wannan tsoron da nake gani yanzu a cikin idanunka shine zai tabbatar da hakan, koda ni bana raye kai zaka rayu ka tuna. Nagode da saurarena da kayi sir”.

Da sauri yasha gabanta kasancewar ta riga ta miƙe. Tai takwaf-takwaf da fuska tana mai tsaresa da manyan idanunta da tuni hasken cikinsu ya koma launin ja. “Ki fahimceni Fareedah, koba komai na fiki shekaru, na fiki ilimin sanin rayuwa dama sirrikan dake zagaye da lungu da saƙo na ƙasar Ruman….”

“Na sani sir, tabbas na sani shiyyasa ma na fara nemanka. Sai dai nima kayi haƙuri, dan babu shawararka ɗaya data shiga cikin wannan kan nawa, saboda abinda ke cikinsa tamkar kundin littafin da aka rubuta labari daki-daki ne, kaga dole zaizo feji bayan feji. Kuma duk abinda ya shiga ciki bazai taɓa goguwa ba sai ta hanya ɗaya tak! Mutuwa!. Mutuwa ce kawai zata goge wannan yunƙurin insha ALLAH. Na barka lafiya”.

Sororo ya bita da kallo harta tare mototaxi ta shiga, ji yay ta ƙara masa girma a ido, girma bana shekaru kawai ba na wata ilhamar kwarjini da cikar mutuntaka. In har yara irinta da ayanzu suka fara rayuwa zasuyi irin wannan tunani akan al’ummarsu mi manya kakaninsa, iyayensa, yayunsa dama sa’aninsa sukeyi ne su? Shin basa ganin abinda take gani ne? Ko kuwa da gaske tsoron data ambata ta gani a cikin idanun nasane a idon kowa?. Kenan hatta da sauran sarakunan ƙasar da mafi yawan cikinsu sun rasa ƴaƴansu suma cikin tsoron suke? Anya maganar mutane ba tabbatacciya bace akan danganta Shahanshan na daular ruman da magajin fir’auna daya shuɗe batare da labarinsa ya gushe ba?. Iffah! Iffah!! Da gasken gaske ke tadabance kamar yanda nasha faɗa a aji aduk sanda kika bada amsar data danganci darasi…..

Kwanaki uku kenan da Iffah ta tunkari malaminta batare da nasara ko ƙwarin gwiwa daga garesa ba. Sai dai hakan baisa taji ta sare ba ko haƙura da ƙudirinta. Koda ace nata ajalin take tunkara tayi alƙawarin sai tabi kadin jinin ƴan uwanta guda biyu. Koda ace bata da ƙarfin ikon ruguza mulkin sarkin dake kama da mulki irin na fir’auna zata tabbatar sai kuwwar gunjin kukanta ta fita a duniya, koba komai tanada yaƙinin a bayanta zata samu masu share mata hawaye insha ALLAHU.

 

Hanyar da tabi a farko ita kaɗaice hanyar da tasan tanada ita wajen bi ta samu nasara cikin sauƙi. Sai gashi kuma ba’a dace ba. Gashi tabi ta biyu itama, sai dai anƙi buɗemata ƙofar saboda tsoro da ƙarfin tasirin mulkin azzalumin, a yanzu haka tunaninta hanya ta uku koda itama bazata samu nasarar ba. Zata kuma cigaba da bin hanyoyin koda zasu ninka dubu sau dubu har sai ta dace. Nannauyan numfashin data zuƙa ta fesar, tare da gyara kwanciyata ta jawo wayar Arfa da har yanzu bata bari wani a gidansu yasan da tana amfani da ita ba. Ido sosai ta tsurama wayar, tabbas ba gizo bane tarin missed call ne daga malaminta. Taruwarsu da rashin jin sanda suka shigo wayar kuma nada nasaba da kasancewarta a silent. Tayi kamar zata share amma sai ta kasa hakan. Dan a yanzu shine kawai madubin da take kallo matsayin damar dake a hanunta ta isa ga abinda take so da wurwuri. Cikin sa’a tana kokarin kiransa sai ga kiran nasa ya sake shigowa. A dakile ta amsa tare da masa sallama murya a cuɗe.

Kalmar farko data fara fita a bakinsa. Iffah taja numfashi mai nauyi tare da haɗiyewa muƙut. “Sir bakamun laifin komaiba nikam”. Ta faɗa tamkar komai baima faruba. “Humm” ya faɗa shima, sai kuma ya ɗora da faɗin “Ina son mu haɗu”.

“Babu dalilin hakan sir”.

“Akwai Fareedah, kar kiyi taurin kai”.

“Koba komai kai ɗin malamina ne ai, mi zaisa na maka taurin kai?. Iya gaskiyata nake faɗa maka”.

“A cikin gaskiyar taki harda haƙura da samun abokina”.

Zumbur ta miƙe zaune tamkar wadda aka kwantsamawa a radu a tsakkiyar kunne. “Sirrrrr!…..”

“Na amince zan haɗaki da shi”.

Ya katseta da sauri. Jitai tamkar ta sandara ihu ko zaifi fahimtar farin cikin dake a tare da ita, amma sai tai ƙoƙarin gimtsewa. “Sir ba dole sai shi kawai bane zaiyi aikin, harma na samu wan….

“Fareedahhh!”.

Ya faɗa da wani yanayi a muryarsa. Ajiyar zuciya ta sauke a ƙasan maƙoshi. Sai kuma ta lumshe idanu tamkar tana a gabansa tace, “Shikenan ka turamun adireshi. Sai dai inda bazai taɓa mutuncina ba”.

Murmushi yayi mai sauti, tare da faɗa kamar yanda ya saba tun acan baya. “Fareedah ke ta dabance ƙwarai da gaskeeee”.

Baki taɗan laɓe batare da tace komai ba ta yanke wayar……….✍

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button