Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 1

Sponsored links

Murmushi ta saki mai sanyi bayan gama sauraren dogon bayanin nasu, ta ɗan muskuta zamanta na ƙasaita cike da ƙarfin hali da sake bayyanar rauninta na tsufa da halin rashin ƙarfin jiki da jiyyar kwana biyu ta haddasa mata. Malikat Haseenat kenan tare da manyan masu faɗa ajin masarauta da suka buƙaci zama da ita akan lamarin Iffah da suke buƙatar shiga kotu domin yanke mata hukunci dai-dai da abinda ta aikata bisa tunzurawar Miran Arshaan da Miran Jasim. Cikin dattakonta da ƙasaita ta sake jan numfashi a karo na biyu idanunta akan su Miran Jasim, sai kuma ta ɗan kaudasu tana jinjina kai.

 

“Bazan hana ko dakatarwa ba akan gurfanar da mai laifi irin Zawjata-almilk. Sai dai a nawa adalcin ina bada ƙwarin gwiwa da shawara ga masu zaman shari’ar bin komai a sannu da yin ƙwaƙwƙwaran bincike. Sashen Shahan-shan dai zagaye yake da ƙyamarori, hakama madarar da aka tabbatar ya sha tana buƙatar musan daga ina ta fito, shi kansa dafin data zuba waya samar mata da shi har ya shigo cikin masarautar nan?. Abu na ƙarshe shine bata tsaro na musamman da saka idanu a dukkan abinda zata ci. Dan in har wani abu ya sami yarinyar nan batare da gaskiya ta fito ba a tabbata hukunci zai koma hannuna, kuma zan iya zartar da shi akan kowa. Idan nace kowa ina nufin kowa ma koda nice a karan kaina”.

 

 

Babu wanda ya iya tari a falon sai jinjina kawuna kawai suke. Yayinda Malikat Haseenat bata sake tofa komai ba sai ma ƙoƙarin barin falon da tai ta hanyar gara wheelchair ɗinta da remote ɗin jikinta (nace kaga ƴan gatan duniya lols😉). Da kallo suma kawai suka bita babu alamar wani zai ce har lokacin. Sai dai zukatan wasu tamkar zasu kama da wuta dan baƙin cikinta, ji suke kamar subi dare wajen mata yankan rago su zubar da jinin banza. Wasu ko gamsuwa sukai da bayanin nata, dan dama sunbi wannan ayarin ne kawai saboda rashin ƙarfin cewarsu, amma da za’a basu zaɓi sunfi buƙatar ayi haƙuri ma har Shahan-shan ya ƙarasa samun lafiyar da kowa ke fata…..

a a dagule. Sai faman huci suke kamar wasu zakuna. Tamkar basuga juna ba suka fara kaikawo kamar masu safa da marwa. Sunyi haka ya kai sau hur-huɗu kafin Miran Arshaan ya dakata cikin ƙunar zuciya ya furta, “A wannan gaɓar maciji muka kashe bamu sare kansa ba. Kauda wannan yaron a bayan rayuwar wannan tsohuwar sunansa BAYA DA ƘURA….”

“…Idan har barin wadda rayuwa ta zame mata saura ƙiris a zahirance zai amsa suna baya da ƙura to cigaba da numfashin waccan yarinyar sunansa BAYA DA TARNAƘI”. Miran Jasim ya katsesa a zafafe shima. Tsaye sukai sunama juna kallon kallo. Kafin Miran Arshaan ya katse shirun ta hanyar faɗin, “Tsuntsayen biyu jifa iri ɗaya suke buƙata. Inba haka ba a cikin ƙarfin iko za’a tabbatar da ƙarfafa mai rauni”.

“Na tabbatar da hakan ta hanyar gani da ido, kunnena kuma sun jiye min tabbacin AKWAI WATA A ƘASA bayan tatsuniyar gizo da ƙoƙi”.

“Miye mafita?!”.

Cewar Miran Arshaan cikin tarar numfashin Miran Jasim. Miran Jasim ɗin ya kafesa da idanu yana sakin wani murmushi. “A wannan gaɓar jifar tsuntsu huɗu da dutsi ɗaya ne ba biyu ba”.

Jimmm Miran Arshaan yay yana kallonsa, dan a saninsa da hasashensa tsuntsayen da ya kamata su jefa uku ne kawai ba huɗun ba. Sai dai kafin yace komai Miran Jasim ɗin ya katsesa da sake faɗin, “Tabbas huɗu ne, sai dai zamu fara kauda ukun kafin cikon na huɗun, dan haka dole ne a gobe mu ziyarci Barbushi”.

Miran Arshaan zai yi magana sai kuma ya haɗiye, batare da ya ƙara tofa komai ba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “Asuba ta gari”.

Da wani mugun kallo Miran Jasim ya bisa, yayinda shima Miran Arshaan ɗin ya fice yana taunar lips tabbacin da nasa ƙudirin shima.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button