Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 9

Sponsored links

Kama hanun yaron da Iffah tai da nufin subar wajen duk da key ɗin motar mutanen har yanzu na’a hanunta yay dai-dai da isowar wani nutsatstsen taku mai tafiya da sassanyan ƙamshin turare tamkar shi kaɗai iska ke tsintowa tana busawa a hancinan mutane. Kamar wani magic wajen yay tsitt na wasu sakkani, tsirarun mutanen da suka taru a wajen tun furuwar abun duk suka zuba masa idanu. Ita kanta hajiya Iffah mai masifar ƙirjintane yay wata irin harbawa lokacin da mutumin ya sauke nasa lulu idanun cikin tsakkiyar nata. Da ƙyar ta iya fisgar su daga cikin nasa tana ɗan murguɗa baki da sauke niƙaf ɗinta cike da dakiya.

Idanun nasa ya janye daga kanta shima da matsawa gaban yaron ya kai tsigunne dai-dai tsayinsa dan ya fara ɗauka yarinyar nan aljanace ma dai kawai. Cikin sassanyar muryarsa mai zurfi da nutsuwa ya motsa lips ɗinsa kaɗan tamkar an fisgo maganar.

“Kana lafiya?”.

Kai yaron ya gyaɗa masa.

Ya ɗan ɗage gira da motsa bakinsa kamar zai taɓe. “Uhhm! minene sunanka?”.

“Amjed”.

Yaron ya faɗa cike da kwarin gwiwa.

A hankali ya sake kaɗa fararen idanunsa tare da jinjina masa👍🏻 ya saki wani sassanyan murmushi a karon farko da jan kumatun yaron. “Oh my Friend! nice name. Kana sona da aboki?”.

Da sauri yaron ya jinjina kai yana washe baki. Idanunsa ya ɗan sake fiddowa suka ƙara girma tare da ƙara sakin murmushi. Ya riƙo hannu yaron alamar suyi musabaha.

Al’amarin ya birge mutane da yawa, duk da babu wanda yasan wanene shi, amma ko makaho ya kalla wannan mutumi yasan babban mutum ne. Suit ɗin dake jikinsa farare tas ma kawai abin kallone. Balle shi a karan kansa daya kasance ƙyaƙyƙyawan gasken fatarsa da gogewarta har ɗaukar idanun mai kallo take. Ga wani ƙamshi na musamman mai saka nutsuwa ga mai shaƙa, yanayin kamewarsa da cikakkiyar isa irin ta manyan mutane ke ƙara kawata kwarjininsa da cikar kamala ga duk mai kallonsa.

A karo na biyu suka sake haɗa ido da Iffah dai-dai ya gama gaida kakar yaron nan da keta faman washe baki da jera masa godiya dan kuɗine dunkulallu sabbi ƙal ya damƙa a hanun Amjed. Harara ta balla masa da janye idanunta da sauri saboda wani abu mai tsananin sanyi taji yana tafiya daga ƙafafunta har saman kanta. Cike da takunsa na nutsuwa da ƙasaita shima ya juya ya bar wajen kai kace akan dole yake taka ƙasar saboda takun zaratan maza masu cikakkiyar isa da lafiya ce tattare da tafiyar tasa. Iffah ta jefama ɗaya daga cikin samarin nan biyu key ɗin motar, dan ɗayan ya tafi da hanzari ya buɗema ogansu ne. Dai-dai zai shiga ta ballama wanda ta jefama key ɗin harara da faɗin, “Daga yau ko daga nesa kuka hangoni to ku canja hanya koda a jirgi kuke kuwa”.

Shigar maganar tata a cikin kunensa dai-dai zai shiga motar da aka buɗe masa ya ɗan ɗago idonsa, sai dai wadda ya ɗago da nufin kallar da mamakinta ke cin ransa tuni ta nufi barin wajen tamkar ba ita ta haɗa dabar wajen ba… Suna ƙoƙarin shan shataletalen titin idanunsa ya sake sauka a kanta ta miƙe titi tana tafiyarta a nutse, sai dai fuskarta a rufe take da niƙab data saki tun bayan haɗa idonsu na farko….

“Badai a ƙasa kika tahoba auta? Na ganki a gajiye tamkar an koroki”.

Zubewa tai a taburmar da Ummu ke zaune, tare da ɗora kanta a cinyarta tana ƙara narke fuska. “ALLAH a ƙasa na taho Ummu. Haka kawai naji ina son na taho a ƙafan”.

“Ai gashi nan duk kin gajiyar da kanki, dama keba wata isashshiyar lafiya ba. Tashi kiɗan watsa ruwa dan sai warin rana kikeyi”.

“Kai Ummu warin rana fa?”. Tai maganar a shagwaɓe da kamo rigarta ta kai hancinta. Miƙewa tai tana tura baki gaba da faɗin, “ALLAH Ummu kinso dai yarfanine amma ƙamshin ma turare nakeyi”.

Murmushi kawai Ummu tai da girgiza kanta, ita kuma ta shige ɗaki sai faman cika baki take da iska a dole taji haushi…..

Da daddare suna zaune a tsakar gida cikin hasken farin wata daya raba Hanash na koyama Iffah aikin makaranta. Daga gefensu Ummu da Babiy ne zaune yana cin abinci. Hira suke jefi-jefi akan kayan lambunsa da zai fidda a ƙarshen satin nan ga ƴan kasuwa. Iffah tai karaf jin Babiy yace zuma batayi kirki ba wannan karon bazata wuce tulu biyu ba.

“Babiy sai a bar mana mu shanye kawai a gida. Kaga dama Ummu zatamin alkakin saukar islamiyyarmu nan da wata biyu”.

Murmushi Babiy yayi, “Zanso haka Ibnati, sai dai bazai yuwuba dan dukanta zan kaita masarauta ne”.

Take murmushin fuskar Iffah ya ɗauke baki ɗaya. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru ta maida kanta ga aikinta kamar bataji ba. Shima Babiy sai bai sake cewa komai ba akan zumar suka cigaba da maganarsu da Hanash da Ummu dake saka baki jefi-jefi…..

Tun wannan magana babu wanda ya sake tada zancen zumar nan. Babiy da Hanash suka duƙufa tattare kayan lambu da za’a fitar. Yayinda Iffah ta cigaba da zuwa makarantarta a zahiri kamar babu wata damuwa tattare da ita. Sai dai kuma a baɗini tun randa akai maganar kai zuma daular ruman zuciyarta sam bata huta ba. A duk motsinta cikin ƙullawa da kwancewa take game da babban burinta na ɗaukar fansa. Wanda tasan bata da wata hanyar yin hakan sai ta wannan zuma da Babiy ke kaiwa masarauta. Kuma tasha jin cewa Tajwar ne ke shanta kawai.

Har ana saura kwana biyu bata samu wata mafitaba akan ƙudirinta, dan haka tana zuwa makaranta taja wata ƙawarta da kafin yanzu da ta canja suke sabgarsu da rashinji tare gefe. Ikram da taji farin cikin ƙawarta ta fara dawowa yanda take babu musu ta bita suka koma can ƙarƙashin wata bishiya suka zauna.

“Ko kefa Iffah, ALLAH bana jin daɗin yanda kike shareni yanzu sam. Dan ALLAH ki manta da komai mu cigaba da yima su Akia Arfa addu’a”.

“Humm”. kawai Iffah tace da ɗan laɓe fuska. “Kinga ni ba wannan yasa na kiraki ba, tambayarki nake so nayi?”.

“To ALLAH yasa na sani”. Cewar Ikram tana gyara zama.

“Kinma sani, kwanaki bakin bani labarin sister ɗin mamanku tasha zuma taita ciwon ciki ba, kafin aje asibiti har hanjinta ya kakkatse?”.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button