Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 15

Sponsored links

“Kinyi alkawarin zaki riketa tsakani da Allah? In kinsan bazaki iyaba kema gwara ki sanar dani in nemi inda zan kaita”…

 

Daddy ya sake tambaya dukda ya gamsu da maganganunta, ya kuma yarda tana son shi sosai kamar yanda ta fada, kuma ko ba komai gwara ita tinda tana nuna abinta a fili akan momma me munafurci……..

 

“Nayi wallahi, tawo daughter kinci abinci kuwa, taso muje naga kamar ma bakya jin daddy”…..

 

Murmushi daddy yayi yacewa fatima zainab ta tashi ta bita…….

 

Daganan wani sabon phase na rayuwarta ya sake budewa, inda ta gwammaci zamanta a gurin momma so dari akan mama, a takaice dai lamarin rayuwarta sai ya kara hargitsewa, da farko mama ta dan fara sata aiki saidai ganin yanda take kwabamata yasata gane bata iya komai ba, nan tace bazata zama me koya mata ba wallahi gwara ta saura a haka yanda duk inda taje bazata moru ba, ada da take kwana a kitchen sai mama ta maida gurin kwananta store, batasan store din ya fiye mata kitchen ba dan koba komai yafi dimi dukda ba fanka ba fitila ga beraye, nan fa shayeshaye yaci uban na da dan wani zubin sai tayi kwana biyu a kulle a ciki, gane hakan ne yasata take siyo codeine in excess tazo ta boyeshi tayita sha tana mayenta ita kadai, gashi mama ta iya takunta dan daddy ko momma basu taba gane halin da take ciki ba, daddy har dena tambayarta yayi ko akwai abinda ke damunta ganin kamar mama na iya bakin kokarinta akanta, a lokacin duka yayan mama boarding sukeyi amma in suka dawo hutu suyita mata rashin mutunci iri iri, momma da take hanata abinci na kwana daya sai gashi tagamu da mama da sai tayi sati biyu abinci, abu daya ke taimakonta kusan kullum sai daddy ya kirata sunsha fruits a part dinsa hakan yasa ta saba da rashin cin abinci, sai ya zamana ko an bata abincin batasan ci dan bata saba ci ba, shiyasa gatanan kullum sai a hankali ba auki sai shegen kyau, taimakonta daya tanada diri sosai kuma duk raman da zatayi iya fuska ne da wuya amma mazaunanta da hips dinta basu san anayi ba, kadama boobs dinta suji labari…..

Sai da aka kai ruwa aka kai rana kafin daddy ya yarda momma ta dawo gidan da sharuda dayawa…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button