Hausa Novels and Stories

Idon Naira 3

Sponsored links

A falon nasu ta samu Abbah da su Ummanta suna kalacin safe ta tsuguna ta gaida su gaba ɗaya a jam’i tana ɗauke idanunta daga duban sashin da Amarya Hafsatu ke zaune ta zauna daga gefen Ummarta ta zuba kunun tsamiya da ƙosai ta fara ci.

“Maryamah ƙarfe nawa za ki dawo daga makarantar yau?”

Abbanta ya tambaya idanunsa a kanta, sai ta ɗaga kai ta dubesa tana amsa shi da cewa,

“Ƙarfe biyu Abbah.”

Malam Adamu ya gyaɗa kai yace”

Madallah, Ga kuɗin motarki na kwana biyu zan baki don tafiya Lokoja ya kamani sai jibi zan dawo idan Allah Ya yarda.

Ya yi maganar yana zura hannu ya zaro kuɗin ya miƙa mata

Maryamah ta amsa kuɗin ta yi godia tana cigaba da cin abincin har ta kammala Ta yi wa Abbah da Umma sai ta dawo ta fice daga falon.

Bayan tafiyar malam har kusan yamma tana dakinta Bata fitoba

Ta muskuta tana sake rintse idanunta kewa da kaɗaicin rashin abokin hira ko wanda za ta yi walwala tare da shi na sake danne zuciyarta

ta buɗe idanun tana janyo radio ta kunna don shi ne abokin hirarta idan Malam ya fita kasuwa ko idan ya yi tafiya baya gari gaba ɗaya don sam bata iya fita zaman falo sabida gujewa ɓacin rai da kallon ƙasƙanci daga abokan zaman gidan.

Wannan shi ne kalar irin rayuwar da Hafsatu ke yi a gidan Malam Adamu tun da ya auro ta shekaru biyu da suka wuce har kawo yau da take ɗauke da cikin watanni bakwai Sam Ummar Maryamah da ita kanta Maryamah basu taɓa nuna cewa akwai lokacin da za su amsheta da daraja,

Basa zaginta basa komai hakama basa Shiga sanbarta,

Anty hadeeza kuwa Sam batayi Mata kallon mace ma take gani bare harta dauketa kishiya ko cikakkiyar mutum ma,

Ita ko Maryamah tsakaninta da ita gaisuwar safe ce idan ta gaidasu a tare da iyayenta sai sallama idan tashigo guri hafsatun na gurin.

Hafsatu abin na damunta ƙwarai gashi Malam ba mai son shige shigen gidajen maƙwafta bane bare ta yi ƙawaye waɗanda za su dinga ɗebe mata kewa Mace ɗaya ce dattijuwa da ta saba da ita me suna Iyah me ƙosai ita ma ɗin ita ke shigowa gidan ba Hafsah ke zuwa nata gidan ba kwana biyu ma tayi tafiya ta tafi can garinsu shiyasa bata da abokin hira sai dai ta shige ɗaki ta kunna radio ta yi ta saurare.

Ƙarfe biyu Maryama ta shigo gidan tana tafiya tamkar ba za ta taka ƙasa ba sabida gajiya ta wuto matsakaicin tsakar gidan nasu ta shigo zuwa falon gidan Cikin sa a tana sanyo kai cikin falon idanunta ya sauka akan Hafsatu da cikin jikinta ta yi saurin kawar da kanta ta raɓa Hafsatu za ta wuce sai Hafsatu ta yi ƙarfin halin kiran sunanta,

“Maryamah”

cak ta tsaya ba tare da ta waiwayo ta dubi matar uban nata ba

Hafsatu ta sake cewa,

“Don Allah ki taimaka ki amso min batir a shagon nan kusa damu don Allah!”

juyowa gaba ɗaya tayi ta zube idanunta akan Hafsatu ta kalleta kamar ba za amsa kuɗin ba sai kuma ta karba batareda tace komaiba ta raɓata ta fice don zuwa yi mata saƙon.

Ajiyar zuciya me sanyi Hafsah ta sauke tana jinjina irin wannan halayya ta Maryamah gashi ita Kuma kaman mayya Allah ya saka Mata kaunar maryamah din cikin zuciyarta.

“Gashi!”

Shine kalmar da Maryamah ta furta da muryarta me nutsuwa lokacin da ta shigo cikin falon tana miƙawa Hafsatu manyan batira biyu da ta siyo mata.

Bayan watanni biyu cikin Hafsatu ya shiga watan haihuwa wata ranar asabar da misalin ƙarfe shida na safe naƙuda ya kamata aka kaita asibiti.

Bayan ta sha matuƙar wahala ta haifo kyakykyawar yarta mace fara da ita babu in da ta baro kamannin Hafsatu tamkar an tsaga kara.

Malam Adamu da maƙwafciyarsu Iyah me ƙosai dattijiya me shekaru hamsin su ne ke tsaye daga bakin labour room ɗin suna dakon haihuwar Likitar ta fito ta sanar da su an sauka lafiya tare da miƙa musu Babyn wacce aka naɗeta cikin showel da kayan sanyi farare ƙal

Hannun Malam Adamu har rawa ya ke yi lokacin da ya amsa jaririyar yana ƙare mata kallo wani irin ƙaunar Yarinyar na huda zuciyarsa Ya yi mata addu’a tare da miƙawa Iyah ita yana kutsa kansa cikin ɗakin da aka fito da Hafsatu bayan an gama kintsa ta ganinta cikin ƙoshin lafiya ya sanya shi yin hamdala da jin ƙarin farin ciki mara misaltuwa.

Bayan sun dawo daga asibiti zuwa gida ne Iyah ta wanke jaririyar tas Aka sake naɗeta cikin kayan sanyi sai a lokacin Umma da Maryamah suka shigo ɗakin don ganin Baby.

 

 

 

Maryamah tun kallon farko dataiwa babyn taji jikinta na neman sanyi sbd haka kawai taji kaman qaddarartace aka haifo Mata.

Hadeeza ma bayan ta gama ƙarewa jaririyar kallo ne ta aje ta tana duban Hafsatu ta miƙe tana cewa

Hadeeza ma bayan ta gama ƙarewa jaririyar kallo ne ta aje ta tana duban Hafsatu ta miƙe tana cewa,

“Allah shi raya mana ya baki lafiya.”

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button