Hausa Novels and Stories

Mijin Malama Page 1

Sponsored links

A lullume garin yake, sakamakon yanayin sanyin da ake ciki, wanda ya fara tun watan Ogusta zuwa watan da ake ciki na Nuwamba. Hazo ne ya yi wa samaniya ado, ga iska mai ƙarfi dake ta shi tana ƙara haddasa sanyin shiga jika, yanayin hunturun daban yake dana ko wacce shekara. Mafi yawanci lokuta a irin wannan ƙarnin manyan cututtukan da suke gaba da sanyi suka fi ta shi, irin su mura, asthma, sikila, ciwon ido, lamoniya, bushewar fata, haɓo, hatsarurruka a titi da sauransu.

 

Daidai by pass na First bank motar su ta tsaya akan titi saboda go-slown da hazon ya haɗa, tafiyar 9min (4.8km) ce tsakanin Lodge Road zuwa Aminu Kano teaching hospital. A hankali ta ɗago kanta dake sunkuye tun shigarta cikin motar, fararen Idanunta dake maƙale cikin farin Glasses mai ɗauke da photochromic ta watsa akan titin a nutse. Da ƙyar ta fisgi numfashi saboda a ƙirji yake tsaya mata.

“Jeederh!”

Latifa dake zaune a mazaunin driver hannunta riƙe da string motar ta kira sunanta, tasan ta ji ta sarai don haka bata buƙatar ta amsa, Latifa ta ci gaba da cewa. “We live by our own destiny, kuma Allah na son mu haka, You should not worry about that”

Sai a lokacin Majeederh ta ɗan juya kaɗan jikinta a kame tana curewa waje guda, ji take kamar ita kaɗai ke jin sanyin, duk da cewa Latifa ta rufe Glasses ɗin motar ta kashe a.c.

Baki ta buɗe ta cikin liƙab ɗinta za tayi magana,sai kuma tayi shiru can dai ta ce.

“Worry?” “Kamar haka na ce” cewar Latifa “Kada ki yaudari kan ki dole kina cikin damuwa, duk yadda ki ka kai da zurfin cikin ki, nasanki tsayin shekaru talatin da biyar, komai da komai naki na sani, After that, I am your friend”

Malama Majeederh jin ta kawai take bata fahimta, gangar jikinta ce kawai a motar, tunaninta, nutsuwarta gabaɗaya sun yi ƙaura daga gare ta. Kalaman Abbu su ne suke mata amsa kuwwa! A kunnuwanta.

Latifa bata gaji ba domin ko Aku zata shafa mata lafiya. “Ki zo ki aure Mijina Majeederh zamu zauna lafiya,na gaji da ganinki haka ba aure, na kasa jure yanayin ke ake faɗawa magana ni nake jin zafinta a zuciyata”

 

Cikin sauri ta juya ta kalli Lafita a ranta tana ayyanna girman wautar Latifa, corner Lafita tayi da kan motar tare da sulalewa gefen gwalta ta shiga cikin asibitin Aminu Kano kai tsaye!

“Yes,Malama Majeederh Abdul’aziz Khan” ta ci gaba da driving tana faɗin “Sweetheart ya amince zai aureki, Kinga amintarmu zata sake ƙarfi, ba zan taɓa ɗaukarki matsayin kishiya ba, ki amince Please Please Jeederh”

 

“Ke da mijinki kuna buƙatar ganin psychiatrist” Malama Majeederh ta furta a nutse cikin sanyin murya. Dariya kawai Latifa tayi tana girgiza kai, a ranta ta saka dole tayi forcing Jeederh ta auri mijinta, parking tayi a inda aka tana da domin ajjiye motoci. Ita ta fara fitowa hannunta riƙe da key ɗin motar sai waya, ganin Majeederh bata fito ba ya sanya ta zagawa just to find what’s happening. Hannu Majeederh ta saka ta buɗe murfin motar, tare da zuro ƙafarta waje.

Sai a lokacin Lafita ta lura da yadda farar ƙafar Majeederh ta kumbura har wani ƙyalli take, yanayinta ya sauya gabaɗaya yadda ta kumbura ta buɗe zai bawa kowa mamaki. Da ƙyar ta yunƙura ta fito daga motar can ƙasan ranta tana kiran sunan ALLAH.

“Kamar mai suger? Wannan kumburin ya yi yawa Majeederh, Mami ta gani? Abbu ya gani?” A duk jerin tambayar da Latifa taiwa Majeederh ba wacce ta amsa ko inda take bata kalla ba ta nufi ɓangaren data zo.

 

Da yake Dr Jamal ya san da zuwan nata domin shi ya bata appointment ya sa kai tsaye ta kira number shi, yana ɗagawa ya ce ta shiga. Latifa ta miƙe zata bita zuwa office a kame ta ce. “I need Privacy”

“Take your time” cewar Latifa tana watsa hannu. Brown ɗin Abaya ce a jikin Majeederh, wacce ta amshi fatarta, sai babban hijabi daya sauka har ƙasa wajan ƙafafuwanta hannunta sanye da safa, fuskarta rufe da liƙab ga Glasses ɗin da ya yiwa idanuwanta murfi. Babu abinda ake gani a jikinta sai ƙwayar Idanunta ƙafarta kuma hijabi ya rufe. Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, budurwa ce bata taɓa aure ba shekarunta Talatin da biyar ciff a duniya, cikakkiyar Malamar addinin Musulunci ce, ɓangaren boko ba ba a barta a baya ba.

Zaune ta samu Dr Jamal suka gaisa cikin fara’a ya ɗakko wani babban file ya ajjiye gabanta tare da zaro x-ray ya ɗaga sama ya ce.

“Finally, bayan tsayin shekaru biyu yau mun samu damar gano abinda ke damunki”

Wahalallan numfashi ta sauke a ɓoye,tana yiwa Ubangiji kabbara.

Ta juya idanunta alamar tana son jin me bincike ya nuna? Dr Jamal ya ce

“Mun sha wahala, ko na ce muna kan shan, sai dai duk wacce zamu sha bayan taki take”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button