Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 1

Sponsored links

Gurin gate ta nufa a guje kamar wacce aka biyo, ganin haka yasa securities din gidan suka taso da sauri suna kokarin tareta dan basu manta da tashi hankalin da aka shiga last time data gudu ba…….

“Don’t touch her! Kar wanda ya taba ta!!!”….

Deen ya fada cikin daga murya ganin kowa binta yake yana kokarin kamota….

“Ku tabbatar ko ina a rufe yake!! Amma kar wanda ya sake ya tabata!!”……

Nan aka shiga duba gates din gidan ana tabbatar da cewa a rufe suke……

Shareta Deen yayi ya tafi gate din da tabi ta fita wanchan lokacin dan ya tabbatar ko shima a rufe yake, yana zuwa yagansa a rufe alamun angane an rufe kenan……

Dawowa harabar gidan yayi yaganta tsaye sai masifa take yiwa mai gadi wai ya bude mata kofa ta fita ita bazata zauna ba, mami da Umm na tsaye sai rarrashinta suke amma taki kulasu……

“Saif anya bazaa kira malamai ba kuwa? Lokaci daya yarinya ta birgice haka?”……

Cewar mami tana dafe habarta…..

“There’s no need for that, ku shiga ciki kawai, I’ll handle her!”……

“A’a nidai hankalina be kwanta ba, let me go get my phone”……

“Gaskiya dai gwara asan abinyi, this is not a small issue saif”…..

Umm ta fada tana bin bayan mami dan suyi shawarar abinda ya kamata ayi……

Hade rai Deen yayi ganin yanda securities din gidan suka zuba mata ido, yayi kwafa yace;

“Before the count of three kowa ya bar compound dinnan nonsense!”…….

In a blink of an eye kowa yabar gurin saboda ba karamin tsoron bacin ransa suke ba dan yanda suke tsoronsa ko Mami basa tsoro haka, abu kadan sai ya yiwa mutum illa kuma ba yanda mutum ya iya, tsaki yaja yana harararta yace;

“Kinzo kina yiwa mutane hauka ba dole ayita kallonki ba, yan iska kawai!”……

“Please open the door for me”….

Ta fada a hankali kamar me tsoron magana, abinda takeji yau haryafi na rannan shiyasa har ta kasa fita a labe, ji take kome zaa mata wallahi saita fita daga gidan….

Yatsunsa guda biyu yasa ya bige mata lebe, a take gurin ya dan tsage saiga jini ya fito kadan……

Wani uban ihu ta rusa kamar wacce aka chakama wuka yayi saurin toshe mata baki da hannunsa…..

“Kinga kinsa rashin kunyarki tasa na ji miki ciwo ko? Daga dan taba lips dinki shine zakiyi ihun munafurcin da kika saba salon su Mami suce na miki wani abu?”……

“Meya sameta haka?”….

Umm da jin ihu yasata ta fito da sauri take tambaya…

“Nothing much, ihu kawai takeyi”….

“Meye haka? sake mata baki mana“….

Sai a lokacin ya tuna ashe ya garkame mata baki, hannunsa ya zare daga bakinta ya zaro handkerchief yana goge mata dan jinin daya fito…..

Wani ihun dayafi na dazu ta kara saki sai kuma ta zube kasa a sume….. Saura kadan takai kasa yayi saurin tareta, garin haka har bige hannunsa yayi be sani ba….

“Ya Salam yarinyar nan na ganin rayuwa saif, muje ciki”…….

Karo sukayi da mami dake shirin fitowa taga sun shigo saif rike da ita a hannunsa….

“Yanzu nake shirin fitowa, yana ganku haka?”….

“Suma tayi wallahi yaya”

“Ikon Allah, yarinyar nan na ban tausayi wallahi”…

“Kedai bari she’s really going a lot, Allah dai ya bata lafiya”….

“Ameen ya Allah”…

“But saif why is she always passing out? Anya babu rashin jini a lamarin yarinyarnan kuwa?” …..

Girgiza kai yayi cikin tausayawa yana kallon fatima zainab yace;

“She had kidney failure!”….

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel! Kidney fa kace? How sure are you?”….

“I’m very sure Doctor, namata general check up, duka kodanta is damaged, I don’t even know how”….

“Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha, yanzu duk kasan da wannan shine kayi shiru?”……

Cewar Mami da take ta sallallami….

“I just found out today”….

“And what were you waiting for da bakayi proceeding da dialysis ba? Innalillahi this is too much for her”…..

Umm ta fada kamar zatayi kuka….

“Transplant nakeso a mata, I want to give her my kidney!”……

Shiru ne ya biyo baya kamar wa’yenda aka daukewa wuta, su mami shock suka shiga jin ze bata kodarsa bayan ko sanin wacece ita beyiba, toh why is he willing to sacrifice this much for her?……

Ganin sunyi shiru yasa jikinsa yayi sanyi, durkusawa kasa yayi ya shiga rokonsu dan shi duk a tinaninsa basu amince bane…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button