Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 2

Sponsored links

Shiru ne ya biyo baya kamar wa’yenda aka daukewa wuta, su mami shock suka shiga jin ze bata kodarsa bayan ko sanin wacece ita beyiba, toh why is he willing to sacrifice this much for her?……

Ganin sunyi shiru yasa jikinsa yayi sanyi, durkusawa kasa yayi ya shiga rokonsu dan shi duk a tinaninsa basu amince bane…..

“Mami, Umm pls don’t say no, wallahi she’s in a very critical condition and I don’t want to lose her, idan kuka cemin baku yarda ba wallahi komai ze iya faruwa”……

Shafa kansa mami tayi murmushi dauke akan fuskarta tace;

“My son!”…..

Dagowa yayi da sauri yana addu’ar suce sun yarda dan shi a shirye yake ko yanzu a tafi a cire nasa asa mata…..

“I’m so proud of your kind heart! Ada nace I won’t come back to this conversation, but I’m asking you again today, are you in love with her?”……

“No mami, Fisabilillahi zanyi badan komai ba trust me!”…..

“Nayarda, we’re not against bata kidney dinka dakayi niya but the issue is kasan one of your kidney isn’t functioning well ko?”…..

“Nasani, me lafiyan zan bata mami inyaso sai in cigaba da kula da kaina, I’m a medical doctor it’ll be easier for me”…..

Jan hancinsa Umm tayi cikin barkwanci tace;

“A’a gaskiya ban yarda ka bada naka ba, ina lefin mami tayi maka sacrifice din tinda duk ta fimu lafiya”…….

“Sai in masa, meye a ciki? Sis haka ya kamata ma ayi”…..

Dariya tayi tace;

“Ko kuma ni in bada nawa ba, amma gaskiya saida in siyar, saif nawa zaka siyan mata nawa?”…..

“No duk ku rike naku nizan bata nawa, ku kun riga kun tsufa”…..

“Kajimin yaro, daga abin arziki? Ko tsoro kake kar ince kaban 500m?”…..

Murmusawa yayi yana kallon fatima zainab da yaga kamar tana dan motsawa yace;

“Gaskiya kin rena arziki na Umm, 500m dinne zanji tsoron baki, naaaaah”….

“Nasani ko…….”….

Wani kuka da fatima zainab ta fashe dashi ne ya dawo da hankalinsu kanta banda Deen da tin dazu hankalinsa ke kanta…….

Daidai nan kuma malaman da Mami tasa a kirawo suka karaso, kiran landline din parlourn mami akayi mami ta dauka tace a shigo dasu cikin gidan……

Daidai shigowarsu ta sake kwalla wani kara me karfi da saida gidan ya amsa gabadaya…..

Babu bata lokaci suka fara mata karatun alqur’ani me girma, a take ta fara fizge fizge harsu mami suka kasa riketa, da sauri Deen ya rukota ganin daya malamin na neman kama hannunta, shifa shiyasa tin farko beso ankira malami ba kar azo garin rukiya ayita tabata…..

kam kam ya riketa sannan ya shiga tayasu karatun…

Tin tana ihu muryarta na fita har muryarta ta dishe ta koma ihu a hankali, saida taga ba sarki sai Allah sannan ta fara magana

“Garin yaya akayi sake akanta haka? Yanzu sai munyi da gaske kafin ya rabu da ita dan ya riga ya shiga jikinta sosai, alamun kuma sun nuna ya dade tare da ita”……

“Ya hayyu ya kayyum, toh meye abunyi mallam?”…

Umm ta fada batareda ta bashi amsar saken dayace anyi ba dan batasan me zata fadamasa ba tinda itama batasan komai akanta ba…….

“Ai wannan din karamin matsala ne akan sihirin dake jikinta!”….

“Sihiri kuma? Oh Allah ka kawo mana dauki”…

“Karku damu da yardar Allah komai ze daidaita, mu da Allah muka dogara!”…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button