Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 5

Sponsored links

zan fito kenan Naga wata katuwar mota me kyau tayi parking wani mutum kyakyawa baki ya fito daga motar shi baza a kirashi da matashi ba sannan baza a kirashi da babban mutum ba,tunda ya fito yake kallona kamar maye,da sauri na tafi na dane saman machine din da muka zo tare,da Sauri mutumin yace dan Allah malam me machine tsaya,nace Kai Musa muje,Mutumin yace karka tafi zan baka kudi,Musa ya tsaya cak da machine na bata rai cike da masifa nace Musa muje nace fa,Musa yace Allah ya gani bazan tafi ba kina ji dai yace zai bani kudi haka Kawai ki cuceni ke nawa zaki bani? to ba inda zani,kinga dan Allah ki saurare shi yayi sauri ya barmu mu tafi,baki na turo gaba tare da kallon mutumin nace Ina jinka,Murmushi ya saki yace Kawai kwatancen gidanku zaki bani idan nazo sai na fada Miki dalilina na tsaida ku,Shuru na Masa har ya gaji da tsaiwa yace Ina jinki princess,Harara na watsa masa,Musa zancen ya karbe ya Fara Masa kwatancen gidanmu yace idan kazo kauyen namu kace gidan su Rabi Yar tsuntuwa ko gidan Dagaci,Murmushi mutumin yayi yace nice name sunana Alhaji Mas’ud amma kowa da Alhaji Kutama ya sanni,baki na tabe Ina kallo ya bawa Musa dubu biyu,Musa sai Murna Yana godiya yace zaku iya tafiya,sai lokacin Musa yaja machine muka tafi Yana murna,nace Wlh Musa kayi asara tirrr da Kai,dariya ya sake yi tare da furta ba komai naji.

Ina sauka a kofar gidanmu na biya Musa kudinsa na shige gida da sauri,Ina shiga Dagaci ya hauni da masifa da bala’i,Gwaggo tazo ta fisge ledar lemukan tare da dungure min kai tana furta gantalalliya anyi gadon karuwanci,Aunty Amarya tace yo matar da aka tsinta yashe a titi cikin jini ai kinsan bata da uba Yar shege ce ai,bance komai ba sai ga Mairo da Gaji sun fito daga daki ashe fitata suka shugo gida,Gaji ta kalleni tace jaraba ja’iba haihuwar kwararo na tsaneki wlh Gwaggo ban San ya akayi Yar shege take da kyau haka ba,kalli duwawunta Lodi guda Nawa Kuwa sai kace Kullin Sugar gata Fara Ni Kuwa wankan tarwada Mairo ma haka,duk inda tazo ta tsaya Muka tsaya dole ita za a dinga kallo,kalli duwaiwaka sun Bude,Aunty Amarya tace ai sabo da maza ne yasa Kwankwaso ya bude inda Zaki San Yarinyar nan tasan maza matan aure ne kugunsu yake fashewa amma gashi ita tun tana budurwa,Dagaci da shigowarsa kenan yace Allah ya bata sa’a tayi cikin Shege a gidan nan taga yanda ake daddatsa mutum da ransa a gidan nan.

Ina jinsu ban kulasu ba sai da na gaji nace baiwar Allah ce dai, na ebi ruwa nayi wanka nayi Sallah naje wajen Gwaggo a hankali kamar almajira na duka nace Gwaggo Zan samu abincin? Aunty Amarya da kinibibi ta amshe zancen da furta ke dalla algunguma ba abinda Kika iya sai ci shegen ci kamar Yar Jaka da wata jar Fuska sai kace zabiya na Mura,a hankali nace kuyi hakuri kaddara tace tazo haka da ace akwai Iyayena baza ku ganni a nan b….kafin na karasa duk masifar dauriyata na fashe da kuka me tsuma zuciya na mike Zan tashi Mairo ta fito daga daki sanye cikin Riga da wando damammu sun Mata kyau tace dan Allah Gwaggo ku bata abincin nan ko a huta da jaraba,Gaji Kuma tace ku kyale Yar iska tayi kukan jini yarinya sabo da samun sarari tusar asuba shike nan ana magana sai kuka,Gwaggo lokacin su Audu yara sunci abinci sun jagwalgwala shi ta jawo ragowar ta Kara wani dan kadan akai ta tura min tana furta gashi Nan sarkin ci ciki Kamar zani dauki ki tafi ko na hambareki, Dauka nayi da sauri sabo da tun safe banci komai ba na koma dakina Wanda ba komai sai tabarma sai Ghana must go wacce kayan sawata ne a ciki,Zama nayi na lashe abincin tas na fito da kwanon,Muna yin Sallah Isha na fito nayi wanke wanke nasan ya zama dole da dare ma bana hutawa,Ina kwance a dakina bacci ya Fara daukana Dagaci ya shigo har dakina yace ke tashi na aikeki shago ki siyo min battery Zan saka acocilata wato touchlight,mikewa nayi na duba agogona wani na roba Wanda ake Kira da lado lado karfe goma na dare ga shagon da nisa dama komai dare ni suke aike ba ruwansu da cewar ni macece.

Haka na tashi Dagaci sai kallona yakeyi Kamar maye,kunya ta kamani,bawan Allah ya Fara lasar labbansa nidai na zurma Hijab na karbi kudi na tafi da sauri a tsorace haka naje na siyo na kawo Masa ya karba tare da shigewa dakinsa.

 

Dama kwanan Aunty Amarya ne yau Dagaci akwai abinda ya kulla a ransa fada yake so ya takali Amarya, Amarya ta Sha wankanta tana kamshi tazo ta kwanta a bayansa tare da rungumeshi, cike da masifa yace ke mene haka ya naji kina tsami,Amarya ta bude baki kafin tayi magana cikin masifa da bala’i yace tashi ki bar min dakina kazamar banza shi yasa Gwaggo take birgeni,Amarya kishinta ya motsa ranta ya baci ta mike cikin fushi ta fice daga dakin Dagaci ta koma dakinta tare da kwanciya,karfe biyu na dare Dagaci ya fita daga dakinsa nayi nisa a bacci kamar a mafarki haka naji ana shafa min nono tun Ina Jin Kamar ba gaskiya ba sai naji gurnanin mutum Yana ahhhhh…uhhhhhh Yana ci gaba da lagude min Boobs da sauri na farka na bude baki zan tsala ihu naji an rufe min baki da hannu daya shi Kuma Daya hannun ana shafa min kirji,jikina ne ya hau rawa Kamar an jona min shocking,Dagaci yace ke ke ke shiiii kwantar da hankalinki Baban Mairo ne Dagaci yi Shuru ki bani hadin Kai idan ba haka ba sai na koreki daga gidana Kuma kin San baki da wajen zuwa baki da kowa sai ni a duniya Zan iya yankaki Babu Wanda zai ji labari sabo da haka ki yarda dani Kawai ai dama kina bawa mazan banza ga Wanda ya rike ki tun kina tsumma ni sai a barni a banza ai kamata yayi a fara kosar dana gida sai a kaiwa dawa,fisge fisge nakeyi da Shure Shure amma ya rikeni Yana furta zai yankani Ina ji Ina gani zai min fyade ta karfi,Takalmi na jawo da kyar cikin duhu na shiga kwalawa Dagaci a kansa ta ko ina wanda ba shiri ya sake ni, Amma mayen ya sake dawowa ya rikeni ban San Ina na cafka ba da bakina na gartsa Masa mugun cizon da ba shiri ya sakeni yaja baya azaba tasa ya mike ya bar dakin ganin zan tona Masa asiri.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button