Hausa Novels and Stories

Dare Daya Hausa Novel Page 17 – 18

Sponsored links

A hankali ya miƙa mata hannunsa ta daura nata akai ya ɗago ta wata ƙara ta saki tana cije lips dinta yabi bakinta da kallo masha Allah dan mitsili dashi yasha lipstick sai shaning yake ƙafarta ya kalla subhanallah ya furta cikin zuciyarsa sbd ganin kamar tayi targaɗe a ƙafar kuma daidai idon sawu(ɗan gwuiwa amma na ƙasa gurin duga dugi) tsaye ya miƙar da ita sai ruwan hawaye take tana yarfe hannu mannal sai faman jera mata sannu take itama tayi narai narai da ido kamar zatayi kuka staff dinda ya kawo musu ruwa shi yaje ya jira manager ya fito cikin sassarfa yana subhanallah MAHELET garin yaya Hakan tafaru nan aka gaya masa yanda akayi hannu yasa ya ciro waya zai kira momma tace dan Allah karya kirata momma nada hawan jini kuma bataso a ɗaga mata hankali daddy please ka gyara mata ƙafanta kamar yanda ka gyarawa UNCLE gaba ɗaya suka haɗa ido suna kallon yarinyar murmushi ta sakar musu tana cewa my Daddy is a professional doctor don’t worry Aunty kinji yanzu zai gyara miki ƙafarki hakama Uncle da yaji ciwo a ƙafa ni na riƙe sa Daddy ya gyara masa ƙafa amma ke basai na riƙe kiba ladies are stronger than man gaba ɗaya gurin aka kwashe da dariya amma banda DADDY Sam bayason yawan surutun mannal batajin magana ko ƙadan

 

Cak ya dauki MAHELET ya nufi waje da ita manager na biye dashi yana riƙe da hannun mannal da keta faman basa labarin daddyn ta yarinyar akwai shiga rai ga surutu MAHELET kuwa gaba ɗaya taji tama kasa motsin ƙwarai sbd yanda ta jita a jikinsa sai zuciyarta ke bugawa da sauri sauri Tanaji kamar ta saki fitsari sbd tsoro bayan motar sa ya buɗe ya Sakata mannalta shiga ya mayar da ƙofar ya rufe shida manager suka shiga gaba ya jasu bai tsaya ko inaba sai Mannal clinic yar ƙaramar hospital ce kuma private tsaf tsaf, babu wasu mutane da yawa saidai akwai patients wadan da aka kwantar da yawa nurses ke kula dasu shiyasa babu wasu masu zaman jiya da yawa kuma sai ƙarfe hudu ake zuwa ganin mara lafiya saida yasa aka bude mata files kafin ya shiga da ita aka fara yimata hoto sukaga buguwace kawai, office dinsa ya kai ta ya kwantar da ita yace karta yarda ta dago idan ba haka ba saiya saɓa mata ɗaga masa kai kawai tayi sbd tsaronsa da takeji wani liquid ya dauko ya murza mata a ƙafar, yana murza ƙafar ta saki ƙara ta dago ta riƙe masa hannu gam ta saki kuka dan Allah ka barmin ƙafana haka wlh naji sauƙi momma tanada wani magani zata shafamin idan nakoma gida tana magana tana kuka harda majina gashi ta riƙe hannunsa gam cikin nata, ɗan ƙaramin tsaki ya zaki ya fisge hannunsa yasa hannunsa daya ya riƙe duka hannunwanta biyu ya shiga murza mata ƙafar yana liliya mata tana yakucin sa tana turesa harda citso ta gatsa masa a hannu amma bai dena bah saida ya tabbatar ya Bazar mata da jinin da ya kwanta a ƙafar…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button