Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 10 Hausa Novel

Sponsored links

Khalil na xaune yana waya a bakin gate mai gadi ya karaso wajen daga boys quarters, Khalil ya saka wayar a aljihunsa bayan ya gama, Aminu da har ya xauna ya mike yace “Aa bari in baka waje ka ci gaba da wayarka….” Khalil yace “Na gama” Aminu ya dawo ya xauna yana kallonsa yace “Na lura baka son kayi waya a gaban mutane saboda hayaniya ko?” khalil yace “Haka ne” Aminu yace “Ina can tare da su Saminu muna ta jajanta lamarin tsuntsayen nan da suka gudu, abun da mamaki da al’ajabi, sun kusa shekara daya da rabi fa a wajen ba a ta6a nemansu an rasa ba sai yau” Khalil yace “Ai gwara da suka gudu kar xunubanta ya dinga shafarsu su ma”

Aminu ya kyalkyale da dariya yace “Wllh baka da dama, ni tashin hankalina abincin da tace xa a hanamu, in an hanamu abinci ya xa mu yi? Ba fa kanta kenan, duk da nasan uwarta baxata yarda da hakan ba, amma makira ce tana iya biyomu ta kwace idan an kawo mana” Khalil yayi murmushi kawai, Aminu yace “Amma fa kana bani tsoro da mamaki yanda kake nuna mata baka shakkarta, akwai wani littafi da na ta6a saurara a shafa labari, kaga yanda ta sa ka gaba haka? To haka ita ma yarinyar littafin ta sa mutumin gaba yana aiki a kampanin babanta ita kuma ita ce manaja a kampanin, tayi ta masa walakanci da rashin mutunci daga baya ta xurma sonsa in gaya maka, To sai….” Dakatar da shi khalil yayi yace “Me kake nufi?” Aminu ya gyara xama yana washe baki yace “Toh wa ya sani ko hakan xai iya faruwa wataran, barin taga sambalele me dogon hanci, ka fa san matan nan ba alkibla garesu ba….” Khalil yace “Ta wahala…. banda abun ka ina ita ina talaka? Sai dai kuma bata san wani talakan ma ko da kudi aka hadasa bazai saurareta ba, in dai kamar ni talakan yake wllh ko kallonta baxai yi ba” Aminu ya gwale ido, sai kuma ya tuntsire da dariya yace “Yanxu kana nufi misali yau ace maka gata nan ka aura baxa ka aura ba?” Khalil yace “Misalinka ba me yiwuwa bane har duniya ta nade, don kuwa da in aureta gwara na aura Krista, ko kuma in dauwama ba auren, kai kasan darajan da Allah yayi ma ɗan Adam kuwa? To bari kaji ko da kudi wannan yarinyar baxata tsaya inda budurwata take ba, ga ta dai yar talakawa kamar ni amma ita wannan fitsararriyar baxata tsaya inda xata tsaya ba wllh….”

 

Aminu yace “Aa dole xaka ji haushinta wllh, nima kuma ina taya ka jin haushinta kullum, ji tijaran fa da tayi maka daxu, banda yanayin rayuwa a ina xata ganka har ta cakume kwalar rigarka tana dungure kanka tana maka munanan xagi, a ƙalla ai xaka bata kusan shekara goma na sani, amma ta maka wnn cin mutunci da tijara gaban Nihal da kawarta, ba ma wannan ba ji yanda ta dau bahon ruwa gaba daya ta juye maka a cikin jama’a” Khalil yayi wani Murmushi bai dai ce komai ba, Aminu yace “Ni dai yau ace min ga ta in aura xan yarda in aureta ko don kudin babanta da kuma halaccinsa, sai kuma in saita mata xama….” Daga sama har kasa khalil ya kalli Aminu, bai san sanda yayi dariya ba yace “Kai ta kudin kake kenan” Aminu ya washe hakora, Khalil ya girgiza kai yana Murmushi, Aminu yace “Wllh ni fa naji dadin bude kejin nan da aka yi tsuntsayen suka gudu, Allah ne ya bi min hakki na abinda ta min jiya a kan su” Khalil yace “Ku kuka bar mata tsuntsayen suka kai har warhaka a gidan ai” Daga haka ya mike ya bar Aminu a wajen xai je yayi alwala kafin a kira isha’i. Nihad na komawa dakinta taga missed calls din Husnah da yawa, ta xauna gefen gado ta kirata, yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad ta dinga jin hayaniya tace “Kina ina haka?” Husnah tace “Mozida suite” Nihad tace “Me ake yi a nan?” Husnah tace “Wllh na manta ban gaya maki ba shekaranjiya a schl, Abokin saurayin Naf ne ke birthday, nayi ta kiranki tun daxu baki daga ba dama wai in gaya maki” Nihad tace “Toh ai tun jiya ya kamata ku gaya min, kuma yanxu kinga dare yayi” Husnah tace “Kashhh, kinga ke matsalarki kenan Nihad, karfe takwas din ne dare?” Nihad tace “Toh ta yaya ma xa ayi in taho babu me kai ni, kinsan wawan nan har yanzu Abbanmu bai koresa ba wa yasani ma ko asiri yayi ma yan gidan duk suke supporting dinsa, Umma ce kadai ke bayana a ko da yaushe, throughout na xuba ido yau in ga ko xai tafi ban ga ya tafi ba” Husnah tace “Kinsan abinda zai faru?” Nihad tace “Aa” Husnah tace “Yanxu xa mu fita mu karo wasu wine, kawai ki san duk yanda xa ayi ki fito mu hadu a wannan katon supermarket din na anguwarku” Nihad tace “Kar fa ku bar ni inyi ta jira Husnah” Husnah tace “Haba wani jira, bayan gashi nan yanxu ni da Naff da Sumy za mu fito” Nihad tace “Okay, bari a shiga masallaci sbda yan sa ido, sai in fito” Husnah tace “Sai mun hade, kar kuma kice ban gaya maki ba, A abokan celebrant din har da ‘ya yan gwamnoni, shiga ce ta kece raini xa ki yi, duk da nasan ki ba wasa” daga haka Husnah ta katse wayar. Nihad ta mike ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje jin ana kiran isha’i, ta dauro alwala ta fito da sauri, tada sallah tayi bayan ta idar ta fito da wani ubansun gown dinta ja wanda Aliyu ne ya siyo mata daga kasar waje ta saka, ko make up bata yi ba duk ta harhada kayan make up din da turarruka a wani babban jakarta da xae iya daukan hijab da takalmi da tarkace da yawa, tana jin an tada sllh sae da ta jira aka yi raka’a daya snn ta fita da sauri bayan ta sa ma dakinta makulli, tayi surveying parlor don tabbatar da babu kowa a ciki, ko wa na dakinsa, dama kuma gidan ana magrib kowa ke shigewa daki babu me shiga privacy din wani, sai kuma washegari idan an hadu wajen breakfast, yawanci da yake a bangaren Umma dakinta yake, Umma kan shigo taga ko tana waya kuma da wa take wayar, to dai ta sa ma dakin makulli ko taje xata shiga xata ji sa a kulle, da sauri da sauri ta fito compound nan ma ta ci sa’a babu kowa, duk suna masallaci, kan kace me ta bar compound din ta kama hanyar inda supermarket din da Husnah tace ta jirasu yake, tana isa wajen ko minti biyar ba ayi ba sai ga motarsu Husnah suka dauketa suka wuce, Husnah tace “Yanxu da Habibu na nan nasan da kansa zai xo ya daukeki idan aka gama partyn ko karfe sha biyun dare ne, yanxu dole kinga sai mun ajiye ki a nan after the party in ba dai saurayi kika yi a can ba” Nihad dai ta xuge jakarta ta fara gyara fuskarta xata yi light make up.

Wajen partyn ya hadu iya haduwa kamar yanda Husnah ta fada ai kam ya yan manya ne suka cika wajen, very dim light ne kunne a inda suke birthday din, babu abincin da babu da abun sha tun daga ruwa, lemo, wine, alcoholic drinks, kai komai da akwai a wajen, gasassun rago biyu aka bankare wajen, ga manya manyan pepper chicken… cake din da budurwarsa tayi masa ma kadai abun kallo ne… duk hayakin cigarette ya turnike wajen, an sha shagali iya shagali a birthday din nan, abinda Nihad bata yarda da shi ba shine ta sake ma maza fuska a wajen, xata dai shige cikin kawayenta mata amma bata xama cikin maza, ko da kana ta shisshige mata ma banxa xata yi da kai tayi ta danna waya, Husnah ta kwankwade glass din wani alcoholic wine, glass na biyu kenan ta sha, su Naf da sauran yan matan wajen su ma duk wine din suke sha, Husnah na kallon Nihad dake rike da cinyar kaza da wani can drink a gabanta tace “Wllh ki ɗan dana wine din nan ya fi na wancan ranan dadi sannan shi wannan babu abinda xa ki ji idan kika sha, wllh soo cool” Nihad tace “Aa baxan sha ba drink din nan ya isheni” Zully tace “Ke dadina dake kwabsin ki yayi yawa, don Allah ki ɗan kurba idan bai maki ba sai ki bari kar ki sha, nima kinsan ai ban fiye son wines haka ba, amma tunda kika ga ina shan wannan ya kamata kisan ba karya” Nan duk suka mata caaa akan cewa ta ɗandana idan bata ji dadinsa ba sai ta bari, Husnah ta cika mata glass din gabanta tace “Kiyi sipping first ki ji” Nihad ta dauka ta kai baki ta kurbi kadan, bayan few seconds ta wara ido tana kallonsu tace “Waow its really nyc, it tastes good” Husnah ta kyalkyale da dariya tace “Ba na gaya maki ba da kin tsaya kin kwabsawa” Nan Nihad ta kwankwade wine din, Husnah ta kara cika mata glass nan ma ta shanye, Naff sai dariya take tana cewa “Wllh ki bar ta haka Husnah tam ni dai na gaya maki” Husnah tace “Toh meye a ciki ai baya wani bugarwa”

Haka dai Nihad ta sha wine tayi nak, party din da ba a karasa da ita ba kenan tayi ta masu layi a wajen, banda dariya babu abinda suke mata, Husnah tace “Kaii amma jininta ma bai da karfi wllh, ɗan wannan wine din shine xai bugar da ita” Nan suka ci gaba da shagulgulansu, Nihad kuwa ta kife kai a wajen sai bacci, ba a tashi birthday din nan ba sai karfe dayan dare, Husnah ba irin tashin da bata yi ma Nihad ba amma ta ki tashi, da ta dagota xata koma ta kife kai, wani abokin celebrant din yace “Na kama daki a nan why not kawai ku barta ta kwanta ta huta” Husnah tace “Aa nasan halinta tana farkawa xa mu samu matsala da ita, kawai dai kamata yayi mu ma a kama mana dakin dama dare yayi ba lallai a bari mu shiga schl ba yanxu, idan ya so duk sai mu kwana a nan” Ba don ransa ya so ba haka nan ya kama masu dakin, suka ciccibi Nihad sai dakin suka kwantar da ita saman gado, Husnah dai na ta kaffa kaffa da Iphone din Nihad a wajen tunda ta san halin wasu daga yan matan dake wajen. Sai kusan biyu suka kwanta a dakin bayan duk sun yi wanka.

Karfe hudu da rabi Nihad ta farka da wani axababben ciwon kai, da kyar ta mike xaune tana bin dakin da kallo, sai kuma ta sauka tana layi ta nufi kofar dake dakin wanda bandaki ne, ta kuma sani tunda sun saba lodging a wajen ita da su Husnah, tana shiga bayin bayan tayi fitsari taji wani amai ya taho mata, nan ta dinga kwarara aman tana rike da cikinta dake juya mata, da kyar ta wanke bakinta bayan ya lafa mata ta fito, bata sake komawa baccin ba sbda ciwon kai me tsanani da ya takurata, ganin biyar ya kusa ta ta6a Husnah da kyar, ta fi minti goma tana tada Husnah dake xuba minshari kamar wani kato, kafin ta bude ido cikin magagin bacci tace “Wai ya aka yi Nihad?” Da kyar Nihad tace “Don Allah wa xai yi dropping dina gida kafin yan gidanmu suyi noticing bana nan, asuba ya riga yayi”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button