Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 95

Sponsored links

Me chemist din kuwa da Gaji Suka je Suka sashi ya min sharrin ciki gaba daya yanzu bashi da kasuwa duk da ba a San me yayi min ba babu Wanda ke saurar chemist dinsa sabo da an bude sababbin chemist,Ni Kuwa Nawwar nasa ya bawa Bala Babban jari ya tura Masa dubu dari uku ya ja jari sai godiya yake min kamar ba gobe.

Tsabar son abin duniya na Papa kullum sai ya Kira Wise tun Yana Kira yace ya Kira ne ya gaisheta har ya saba da hira,Yau da dare cikin dare suna kwance da Maman Sabreen ya lallaba ya tashi ya barta ya fito Palo ya Kira Wise bugu Daya ta dauka da muryar bacci,yace Sorry na tashe ki ko kiyi hakuri na riga na Saba da ke nifa Ina ganin kamar mun wuce matakin da muke na gaisawa ni gaskiya sonki nake Yi Kuma aurenki zanyi idan kin amince, Wise tayi Murmushi a hankali tace gaskiya anya Kuwa to ka bani dai lokaci nayi tunani yace na baki farin cikina,kece ruhina,Wise tana jinsa tace ji mutumin banza Yar cikinka a fili tace na gode yace dan Allah ki soni karki ce a’a na Riga na baki Amanar zuciya….Amanar zuciyaaaaaaa yaji Mama ta fito tana tambaya uban wa ka bawa amanar zuciyarka? Dama abinda kake kenan kullum tsakar dare sai waya waya haba Yusuf Ashe amanata zaka ci kace baza ka min kishiya ba ka tuna Alkawari fa kayi min,Papa yace na karya shi yau shike nan bazan Kara aure ba ance idan ka Kara aure kofofin budi zasu Kara bude maka shike nan so kike nayi asara tsaki yaja yaci gaba da wayar, Wise tace Uwargida ce ne? Yace itace take min ihu,tace kyaleta kishi ne ni gaskiya Zan fasa auren naka yace kiyi Hakuri Dan Allah kyale wannan tsohuwar hakorinta fa sun Fara cirewa,nace Allah sarki bata da hakora yace ai duk na gaba sun zube tsufa ya kamata da gaske, Wise tace gaskiya kana bukatar sabuwar zuma,dariya ya saki Hahahahaha shi yasa kike birgeni,Mama tayi sororo tana ji yace kiyi mafarki na sannan ki gaishe min da kudadenki, Wise Ido ta zaro tace amma wannan ya cika mayen kudi har kudin Nawa ma na gaishe Masa da su,Yana Gama wayar Mama tace yanzu Yusuf ni zaka cewa hakorana sun zube kayi min sharri,Tsaki ya ja ya mike Mama ta cakumo shi ta kafa Masa hakoran a gadon baya tana cizonsa Yana ihu,tace wannan mene kace sun zube,ranar sabo da bala’in Mama basu yi bacci ba.

Jamcy ce taci kwalliya ta shigo gidan Nawwar a motarta tana parking ta fito ita ga tsagera tana tauna chewgum tana taku,taci sa’a su Star suna palona gaba dayanmu ta shigo ko sallama,Yar zabil tsawa ta Mata ke koma kiyi sallama,ubanki ma yayi kadan bare ke cewar Jamcy,Ina shegiyar da akace ta gagari kowa ba wacce ta Isa ta auri mijinta gani ni na zo Kuma sai na auri mijinki Nawwar na dade Ina sonsa,Star basu ce Mata kala ba Suka maidata banza ta gama zage zagenta Shuru,Wise ce ta dakko sabuwar hira ya dinkunan Kuwa kin karbo? Nace sai gobe Inshaallah,Jamcy bata hakura ba tace ana magana Kun maida mutum mahaukaci nan ma Shuru basu ce kala ba sai hirarmu muke ta zubawa Muna tafawa,taci gaba da cewa idan Kun hana Sabreen Zama ni nafi karfinku baku Isa ba,Nan ma shewa mukayi muka tafa Muna hirar mu,Jamcy ta kule Kamar ta hadiyu zuciya tayi tsokanar tayi Shuru sabo da bata da abin fada, Tsaki ta ja tace karuwan banza karuwan wofi Yan Iska duk Wanda yake ba dan sunna bane ai dole yayi haka,idan Kun haifu kuyi magana banzaye karuwai,Ni dariya ta bani Kawai kizo ba gaira ba dalili ki dinga tsokana,ba Wanda ya kulata duk magana intayi sai mun saki shewa wannan yafi Mata ciwo ta juya ta fice tana Jan Tsaki,ko da ta tafi ko zancenta bamuyi ba hirar mu Muka ci gaba,Wise tace Allah yasa ta dawo yanzu mun Mata abinda yafi komai ciwo to nan gaba jini da majina zamu hada mata.

Baffa kwance yake a dakin Iyamami saman gadonta ya sata gaba ya hanata sukuni,yace gaskiya ni a san yanda za ayi dani dan ni gaskiya ku Nemo min matata ai da zugarku yasa na sake ta kune kuka dinga zugani,Iyamami ta juyo da masifa tace kai kaci ubanka yau naga marar mutuncin yaro abinda kake ko Auta bazai Yi ba,Nema kake ka susuce ta ja tsaki,Baffa yaki tafiya yace Allah sai Kun Nemo min matata ba inda zanje ai da Yusuf ne da tuni kuna tausayinsa Ni shike nan kamar bare an ware ni ba a so na ya karasa da muryar tausayi,Nawwar ne ya shigo bayan sun gaisa Baffa yace Nawwar wato baza ka fada min inda uwarka take ba ko? to ai kafin a sameka ni ta sani ita na sani yanzu kazo sabo da uwarka ce ka fini zakewa,Nawwar shi kunya ma yake ji abinda Baffa ke yi, Ya hana kowa sukuni tashi yayi zai bar dakin Baffa yace sai na talauce tukun zakuyi bayani tunda so kuke ku ganni na zama abin Allah sarki a gari,Nawwar tafiyarsa yayi ya bar Baffa da Iyamami suna ta fama.

Satin Mairo biyu a Kaduna rannan sunje kasuwa da Sadiya kawarta ta sake ganin Rufaida Cele a kasko tana ta yiwa me shago masifa wannan waken suyar kace wani naira dari ta karu akai sabo da tsadar rayuwa ni a awarar tawa nawa ce ribata eyyeee Zan daina zuwa siyayya wajenka Dan Allah jibeka gaba Daya kamannin Yan Tanzania ne da kai,Haka tana mita me shago Yana dariya yace Cele tsiyarki yawa gareta,sai da ya gama zubawa ta dakko biscuits Kato me tsada tace alakoro na Sha shayi da shi,ta dauki kayanta tana juyawa taga Mairo a bayanta ta kafeta da Ido,tace baiwar Allah wai lafiya da wata fuskarki Kamar anyi kilishi da biri, Nuna Mairo tayi da yatsa ke dai da gani koko da miyar kuka sunyi saukar ungulu a fuskarki,Sadiya ta kalli Cele sanye take cikin tsohon leshi riga da zani tace ke wai ke bakya Shan kokon ne aikin banza,Cele tace Kutmar….ta duro ashar ta ajiye ledar wake taci kwalar Sadiya tace wa ya fada Miki Cele tana magana ana maida Mata da martani,karki ganni a Haka kina ganina Kinga Kalar shayi jikina duk shayi ne kwakwaran juyi nayi sai dai kiga Lipton da citta da kaninfari suna zuba kasa shegiya me kunnen bera ta sake jijjiga Sadi ya,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button