Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 1

Sponsored links

A hankali take bin ilahirin wurin da aka ajeta da kallo…this is the first time da ta taɓa shiga wani Company da sunan aiki,saukar da lulun idanun ta da suke a ƙaƙƙafe na rashin kunya tayi tana duban computer n dake gaban ta…huuuuu wani gwauron numfashi ta sauke a hankali tana gyara zaman mayafin da ta yane kanta dashi, shigar suit ɗin jikin take kallo kamin ta sheƙe da wani irin wawan dariya jikake wurin ya amsa hahahaaa…Saurin kallon ta ma’aikatan gyefen ta sukayi wanda hakan yasa Sumayya ɗaure Fuska tamau kaman ba ita tayi dariyar ba,wanda dama wannan al’adarta ce , komai ta nuna bata son raini…ganin yanda ta haɗe girar sama yasa duk rawar kan ma’aikatan wannan wuri mata da maza shiga hankalin su , a zuciyoyin su suna cewa ” wannan itama BOSS ce ,but aƙwai babban ta a sama zata daina wannan fuxgar ne haɗuwa ɗaya idon sukayi”. Ma’aikatan ke magana kowa da abun da yake saƙawa a zuciyar shi game da Sabuwar ma’aikaciyar tasu Wato Sumayya.

Ɓangaren Sumayya kuwa juyi take a kujerar da take kai kaman wanda ta saba hawan zuciyar ta ,tafff ƙugunta da cinyoyin ta suka cike kujerar ,saboda tsaban ƙiban ta da ƙasa Allah yabata hip da manyan mazaunai ka aza ta haura shekara ashirin da biyar in kayi mata kallon sace…. Nisawa tayi tana ciko wuya a zuciyar ta cewa take” Oh Sumayya wannan anya rayuwar da kika ɗauka ma kanki mai ɓillewa ce kuwa? Mtswww ɗan tsaki tajah a hankali kamin tace ” nida ba zama nazo yi ba ,naxo na saci kuɗin Company na gudu , ya za’a ajiye Ni anan wurin? Tayi maganan tana duban gyefe da gyefen ta babu alamar hanyar satan kuɗi …taɓ wallh da sake dole na bar wurinan na koma wurin asusun kuɗi na companyn kamin su gane takardun dana taho dasu ba nawa bane , daga Ni sai takardar secondary gomma nayi komai oya oya nabar Company nan.

Rintse ido tayi nan take ta tuno da inyamurin ta mai lapo data amsa masu bashi yanxu bashi ya dameta…Wani irin buɗe idon ta tayi da sauri tana rarrabasu kamin ta ce “Ta ina zan fara? Miƙewa tayi tsaye tana kallon sama inda taga PA Wanda ya ɗauke ta aikin ya nufa…ƙallon glses ɗin wurin tayi ganin ya hasko mata komanta yanda ta sauya kaman ba itace Siman Gaye ba…Murmushi tayi a hankali tana tuno da abun da ya faru da ita da Mmn biyoda kwanaki da suka wuce….

Tafe take tana surfa bala’i haɗi da sauri zaf zaf ,yanda take masifa ka aza da wani a gyefen ta takeyi… cilla ƙafafun ta kawai takeyi tamkar wacce zata tashi sama…na gaji da wannan ƴar iskan garin ,ace bashi ya hanani sukuni , Anbi an dameni, wallahi duk wacce ta kuma zuwa mun da maganar bashin ta sai na tijara koma waye? Wannan abu haka?.. Kai innalillahi yanzu ta ina xan fara ne?”. Tayi maganan tana tsayawa haɗi da kama ƙugu… matashiyar budurwa ce da ashekaru baxata haura ashirin ba take wannan banbamin tare da surutai yin su take ita kaɗai kaman zautattaciya. Daganin ta kasan fitinanniya ce lamba ɗaya… Sakin hannayen ta tayi tana cigaba da tafiya ,yanda take tafiya zaf² yasani ƙare mata kallo ina mmki.

“Wasu yaran inyamurai da yarbawa ne da suka duƙufa wasa suka hango ta can nesa wanda a yanayin sa hijabin ta an jawo shi gaban goshi na tsaban iyayi da ƙauɗi yasa su saurin miƙewa ba tare da kowa yayi mawa ɗan uwan sa magana ba”.

Kamin su rufe baki Sumayya da ta hangosu dama bata raga mawa yaran layin ko kaɗan , bare su da cikin su akwai wanda yayi mata laifi… Hakan yasa su cikin sauri ta ɗaga ƙafanta kamin su ankare har Sumayya ta iso gaban su…babbabara uban can, Ni kuke kira da Siman gaye? Ni sa’ar ubanku ne ko uwar ku?”.

“Jikin yaran ne yahau rawa kar kar kar kaman wanda aka sa masu shocking kamin salihu yace” A’a ke ba sa’an mu bace, Don Allah Sima kiyi haƙuri”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button