Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 5

Sponsored links

Ta tsorita sosai da ganin shi haka, ido ta zaro waje tana kakakin mutuwa,

Wani irin shocking yaji yabi jikinsa kamar Wanda ya rungumi electric gass, jiyayi kamar wuta ne yake ci a jikinsa,

Da ‘kyarr ya iya wurgar da ita gefe, sauran kad’an ya fad’i ‘kasi badon ya ri’ke motarsa da karfi ba, a gigice ya shige cikin motarsa ya figeta da gudun gaske! Shi kad’ai yasan irin rad’ad’in da yake ji a jikinsa, ga hankalinsa ya fara barin jikinsa.

Ayush tashi tayi tangal tangal kamar zata wad’i kasi tayi gurin da mahaifiyar take kwance ta fad’a saman ta, numfashin ta ne ya tsaya cakk, lokaci guda ta sume a gurin.

Motar ce tasau hanya sakamakon ba’a cikin hayyacinsa yake ba, cikin jeji motar ta gangara wata ‘katuwar bishiya motar ta daka, kansa ne yayi wani irin buguwa a take shima ya suma………

Kwance take a saman gadon asibiti tana ta sumbatu “Uma! Uma!! Uma dan Allah karki mutu ki barni, Dan Allah Uma ki dawo gareni” tana cikin wannan yanayin hankalinta ya fara dawowa jikinta, ido ta fara bud’ewa a hankali tana ganin Dishi-dishi har idon ya washe

Wata farar Mata ta gani gefen ta tana zaune ta zuba mata ido sai kyakykyawar murmushi dake kwance a saman fuskarta

Tashi ta fara ‘ka’karin yi, sai ji tayi matar tace “Sannu ko, ya jikin nakin?”

Tana shirin gyara mata zaman.

Juyowa Ayush tayi tana kallon matar daga bisani tace “Ina Mamana?”

Shafa sumar kanta matar tayi sannan tace “Am sorry my dear, ke kad’ai aka kawo asibitin nan, but mutanen da suka kawo ki sunce already sun sallace Mahaifiyarki bayan sun tabbatar da ta rasu, we’re losses your mom”

Fashewa tayi da wani matsanancin kuka tana fad’in “shikenam kin tafi kin barni Uma, Ina Zansa rayuwata, bazan iya rayuwa ba tare dake ba Uma, bani da kowa innalillahi wa inna’ilaihi raju’un” kuka ne yaci raanta sosai.

Rarrashinta Matar take tana bata baki, da haka har Ayush ta samu da dawo hayyacinta, ajiyar zuciya ta shiga ja. Murya a sanyaye Matar take fad’in “Allah yana tare da ke, insha Allahu bazaki tozarta ba”

Ayush murya Ciki-ciki tace “banida kowa sai Uma na, yanzu Ina zansa kaina”

Ajiyar zuciya Matar tayi ta jawo Ayush jikinta tana shafa bayanta alamar rarrashi sannan tace “meye sunanki?”

“Sunana Ayushmat” atakaice ta bada amsa!

“Shin zaki iya zama a tare da ni?” A cewar matar.

‘Dagowa Ayush tayi ta ‘kurawa matar ido daga bisani ta mayar da kanta saman jikin matar, batace komai ba.

Matar ce ta sake yin magana tace ” no karki damu insha Allah Zan ri’keki tamkar mahaifiyarki, ni sunana *DOCTOR* *FATEEMAH* wannan asibitin da kike gani ‘s my own, inaso ki kwantar da hankalinki, zaki cigaba da zama dani a gidana”. Kafin ta rufe baki taji wayarta tana ringing, d’aukar wayar tayi tare da karawa a kunnenta, ji tayi ance *HAJIYA* *KI* *DAWO* *GIDA* *YANZU* *AKWAI* *MATSALA* daga nan aka katse wayar!

“Ikon Allah meke faruwa ne, kinga Ayush ki jirani Ina zuwa yanzu” ta shafa sumar kan Ayush tare da d’aukar hand-bag d’in ta tana tafiya cikin tsari duk da tana had’awa da Sauri-sauri sai takun takalminta da kake ji qwas qwas qwasss, dan’kararren less ne a jikinta tasha d’inkin Riga da zani sai gyalen data yafa, ko Ina sai ‘kamshin turaren jikin ta yake, asalin er washh ce,

Ayush kallon ta take ba ‘karamin burgeta Doctor Fatima tayi ba, har sai data ‘kule mata kafin da dawo da kallon ta kan ledar ruwan da aka d’aura mata.

Da gudun gaske Doctor Fatima ta shige harabar gidanta da dan’kararren motor ta black colour mai taya ta bayan motar.

En Sanda ta gani su uku sunyi cirko-cirko suna jiran isowarta already mai gadi ya barsu sun shigo cikin gidan, cikin tashin hankali ta nufi gurinsa tana fad’in “lafiya kuwa na ganku a cikin wannan yanayin?” Ta ‘karasa maganar tana kallon Ogan nasu.

Ogan ne ya bada umarni cewa “a fito da shi”

Doctor Fatima ce ta maida kallon ta kan Wanda za’a fito dashi daga cikin motor,

Lokaci guda ta furta “innalillahi wa inna’ilaihi raju’un *JUNAID* , maiya faru da shi? ya naga jini a saman kansa? mai kuka mishi? Wayyo Allah na Junaid, Allah yasa dai ba ciwon naka bane ya tashi” tana zubda hawaye tana sumbatu.

Wani daga cikin en sanda ne yace “Hajiya wad’annan tambayoyin nakin bazasu amsu ba anam sai mun shiga daga ciki tukun”

A gigice Doctor tace “to to toh mu je mana jini yanata zuba masa”

Ayush kuwa dake kwance saman gadon asibiti ta ‘kudurta a raanta a cewa duk Wanda yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyarta sai ta d’auki fansa,

Jinin mahaifiyata bazai zuba a banza ba…..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button