Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 105

Sponsored links

Ko kusa ba haka bane, ko wani naga zai cutar da hadimin wannan daula bama shugabana ba sai inda karfina ya kare ai. Ni dai a ranar daren wata laraba wani bawan ALLAH ya sameni akan shi din jami’in ne na hukumar bincike akan sanin nau’in dabbobi masu dafi.Yazo kuma wajena ne da bukatar samun kalolin dafin macizai zaiyi bincike a kansu. Da farko naso naki, dan nasan dan adam na wannan duniyar ba abin yarda bane. Amma sai ya nuna min katin shaidar aikinsa. Hakan yasa na yarda da shi na dauka na bashi

“Sosai ma kuwa. Dan akwai ma cctv footage na abinda duk ya faru a tsakaninmu batare da shi ya san inada camara a wajen ba.” ya kare maganar yana duban shugaban

 

jami’ai. Ya fahimci mi yake nufi, dan haka ya mike ya mikawa Sayeed Hanifud-Din flash da ke a hannunsa, anan take kuwa aka saka flash jikin lap-top aka kai gaban Tajwar Eshaan, sai ko ga duk abinda ya fada din dalla-dalla.

An shigo da wanda ya amso dafin macizan, wanda ya kasance amintaccen hadimi ne ga Miran Jasim, kowa ya sani kuma a masarautar nan, dan tun yana a matashin saurayi ma yake tare da hadimin, shine ke masa duk wasu ayyuka na sirrinsa dama na mugunta. Ai Miran Jasim baima san yay wata iriyar zaburar tashin hankali ba jikinsa na kakkarwa. Yayinda gaba daya kotun ta dauka yan kananan magana har sai da aka tsawatar. Sayeed Hanifud-Din da shima dai gaba daya jikinsa yay sanyi da al’amarin ganin daga inda ya fito, dan koba’a fada ba komai a bayyane yake. Fuskantar hadimin da gaba daya ya fita hayyacinsa a hannun jami’ai yay. ”

“Bama bukatar wani kwana

ja da ga gareka ko ja’ in ja, fadar gaskiyarka na nufin zaka iya samun sassauci, zabar yin taurin kai kuwa ya rage naka. WANENE YA

A take kotun ta dauki wani irin hun karajin Miran Jasim da ya zaburo kan hadimin nasa, sai da jami’ai suka rirrikesa. Yayinda jama’a suka hau salati suma har sai da aka tsawatar. Hadimin ya cigaba da fadin, “Sai dai ni ban san mizaiyi da ita ba, amma a gabana ya zubashi a cikin madara ya bani madarar yace na kai sashen Zawjata-almilk nace daga sashen uwar masu gida. Bani da ikon cemasa a’a, amma navi niyyar kin kaiwa sai dai nasan zai iya sawa a bibiyeni idan nai hakan zai halakani kuma, dan haka na cika umarninsa amma ni duk tunanina ma Zawjata-almilk din zai ba. A ranar nata kokarin ganin samun ganawa da ko amintaccen adalin shugabanmu ne amma hakan bai faruba,da ga karshe ma sai naji wai ashe shine za’a bama madarar ta hanyar Zawjata-almilk ba kamar yanda nai tunanin itace zai bamawa din

ba. Kuma zan fadi gaskiya, ba laifin Zawjata-almilk bane ba asiri yay mata kan duk yanda yaso haka zaiyi da ita, daga baya itama zai kasheta.

Duk yanda akaso samun nutsuwar kotun kam hakan ta gagara. Salati kawai kake ji da la’antar Miran Jasim da akeyi. Iffah ta saki wani irin shegen murmushi tana mai kallon Miran Jasim da yay sumar tsaye. Sai kuma ta maida kan Miran Arshaan da gaba daya yay sharkaf da zufa. Wata dariya ta kyalkyale da shi a zuciyarta tana fain (tun banzo kanka ba) a zahiri kam baka isa fassara yanayinta ba.

A bangaren Miran Arshaan kam ya dauka makircinsa ne yay tasiri kan Miran Jasim. Dan kuwa hasalima shiya tura hadimin ya shiga jikinsa duk tsawon wanna shekarun da suke a tare, dan kawai ya san duk wani motsinsa Abinda bai sani ba a yanzu hadimin ba aikinsa yake ba aikin Iffah yake yi, ita kuma ta zabi tattara laifin ga Miran Jasim a karan kanta saboda haka ta tsara binsu daddaya, shi kuma zata cigaba da jansa a kasa har zuwa gabar da take so..

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button