Hausa Novels and Stories

Tabarma Kashi 6

Sponsored links

“Ki maidashi takeaway” saahar ta fada a taqaice da sassanyar muryarta tana miqewa a nutse,karo kuma na biyu kenan da tayi magana tunda sukazo wajen,ta miqa santala santalan fararen yatsun hannunta tana daukar kyakkyawar handbag dinta tare da zare earpiece din kunnenta ta riqesu a hannu daya,ta tura kujerar baya ta fice a tsakiyarsu tana laluben hanyar fita da kyawawan fararen idanunta da suke da wani irin sheqi da daukar hankali

“Ki making payment kafin ki fita” afifa ta fada a gaggauce tana miqewa hadi da tattara sauran kayansu dake kan table din,tasan tsaf saahar din zata fita ta barta da karbo kayan da kuma biyan kudin.

Kallo daya ta yiwa gun biyan kudin ta sauya akalarta zuwa parking lot na gurin cikin takunta me jan hankali,koda karen hauka ne ya cijeta ba zata yarda ta qarasa da qafafunta wajen ba,ba don komai ba sai don gun cike yake da maza,mai amsan pyment din,wanda zai bata receipt…..kai kowa da kowa ma,wannan ya qarawa zuciyarta qunci da damuwar data tashi da ita yau,damuwar da bata shura wasu satittika bata tsinci kanta a ciki ba,wani abune daya zame mata tamkar JARRABI,duk kuwa da irin qarfin tuwo dana qwanji da take sanyawa kowacce fitowar rana da faduwarta gurin yaqar komai da komai,tare da sake samun nutsuwa da tabbatuwar binnuwar komai,binnewa ta har abada,saidai tasan cewa……ba komai KADDARA ke shafewa ba…..ba komai tsahon zamunna ke samun nasarar lullubewa ba…ba kuma komai zuciya da ruhi ke sarayarwa shekaru ba.

Amsa kuwwar sallamar dake ratsowa daga bayanta zuwa cikin kunnuwanta tayi dai dai da sanda take zura key zata bude kyakkyawar qaramar farar motar,cak ta dakata da abinda take shirin yin yanayin fuskarta yana sauyawa kadan kadan kamar wahainiya,kwanyarta ta sarqe da tunani da kokwanton ba ita ake aikewa da saqon sallamar ba,wannan ya bata karsashin sake zura key din tana murzashi.

Kamar yasan abinda kai kawo a zuciyar tata ya rage mata wahala ta hanyar sake kusanto inda take tsayen yana maimaita sallamar da muryarsa mai sanyi,ta dan runtse idanunta kadan cikin salon da yafi kama da lumshesu sannan ta budesu kai tsaye tana zubesu saman fuskar matashin dake tsaye a gabanta,cikin jikinta tana jin kamar ya yarfa mata garwashin wuta.

Wani irin kwarjini ya dakeshi,karon farko da ya fara jin irin haka kaf tsayin rayuwarshi akan wata diya mace,cikin salo da gogewa ya dunqule hannunsa yakai bakinsa yana jan gyaran murya tamkar mutumin daya qware,idanunsa cikin nata yana son ya koyawa kansa juriya a kallonta. Ba tun yanzu ba,tun sanda suka wanzu a cikin wajen cin abinci ya fahimci akwai wani kwarjini na musamman a tattare da ita,wanda yayi imanin shine ya zame mata qaqqarfar garkuwa daga zamantowa abar tayawa ko tunkarar kowanne irin namiji,yayi imanin a irin kyan da Allah yayi mata,ba kowanne namiji bane zai iya mata kallo daya ya kauda kansa,koda ya kauda kansa yana da yaqinin ba kowa keda qarfin mallakar zuciyarsa ya hanata qyasata ba

“Am sorry,kiyi haquri na tsaidaki ba tare da nasan naki uzurin ba…..but……da farko dai sunana mahmud,ko zan iya sanin naki sunan tare da yimin alfarmar aron lokaci koda mintuna biyu ne rak cikin tsadaddun lokutanki?” Kyansa,ajinsa da qwalisarsa masu dukan zuciya da idanun kowacce diya mace da suka bayyana muraran basu nata narkakkun idanun da matacciyar zuciyar ke kallo ba,abinda take gani yasha banban da abinda kowacce mace zata hanga daga gurin mahmud din……tafi hangen wata muguwar dabba dake neman abun farauta……muguwar halittar ɗa namiji dake laluben halitta mafi rauni irin ta diya mace ya cutar da ita…….dukansu haka suke!,dukansu halinsu daya!,gaba dayansu basu da tabbas!,babu imani ko tausayi a qirjinsu!. Kalmomin da suka tasowa daga qasan zuciyarta suna mata amsa kuwwa a kowanne kunne nata,suka kuma taso da wani lullubabben yanayi me tarin daci dake danqare qasan narkakkiyar zuciyar dake dauke da tarin ciwo,suka soma sauya kalar launin fatarta zuwa bacin rai qarara,saita juya tana jan siririn tsaki,ta dora hannu zata buda murfin motar ta shige don yiwa kanta katanga da kuma kariya daga shaqar inuwa guda ita dashi.

“Kar muyi haka dake beauty…….kaina bisa wuyana indai cikin kalamaina akwai wadanda suka bata miki rai” sakar masa murfin tayi,taja da baya a nutse ta zagaya daya side din motar,zuciyarta tafasa takeyi kamar ta ballo ta fito daga qirjinta,ta bude kujerar zaman banza ta fada,ta maida murfin ta rufe ta kuma saka lock ta kulle kowanne murfi. Relaxing bayanta tayi da makarin kujerar hadi da lumshe idanunta,don ko inuwar mahmud batason gani a wajen bare mahmud din kanshi,ta fitar da siririyar iska me zafi daga bakinta hannunta na dafe da kanta.

Ba zata ce ga yadda mahmud yayi yabar gurin ko kuma adadin mintunan daya dauka a wajen ba,itadai taji afifa na knocking glass din,tunda ta buda ido sau daya taga itace,saita maida idanun ta rufe,tasa hannu ta laluba key din ta cire mata lock din hadi da dora key din daga gaban motar.

Sau daya afifa ta kalleta ta dauki key din ta saka ta tayar da motar ba tare da tace mata komai ba,bata da buqatar ji ko tambayar komai daga bakin saahar,tunda ta tarad da mahmud a gurin,to amma shin rayuwar saahar zataci gaba da tafiya a haka?,da kanta ta bawa kanta amsa ta hanyar girgiza kanta,dole dole……koda zasu dinga fada sau dari a rana suna shiryawa……ya zama dole ta dinga gayawa saahar din gaskiya,koda yau bata gani ba…..koda a gobe bata gane ba zuwa jibi lallai hankalinta zaikai kai,lokaci kuma zaiyi mata aikinsa,da wannan tunanin bayan sun danyi nisa saman hanya,motar shuru kamar kurame ne matafiyan,afifa tayi gyaran murya qasa qasa,cikin nutsar da muryarta tadan kalleta ta gefan ido kafin tace……

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button