Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 26

Sponsored links

★Karan farko na tarihi, karan farko na rayuwa, yau ga Iffah gaban *_Malikat Busheerat_*. Mace ta biyu ga tsohon Tajwar Haysam ibn Abdull-Majeed. Mahaifiya ga Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdill-Majeed Shahan-shan na wannan ƙarni. Hamshaƙiyar mace mai tsananin ƙyau tamkar itace ta zaɓama kanta ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da zubin halittar ta. A kallo ɗaya da Iffah tai mata daga cikin hular alƙyabar jikinta ta kasa sake ɗaga idanu ta ƙara saboda kwarjininta. Ta tabbatar ta isa a kirata _Malikat_ (Sarauniya), Uwa ga fir’aunan sarki kuma. Kishingiɗe take a ɗaya daga ƙayatattun kujerun katafaren falon daya amsa sunansa daular duniya, wanda kafin isowarsu cikinsa sun wuce manyan faluka da suma suka amsa suna daular duniya bama ta ruman ba kawai. A gefe da gefenta wasu matanne cikin shiga ta alfarma suma har su huɗu, sai hadimai dake zagaye da ita kowanne da hidimar da yake a gareta cikin matsanancin taka tsan-tsan da kai. Dan ko wadda ke tare da ita suna shigowa zubewa ƙasa sukai jikinsu har tsuma yake yi, ita Iffah har tsoroma suka bata tare da mamaki mai girma na wannan ƙarfin iko.

Iffah dai na tsaye har sai da ɗaya daga cikin matan nan dake tare da Malikat ta miƙe ta kamota ta zaunar ƙasa bisa lallausan carpet ɗin dake a falon saitin Malikat Bushirat da har yanzu tana a kishingiɗenta kuma ko sau ɗaya bata ɗago ta kalla kowaba tunda suka shigo. Kusan minti biyu falon yay tsitt babu wanda ya sake koda motsin kirki, sai ƙarar na’urar sanyi dake tashi kaɗan-kaɗan da wani ƙamshi na musamman.

Iffah da shirun ya isheta kaɗan ta ɗago idanunta ta cikin hula ta saci kallonsu. Sai taga su duka har Malikat ɗin ashe ita suka zubama idanu. Haka kawai tasha jinin jikinta, dan kallone bana a santa ba, kallone dake buƙatar nutsuwa kafin a bashi fassara. Kaɗan taja numfashin dake neman maƙale mata a maƙoshi da ƙara yin ƙasa da kanta hular ta sake rufe fuskarta ruff. A hankali, cikin son ɓoye rauninta da hawayen dake neman kwace mata ta furta “Barka da yamma ranki ya daɗe”.

 

“Malikat ta amsa miki, tare da maraba a gareki”.

 

Ɗaya daga cikin matan ta amsa a maimakon Malikat da har yanzu batako motsa daga kishingiɗar da tayi ba. Sai dai ta ɗago ƙyawawan idanunta farare tas ta sake zubasu akan Iffah, idanun ta juya a hankali ta dubi ɗaya daga cikin matan nan dai dake kusa da ita.

 

“An gama ranki ya daɗe”.

 

Matar ta faɗa da girmamawa alamar ta fahimci mi take nufi. Tsam ta miƙe zuwa inda Iffah take, ta kai hannayenta biyu ta kama hular alƙyabbar tai baya da ita, ƙyaƙyƙyawar fuskar Iffah datai jajur saboda kukan da tasha abinka da farar fata ta bayyana. Idanu Iffah ta rumtse sakamakon jin al’amarin a bazata, ga wani irin harbawa da ƙirjinta yayi har sai da ta ambaci (Hasbinallahu wa-ni’imal wakil) a zuciyarta sannan taji numfashinta da yay sama yay ƙasa a lokaci guda ya daidaita. Kaf hadiman ƙasa sukai da kansu, dan haramunne a garesu kallon fuskar *_Zawjata-almilki_* kai tsaye. Yayinda Malikat Bushirat ta motsa a karo na farko daga kishingiɗar da tai idanunta akan Iffah. Kusan kallon mintuna biyu tai mata kafin ta janye idanun cike da ƙasaitar masu isa, yatsun hanunta ta ɗan murza suka bada sautin (ɗass! Ɗass!!!) har sau biyu. Tamkar ƙiftawar ido hadimar dake tsaye riƙe da wani ƙasaitaccen bowl kalar gold da adon stones masu ɗaukar ido ta iso gaban Iffah da kanta ke ƙasa har yanzu tana ambaton ALLAH a zuciyarta ta zube tamkar mai neman gafara. Kanta a ƙasa alamar bazata iya kallon Iffah ba ta miƙa mata bowl ɗin hannu biyu bayan wata a cikin sauran hadiman ta matso da sauri ita kuma ta janye farin ƙyalle da aka yana a saman bowl ɗin tare da murfinsa, tatacciyar madara fara tas ta bayyana. Cikin rawar murya da tsantseni hadimar ta furta,

“Ya Zawjata-almilki! Wannan madara ce mai daraja daga hannun Malikat domin nuna maraba da zuwa a gareki cikin DAULAR RUMAN”.

 

 

Shiru Iffah bata da alamar motsawa, har hakan ya bama duk wanda ke gurin mamaki har Malikat Bushirat. Tsahon sakanni goma kafin ta ɗago. Manyan idanunta da sukaci kuka har suka gode ALLAH ta zubama bowl ɗin tare da hadimar dake gurfane a gabanta tamkar mai neman gafara. Kanta ta girgiza a hankali tare da sake maidashi ta risinar. Cikin motsa laɓɓanta a hankali tace, “Wannan karamci abin alfaharine a gareni da nuna tsantsar godiya ga Uwa gareni dama ƙasar Ruman baki ɗaya. Sai dai ina mai neman afuwar jinkirtamin shan wannan madara sakamakon azumtar wannan yini da nakeyi batare da nasan yau zata kasance rana mafi daraja da alfarma a gareni ba”.

 

Kalaman Iffah da tasirinsu tamkar saƙar ƙudan zumace cikin kuttu a zukatan duk wani mai numfashi dake a wannan falo. A zahiri da baɗini kuma babu wanda mamaki bai bayyana akan fuskarsa ba, saboda abune da bai taɓa faruwaba a cikin daular ruman. Malikat Bushirat tai ƙyauta a jinkirta amsa tare da biyo jinkirin da sharhin da babu gargada akan harshen mai furtashi. Wannan abu yakai a kalla Iffah a sake kallonta dan ko ƴaƴan gidajen sarauta goma cif da aka kawo daular a irin matsayinta basu samu ƙwarin gwiwar ƙin shan irin wannan madara ba. Hasalima kowaccensu da rawar jiki take amsa ta shanye tas ta bada bowl ɗin tana mai gurfana a gaban Malikat domin yin godiya. Ba’a matsayi kuma kawai ba hatta a shekaru Iffah itace mafi ƙanƙanta a cikin Zawjata-almilki goma sha huɗu da aka kawo gidan.

Ɗaya daga cikin matance ta zabura idanunta dake nuna ɓacin rai akan Iffah. Sai dai abin mamaki Malikat Bushirat da idanunta ke kan Iffah ko ƙyaftawa babu ta ɗaga mata hannu alamar ta zauna tare da sakin wani ƙasaitaccen murmushi. Nuni tai akan a rufe madarar. Ruf aka maidata yanda take hadimar ta miƙe daga gaban Iffah da tunda ta sake maida kanta ta rissinar bata ƙara ko motsawa ba.

 

A karo na farko Malikat ta motsa laɓɓanta, cike da izza da ƙasaita irin ta manyan masu mulki. “A kaita masaukinta”. Ƙasaitacciyar muryarta ta ratsa zuciyar Iffah tare da girgiza gaɓɓanta cikin ikon harbawar jini. Sunan ALLAH ta ƙara tsarkakewa a zuciyarta dan tabbas Malikat ta cika Malikat ɗin babu tantama. Saboda muryar tata kanta barazanace ga duk mai yunƙurin kawoma girmanta wargi da saka tsantseni a zuciyar duk wani talaka dake a ƙarƙashin mulkinta.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button