Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 9

Sponsored links

Ita daman tazo taga lafiyarsa ne da kuma ta bashi hakuri akan yabar Ayush ta zauna da su .

Tayi tunanin ta 6oye Ayush a cikin gidan yanda bazai ganta ba, sai dai duk lokacin da ya gano hakan bazai barta ba saiya hukunta ta, domin ba abunda ya tsana illa a munafurce shi da kuma ‘karya…

Zaman jiranshi tayi har yayi sallar sa ya had’a da lafuloli.

Daga bisani kuma yazo kusa da mominsa ya zaune yana fuskantar ta

“Is there any problem”. Ya furta hakan yana kallon ta.

Murmushi tayi sannan tace “Junaid kana son ganin farin ciki na?”

“Of course Mom” ya bata amsa a takaice!

 

“Idan kuwa hakane!

Inaso ka saurari abunda zance maka, Nan ta kwashe labarin Ayush ta gaya masa, ita marainiya ce daga asibiti bata San Ina zata nufa ba”

Ta dakatar anan tana kallonsa, so take taji abunda zaice,

Sai dai kuma bataga alamar tausayawa daga fuskar Junaid ba , hakan yasa Tasha jinin jikinta, tasan bazai bar yarinyar ta zauna a nan ba.

‘Dan turo ‘karamin bakin shi Junaid yayi ya kalli mom d’insa ta wutsiryar ido yana yamutsa fuska yace

“Ni fa mom duk wannan tatsuniyar takin ban fahimce shi ba, naji labarin Kwata-kwata bai shafeni ba”

 

“Junaid please be patient and help her” murya a sanyaye mom take magana.

 

Juyowa yayi ya kalleta “how comes Zan iya temakan wanda ban Sani ba,

Mom don’t trust any body, yanzu mutane ba abun yadda bane, wani zai iya shugo rayuwarka domin ya cutar da kai, tin Ina yaro na fara ganin yanda rayuwar take, karki ga laifi na don Ina Koran house worker da kike kawowa because House worker ce tayi sanadiyar *MUTUWAR*

*MAHAIFINA* mutumin kirki bai aikata komai ba! Wallahi Mom bazan bar kowa ya kusance mu ba, kuma har yanzu Ina kan bakata na d’aukar fansan mutuwar Mahaifina, idan ban d’au fansa akanta ba sai dai bata Raye to kuwa Zan d’au fansa akan *IYALANTA* har yanzu Ina kan bincike na kuma insha Allahu Zan samesu, hukunci na kuma kisa ne ko wa nasamu acikin familyn ta!

Hakan yasa na shiga Aikin *soja* ban damu da ciwon dake jikina ba, nasan Allah ne ya d’ora mun ciwon kuma Ina neman warakarsa”…….

Doctor Fatima ba abunda take sai kuka domin an fame Mata ciwon dake zuciyarta,

Shima kawar da fuskarsa yayi gefe yana ‘ko’karin share hawayen da ya zubo masa…………

Fitowarta kenam daga toilet, tana d’aure da towel a kirjinta, gashin kanta a baje agadon bayanta ta wanke shi fess har wani shining yake ga ba’ki ga tsayi har ya kusan isowa ‘kugunta, dake gashin Fulani ne da ita!

Ayush farar mace ce ta asali, ga manya manyan idanuwa gashin ido kuwa zara-zara ba’a magana, azo kan gashin gira acike tam da gashi har girar ya kusan had’ewa 2, ga shaden ta luf-luf kwance da gashi, gashin gaban goshinta kuwa ya sau’ko sun had’e da girar ta.

Allah yayiwa Ayush baiwar suman gashi ga kyau ba’a magana, ga tsayin hanci kamar Wanda kullum ake dad’a tsayinsa, lips d’inta kuwa kamar bakin tsuntsu tsabar ‘karanta tana da ‘karamin baki, colour bakinta yaci maroon sosai kamar wacce ta shafa jan-baki, kuma haka bakinta yake tin tana jaririya,

Ayush ko kad’an bata makeup saboda kwalliyar fuskarta Wanda Allah ya tsara mata mah ya isheta,

Ko tayi makeup ko kartayi kullum Ayush a cikin kyau take, doguwar mace ce, siririya marar kauri, sai dai akwai kayan alatu kam

Ta waran ‘kirjinta ba’a magana a cike fam kamar meyin ciko sai dai bata saka rigar breziya, saboda gurin da ta zauna da mahaifiyarta basa samun kud’i balle suyi siyayyan kayan da zasu saka, sai riga kala d’aya da take using dashi kullum….

.Anzo gurin kuma wato waran Baanbom d’inta ga hips kuwa kamar ita tayiwa kanta, ta ko Ina a cike yake a jinkinta duk da batada jiki amma tana da kyakykyawar surar jiki….

Tsayawa tayi a gaban mirror ta kammala shafa cream mai shegen ‘kamshi ta feffesa turare a jikinta ta gama gyara gashin kanta ta d’aure da rivon, shikenam makeup d’inta kenam ko powder bata shafa ba amma fuskar yanda kasan an tsara kyakykyawan makeup ne.

Ta nufi yanda Doctor Fatima ta ajiye mata kayan da zata saka, wata dan’kararriyar doguwar riga ne na kanti mai bell a jiki black color.

Zura rigar tayi sannan ta d’aure kunkumin ta da bell d’in, kunkumi kamar na sauro sai tilin ‘kugu, ga breast d’in ya fito sosai Masha Allah kayan ba ‘karamin kyau sukayi mata ba.

Ba tare da ta rufe kanta ba ta bar room d’in tana taka matakala a hankali ta sau’ko falo,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button