Hausa Novels and Stories

Idon Naira 43

Sponsored links

Zainab ya kalla bayan yashigo palonsa ya zauna a daya daga cikin kujerun palon Yana kallon zainab data kasa zama tana tsaye tana jiransa itama.

Cikin sakewarsa irin ta Wanda baida damuwa yace”

Kece zakiyi magana ko nine zanyi???

Batareda tayi Masa kallon duka idoba ahankali tayi Masa bayanin gidan mahaifinta tazo nema.

Da mamaki ya tambayeta gidan datake nufi Dan duka gidajen yasansu tunda shima anan ya tashi.

Bayanin gidansu da mahaifinta tayi Masa take yaganeta Dan shekarunsu daya.

Cikin danne dacin Ransa na shekaru dasuka wuce ya sanar da ita Shi Dan Iya Fatu ne wadda ta reneta bayan rasuwar mahaifiyarta.

Da mamaki ya tambayi yanda ta haifi Yar dake bayanta Amma takasa sanar dashi komai sbd tasake shiga tsoro da firgicin rayuwa Kuma bayan Jin abinda ya samu iya Fatu dashi lulun.

Zaman Dole yasata sbd kukan da MARYAMAH ta fara

Ta sauketa

Yasa aka kawo Mata abinci Mai kyau daga shagon kicin din restaurant dinsa tabawa MARYAMAH Dan ita bazata iya cin komaiba

Duniyarta da komai nata ya tsaya.

Sallar asuba da tashin hankali yasa bataiba tayi a Rana tsaka kafin taci Dan sauran abincin da MARYAMAH din ta rage bayan ta yagalgala.

Da fari hanata tafiya yai sbd zai bincika Mata tagurin wa mande ds ya siye gidan nasu.

Batada zabi batada mafita tunda ko ta fita batada gurin zuwa Dan haka ta zauna a gurin Lulu din Wanda kaf gidan dakinsane kawai yakeda Palo da dakuna biyu aciki kowane da toilet sbd shine Mai gidan Kuma shugaban gidan.

Yamma nayi zuciyarta takasa nutsuwa saidai Kuma ahakan tanajin sassaucin zama anan idan har tana tareda ‘yarta akan zama a Abuja ‘yarta na Cameroon batasan irin rayuwarda zatayiba acan tunda tanada tabbacin babu Wanda zai tsaya akanta ya Bata tarbiya,

Idan har Lulu zai karba Mata haqqinta na gidan babanta zataso hakan sbd Nan kawai takeda sauran hope na inda zata zauna tayi rayuwa da MARYAMAH dint hakama idan Aqeel yadawo zaiyi saukin samunsu a gidan baban nata.

Dakinsa ‘daya ya bata itada ‘yarta abinda bayayi baikuma taba ba

Wato barin wani ko bawa wani dakinsa ‘dayaba sai akan zainab itama Dan ganinta ayau tareda gane wacece yakejin kamar ‘yar uwarsa ce tadawo garesa tunda dukkaninsu har zainab din uwa daya ce ta renesu abinda baida tabbaci shine idan nono daya sukasha, wato idan iyarsa ta shayarda zainab din.

Itama zainab dayake Bata manta iyah dinba sbd kafin atafi da ita gidan Maryamah tun wancan lokacin iyah dince kawai take kaunarta take siya Mata wasu Yan abubuwan wasu lokacin har Saida aka tafi da ita gidan zainab sukai rabuwa Ashe tahar abada ce.

Dakin baida girma sosai Amma nata na gidan Haj Maryamah baifi wannan din girma ba,

Qatuwar katifa da wardrobe ne Acikin dakin sai madubi da toilet.

Wanka tayiwa maryamah itama tayi tayi sallar ishai Dama ansake kawo musu abinci daga shagonsa sunci sun koshi.

Babu Bata lokaci bacci ya daukesu daga ita har MARYAMAH tunda a matuqar wahala suke.

Washe gari zaunar da ita Lulu yayi yai Mata bayanin gidansu dai agurin Mai anguwa Mande ds ya siya Kuma yasama tabbacin Shi Mai anguwa gidan a hannunsa su Maryamah suka barsa.

Gidan na babanki ne halak malak ba haya ba

Dan haka dai yanzu haqqinki Dole zaa Baki idan DS yaci idan Mai anguwa babu Wanda zaici ya zauna lafiya.

Girgiza Kai tayi ahankali tana Dan rintse idanuwanta dasuka Dan sauya cikin mutuwar jiki tace abar maganar gidan ta hakura Dan ita din ba kowa bace,

Gadon nata ba batajin tanadashi tunda dai su umma basuma San tazo neman gidan ubanta dinba.

Fada Lulu ya rufeta dashi Yana takura da fadan sosai har Saida ta zayyane Masa komai na rayuwarta da dalilinta na baro gidan Yar uwar tata..

Sake Baki yayi jikinsa da bakinsa na mutuwa Dan bai dauka haryanxu akwai wainda zuciyarsu Bata aikiba

Dan kuwa zainab alamu sun nuna tata zuciyar a kwance take cikin ruwa ba jini ba..

Barinta yayi Yakuma ficewa Dan baisan mezai ceba Wanda zata gane Amma dai koma menene sai anbata gadonta wlh.

Daga ita zai MARYAMAH yabari wuni guda a dakin sai siddi daketa dawainiyar kawo musu abinci da abubuwan buqata.

Tunda tashigo ko kofar fita daga palonsa batayiba sbd gida koina karuwai ne da maza

Musamman yanzu da sukasan Lulu bayanan kowane namijin shogowa yakeyi ya shige dakin budurwarsa

Dan babbar qa’idar Lulu bayason maza na zuwa gidan gurin karuwansu,

Saidai kowace idan dare yayi kokum idan tana buqata tace gidan saurayin nata ko alhajin nata koma hotel ne

Siddi sosai ta nuna musu kauna itada MARYAMAH dinta sbd siddin itace Yar hannun damar Lulu

Itama zaman kanta takeyi Amma tanada kamun Kai ba kamar yanda sauran karuwan keyiba.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button