Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 18

Sponsored links

Jin knocking yasa ta tayin saurin miƙewa daga zaunan da take saman gadonta , ƙarasawa tayi jikin ƙopan tare da cewa “Wanene”?

Aunty azmee ce” ta bata amsa daga waje,

 

Ajiyar zuciya sehrish tasaki tare da buɗe mata ƙopan, shigowa azmee tayi jikinta na sanye da Doguwar riga sai babban mayafin da ta yafa,

 

“Ƙanwata me kke yi yanzu ne? halan kina nan zaune cikin damuwa ko? ko irin kiyi tunanin kin gaji da zaman kaɗaici ki kawomin Ziyara a bedroom ɗina bakya yi ko?

 

 

 

tayi maganar tana kallonta, cikin jin kunya sehrish tace “Aunty azmee bana so na taƙura maki ne, shiyasa bana zuwa ɗakin ki,”

 

Murmushi Azmee tasaki tare da cewa ” babu wani batun takura anan, kawai bakya son zuwane, nima kaina gajiye nake da zama wani sa’in duk atukure mutun kamar maye shikaɗ

Murmushi sehrish tayi tare da cewa “ban shaida ba, amma naga hoton wata mata Mai kyau baturiya mai sanye da kakin Soja a bedroom ɗin Babban yaya saman bedside drawer aka ajiye hoton,

 

Azmeee tace “dawa tayi miki kama acikin su”?

 

Sehrish tace “Babban yaya sunyi kama ssae hada blue eyes ɗinsu ma, sai kuma su twins da fawan, amma dae aunty Azmee dukansu ba uwarsu ɗaya ba ko? Ta ƙarasa maganar tata da tambaya,

 

Azmee tace “eh su Twins da fawan da Babban yayansu da junaid uwarsu ɗaya, suma su Kanal Yusif mahaifiyarsu daban’

 

Jinjina kai Sehrish tayi tare da cewa “Su mommynsu ƴar wata ƙasa ce aunty azmeee?.

Sunnar da kai sehrish tayi tana kallon yatsun hannunta cikin jin kunya

 

Azmee taci gaba da cewa “Sunan ta *Fatima ita ƴar America ce amma tana zaune a Australlia,”

 

ɗan shiru tayi na wani lokaci kafin ta sake cewa “Aunty azmee Yaushe zata zo nigeria ne? ita bazata zauna nan ba ko Abba ya sake ta ne?

 

Dariya azmee tayi tare da cewa “Wasa wasa sehrish kema fa kin iya surutu na lura wurine baki samu ba shiyasa kike noƙewa kamar bakyason magana,” tayi magana tana ɗan kallonta,

 

“In har aka tashi aurenki da babban yayansu ae dole tazo asha biki da ita,”

Jin wannan maganar ta aunty azmee yasa Sehrish ɗan zaro ido hada dafe ƙirji aranta tana cewa “tab ! Wannan matar ta cikin hoto anya xata barni in zama surukarta daga gani zatayi zafi Allah,

 

Murmushi kawai azmee takeyi tana kallon Sehrish dake faman sake sake aranta,

 

Ita kanta Azmeen zolaya take mata amma tasan cewa sarai Alexandra bazata ta6a bari Sgr ya auri bakar fata ba,

 

Sun jima suna fira har wurin sallar la’asar sannan azmee tayi mata sallama ta fuce izuwa nata ɗakin,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button