Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 39

Sponsored links

“Hakane Umm Yazeed maganarki nakan gaskiya, kuma tabbas na fara ji a jikina akwai lauje cikin naɗi a wannan lamarin, da alama hanasu amsarmu akeyi”. Abu Zainab ya faɗa ransa a ɓace.

Matar Abu Zainab dake share hawayen itama ta ce, “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un. Wannan wace irin masiface haka? Mi bayin ALLAH nan suka tarema wani da zafi haka?”.

“Sanin gaibu sai ALLAH, inaga inada mafita ɗaya, mu ɗauketa mu maidata gida sai a sanar da ƴan uwansu ko? Tunda mudai munyi iya ƙoƙarin mu…”

“Da hakan kukai tun farko da baku wahal da kanku ba”. Wata murya ta faɗa a bayansu. Da sauri suka juya su duka, sai dai bayan mutumin kawai suka iya gani. Da gudu Abu Zainab ya bisa, amma kafin yaƙarasa garesan harya shige mota sai ƙura ya bulesa da shi…….

Babban ɗaki na musamman aka warema Iffah a sashen Malikat Haseena. Tare da amintattun hadimai biyar da zasu dinga mata hidima. Sai Ghazi biyar suma da zasu dinga bata tsaro duk da dama sashen zagaye yake da masu tsaron, amma an ware biyar ɗinne na musamman domin kula da duk wani motsin shiga da fitar mutane da zai shafi Iffah. Hakan ya sake saka Malikat Bushirat a farin ciki matuƙa. Yayinda sabanin haka ya bayyana a fuskokin munafukai, sai dai wasu sunyi jarumtar dannewa baƙin cikin nacin zukatansu tamkar wutar daji. Malikat Haseena data zartar da hukuncin batama nuna tasan sunai ba. Ita kuwa Daneen Ammarah damar nutsuwar nazartarsu ta samu ɗaya bayan ɗaya dalilin wani ɓoyayyen al’amari dake ajiye a zuciyarta tsahon shekaru.

 

 

 

Daneen Ammarah ta kasance ɗaya daga cikin ƴaƴan Malikat Haseena da Tajwar Abdul-majeed Ibn Aliy. Su huɗu suka haifa. Tajwar Haysam shine babba, (sarkin daya shuɗe kuma mahaifin sarkin yanzun). Sai Daneen Waheeda tana auren wani babban sarki a yankin larabawa. Sai Daneen Ammarah, itama tayi aure sai dai auren bai jimaba sakamakon wani ɓoyayyen al’amari dake tattare da ita, wannan ne sanadin dawowarta gida take zaune kusan shekara goma sha tara kenan bata kuma sake wani auren ba. Ƴar uwarta da mahaifiyarsu Malikat Haseena da marigayi Tajwar Haysam da mahaifinsu daya bar duniya da tabon damuwar ƙaddarar ɗiyar tasa ne kawai sukasan wannan sirrin, al’amarin ya sameta tun tana ƙarama dan bata wuce shekara 14 ba, shiyyasa ta jima batayi aure ba, bayan ta samu tai auren kuma bata jimaba suka rabu da mijin dan auren baifi wata takwas ba ma. Manyan masarauta sunta ƙananan magana akan hakan da fassara al’amarin na Daneen Ammarah ta siga daban-daban amma su Malikat Haseena sukai biris dasu. Sai auta Miran Nayyar nada shekara bakwai ALLAH yay masa rasuwa.

Bazamuce Iffah tayi garau ba kam a wannan yini. Dan har yanzu ko idanunta bata iya ɗagawa ta kalla kowa. Sai dai daidaituwar fitar numfashinta ya saka nutsuwa a zuciyar kowa. Koba komai dai an samu sassauci ai. Daneen Ammarah itace da kanta ta gogema Iffah jiki ta canja mata kaya, itace kuma da kanta tai zaman bata abinci daya kasance mai ruwa-ruwa. Daga haka aka ƙara bata magungunan da duk suka dace da gyara mata kwanciya a lafiyayyen gadon da yaji shimfiɗu na alfarma. Wani irin barcine mai daɗi yay awon gaba da ita, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Daneen Ammarah dake kallonta cike da tausayawa da jin wani ɓoyayyen al’amari akan yarinyar ta sauke numfashi ahankali da mata addu’ar samun lafiya da fatan ya zama kaffara a gareta…….

Duk wani nau’in kiranye ga uwa ta yisa tun lokacin da labarin abinda ya faru da yarinyar can sakamakon saka riga ya risketa, tabbas sune suka bada riga, amma abinda ya faru da yarinyar bashine ya kamata ya faru ba akan rigar, dan shirinsu sam bashi da alaƙa da halin da take a ciki yanzun. Hakan na nufin kenan bayansu akwai wasu masu shiri akan yarinyar kenan?. In dai har hakane kuwa to su ɗin su wanene? Minene tasu manufar kuma?.

 

Wannan amsar take buƙatar ji a wajen Uwa, sai dai har zuwa duhun dare babu alamar zata ziyarce ta. Tun zuciyarta na raya mata ta jira har ta fara jin ita taje gareta mana kawai. Amma tuna zuwa ga Uwa babban al’amari ne mai wahalar yiwuwa gareta yasa ta kasa iya cigaba da tabuka komai har dare ya cigaba da tsalawa masarautar ta ɗauki shiru tamkar babu wani mahaluki mai sauran numfashi. Ta cigaba da kaikawo a cikin wannan shiru, tare da ƙara gwada dabaru kala-kala na kiranye ga Uwa. Dai-dai lokacin da take sarewa, gaɓɓanta ke nuna gajiyawa mummunan sautin dariyar Uwa mara daɗin saurare a kunnuwa ta fara mata kaikawo tamkar tana yawo cikin iska. Ƙasa ta zube akan gwuyawunta tana mai jan nannauyan numfashi dajin sanyi a ranta. Tarwai Uwa ta bayyana a gabanta, akan kujerar baƙin karfenta mai adon gwal sanye cikin jajayen kaya kamar koyaushe. Mummunar fuskarta a matuƙar tsuke take babu alamar itace ta gama dariyar dataita amsa kuwa a mintocin da suka shuɗe…..

 

“Barka da isowa Uwa mai share kukan masu kuka. Uwa ina cikin matuƙar ruɗani, dan aikinmu yasha banban da wanda ya bayyana ga ƴar shilar suda. Kamar yanda na riski yinin jiya a cikin ruɗani, haka na kasance a duhun dare batare da na rintsa ba, na kuma sake wayar gari da ƙishirwar ganinki a yinin yau har zuwa iyanzu da daren ke ƙoƙarin zama dare biyu da faruwar komai?. Shin kuskuren daga garemu ne? Kokuwa kece kika canja aikin ya koma hakan? Ko akwai wasu masu irin shirinmu ne a wannan daula batare da mun san dasu ba? Minene manufarsu su? Wane buri kuma suke da shirin cimmawa?. Uwa ki taimakeni nasan wannan amsoshi in ba hakaba zuciyata na gab da tarwatsewa ne”.

 

“Bazan gaji da tuna miki akwai ƙalubale zagaye da cikar matakin aykinki na biyu ba, kuma wannan ƴar shila na tare da kaddarar ƙalubalenne, sai dai na miki alkawarin tsayuwar daka akan hana faruwar nasarar da zatazo in har bataki bace ba. Tabbas aikin ba namu bane, kuma rigar da aka kai mata ta sanya ba tamu bace itama. Na gano hakane a daren jiya bayan mutuwar waɗan can hadiman da kuma samun lafiyar ƴar shilar.. Hakane ya sani duƙufa bincike tuƙuru domin gano daga ina matsalar take?, wanene ya shirya aikin laɓewa bayan namu? Har yaci nasarar kuɓutar da ita da tarkon makircin sa cikin sauƙi haka?……”

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button