Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 64

Sponsored links

Mikewa sukayi dukansu suka fita daga dakin, suna fita sukaji wani irin kamshin turare ya dakesu, kwafa deen yayi yace;

 

“Kunji kamshi ko? Toh duk uban kamshin nan itace ta fesa turaren”….

 

Basu tankashi ba haka suka karasa dakinta, sai da sukayi knocking sau uku sannan ta taso ta bude, a shirye suka ganta cikin kayan bacci, kwata kwata batayi kama da wacce ke shirin fita ba, hasali ma harta kashe fitila, ba karamin gogewa deen hadda tayi ba saboda yanda tayi maza ta wanke fuska ta chanja kaya, zeyi magana mami ta dakatar dashi tana kallon baby tee tace;

“Wai kin fita daughter?”…

Kallonshi tayi tana wani munafukin murmushi, dama tasan za’a rina tinda taji ya ambaci sunansu tasan sai yaje ya musu magana, shiyasa tana shiga tayiwa khaleel text message din bazata samu fitowa ba sannan ta kashe waya, da sauri ta cire kayan jikinta ta jefa a washing machine ta hau wanke fuskarta, Allah ya taimaketa bawani abun azo a gani ta shafa a fuska ba….. Murya kasa kasa kamar na wacce ta fara baccin dagaske tace;

 

“Tun dazu na fesa, turaren ne me karfi”…..

 

Ze kara magana mami ta nuna mishi kofa tace;

 

“Sai da safe Deeni! Yarinya na baccinta kawai kasa mun zo mun tashe ta”…..

 

Kallon rashin yarda umm tabi baby tee dashi saboda tasan haka kawai bazata masa magana a nitse ba amma kuma yanda takeyi din babu wanda zece ba daga bacci ta taso ba, kawai ta kada kai tace;

 

“Allah ya kyauta!”….

 

Sannan ta bar gurin….

 

Duk yanda deen yaso yiwa mami magiya akan a binciki baby tee shi yasan za’a samu sheda ki tayi, takaici ya isheshi wayarsa ta fashe bare ya nunawa mami hoton daya mata, yanaji yana ganin mami tace baby tee ta koma ta kwanta sannan shi kuma ta tasashi a gaba da fada har saida ya bar part din sannan ta rufe kofa ta koma gurin umm suka cigaba da zancensu…..

 

Wani tinani ne yazowa deen akan yaje ya duba ko khaleel na nan ya sauke haushinsa akansa, saidai yana fita yaga babu khaleel babu alamarsa, haka ya koma yaje ya kwanta ransa wasai tinda dai bata fita khaleel ya ganta a haka ba, shi da yasan su umm ma basu sani ba da be tona mata asiri ba tinda bata fitan ba, yanzu gashi makircinta yasa suna ganin kamar karya ya mata……

 

Bayan ya idar da sallahr asuba direct part din su mami deen ya tafi, a bude ya samu kofar kamar yanda yayi expecting dan da asuba suke budewa, dakin mami ya fara zuwa ya tarar da ita tana lazimi, gaisheta yayi ta gyada masa kai sannan ya tashi ya tafi dakin umm, akan sallaya ya tarar da itama ya tsuguna har kasa ya gaisheta, amsa masa tayi da tambayarsa ya ya tashi, lafiya kalau yace sannan ya tambayeta ko baby tee tayi sallah, ce masa tayi yanzu ta bar dakin ma, ok kawai yace ya fita daga dakin….. Bin shi da kallo tayi tana sake sake aranta….

 

Tana zaune akan sallaya, qur’ani dauke a hannunta tana karatu a zuciya taji knocking, izini ta bayar Deen ya shigo bakinsa dauke da sallama, tana ganin shine ta mike da sauri zata shige toilet, ruko hannunta yayi a tausashe yace;

 

“I’m not gonna hurt you baby girl!”….

 

Sai a sannan taji hankalinta ya kwanta, sakin hannunta yayi ya dauki Al-qur’anin ya mika mata yace;

 

“Dama nazo muyi karatu ne, let’s go downstairs”….

 

Ba musu ta karba sannan tayi gaba, bin bayanta yayi yana irga takunta dinta yana kuma kare mata kallo ta cikin hijab dinta….

Guri ya nuna mata ta zauna sannan shima ya zauna yana facing dinta, nitsuwa tayi sosai harda sunkuyar da kai kamar a islamiyya aransa yace ‘sai kace ta Allah’…..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button