Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 11

Sponsored links

Yanda Mom ta d’auko haka Ayush ma ta d’auka

Tana hawan upstairs a hankali tabi yanda akayi mata kwatance sai gata a d’akin Junaid,

‘Daki wayam ba kowa, sai’karewa d’akin kallo take yayi matukar burgeta

Ta sau’ke kayan abincin a saman dinning d’insa,

Taje gaban mirror tana duban kanta, kwatsam sai ta hangoshi ta cikin madubi yanata sharar bacci akan gadonsa, dake akwai labule ta tsakanin gadon hakan yasa bata ganshi da wuri ba.

Juyowa tayi da sauri tana le’kashi ta bud’e labulan a hankali tana so taga fuskar shi amma sai dai hannayensa suna kan fuskarsa ta kasa ganin fuskar………..

Ayush tsayawa tayi a bakin gadon da Junaid yaketa sharar baccinsa ya rufe fuskar da pillow, tana tunanin ta tashe shi ne ko kuma ta kyale shi kawai tayi tafiyarta

Lokaci guda ta yanke shawarar tashin shi yaci abinci kada yayi sanyi, cikin ‘karfin hali ta haye saman gadon tana rarrafawa a hankali cike da fargaba saida tazo saitinsa ta tsaya cak ta kasa tashin shi.

Shi kuwa adai dai lokacin ya fara wani irin mafarki mai tsoratarwa, A cikin baccin yaga wata ba’kar Damusa mai jajayen idanuwa ta tsaya daf dashi tana shirin Kai masa hari! A gigice Junaid ya Kai mata naushi da iya ‘karfinsa

Wayyo a madadin ya naushi Damusan ashe a Ayush ya kaiwa wannan naushin a saman Nononta ta 6angaren dama, wani irin ‘Kara tayi ta wantsilo ‘kasi sai datayi dungure sau uku ta tsinci kanta a bakin ‘kofa, hankali a tashe ta mi’ke tana tangal tangal kamar wacce tasha kayan maye! a haka ta fice daga d’akin…

Shi kuwa cigaba da baccinsa yayi hankali kwance.

Mommy tana shirya musu kayan abinci a dinning

Ta jiyo kukan Ayush da sauri ta waiwaya bayanta domin ganin abunda take ji,Ayush bata tsaya wata-wata ba sai yaraf ta fad’i ‘kasi tana ta faman juye-juye da shanbe-shanbe “wayyo Allah Zan mutu, kirjina ya fashe ciwoo”. Ta Kama Nononta da hannunta domin ba ‘karamin zogi yake yi mata ba

Duk ta rasa Ina zata saka kanta, idanunta duk sun kad’a sunyi ja tsabar azaba ga wani gumin da yake yarfo mata..

“Ayush lafiyanki kuwa? Ke da waye? Meya sameki” haka mommy taita jero mata tambayoyinda bazata iya amsa su ba a yanzu,

Ganin yanda taketa juyi a gurin yasa mommy tsorita da sauri ta kamo Ayush tana fad’in muje mu d’aki kiyi hakuri”

Ayush KO mi’kewa bata iya yinsa kamar Wanda wuta yake ci akan Nonon haka take jin rad’ad’in nan.

Zaunar da ita tayi a bakin gado, tana fad’in “sannu ko, wai meya faru ne Ayush?”

A lokacin Ayush ta d’an dawo hayyacinta duk da zafin da gurin yake yimata da ‘kyar ta bud’i baki tace “buguwa nayi” bakinta na kakkarwa kamar maijin sanyi,

“A’a Ayush ki gaya mun gaskiya, shin da mai kika bugu?

Kamar bazata yi magana ba can tace “na bugu da ‘kofar d’aki ne” murya sanyi sanyi take magana.

Mommy tace “kin tabbata?”

Kai Ayush ta d’aga mata alamar eh.

Mom tace “to muga gurin da kika ji ciwon” ta ‘karasa maganar tana faman cire rigar Ayush!

“A’a Aunty ki Bari kawai ba wani ciwo sosai bane” a cewar Ayush wacce kanta ke kallon ‘kasi alamar kunya.

Mommy kallon ta take cike da mamaki tace “to banda abunki nifa mace ce er uwarki sannan in baki manta ba ni Doctor ce, dubaki zanyi naga wani kalar magani ya dace ki sha” da kyar Ayush ta yadda ta zame rigarta daga sama sannan a hankali ta zame breziyar ta Mommy tana ganin yanda Breast d’inta d’aya ya kumbura suntum ga yayi jawurr abunka da farar mace

“Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, Ayush duk wannan ciwon a buguwar ‘kofa yake? Ki duba kiga?”.

Banda zubda hawaye ba abunda Ayush take, ita kad’ai tasan irin rad’ad’in da take ji!

Da sauri Mommy ta tashi tana fad’in “wannan bana zama bane kina bu’katar treatment”

Ta fice daga d’akin gaba d’aya ta susuce a ranta tana tunanin Junaid ne yayi mata wannan d’anyen aiki daman ya nuna baya son zamanta a gidan.

Ayush kuwa tashi tayi ta nufi toilet tsayawa tayi a gaban mirrow tana fad’in “wannan bawan Allah ba ‘karamin mungu bane, azzulumi daga tashin sa a bacci yaci abinci shine zaiyi mun wannan hukunci, Allah zai saka mun” ta ‘karasa maganar tana zubda zafafan hawaye, ga Nono d’aya kuwa yayi timm kamar Wanda ya Tara ruwa.

Tana cikin sambatun ta tajiyo bud’an ‘kofar d’aki.

Mommy ce ta shugo hannun ta ri’ke da boxes na pharmacy, ta ‘kara ficewa ta dawo da kulolin abinci ta ajiye a saman table, zama tayi a bakin gado tana jiran fitowar Ayush, ba jumawa Ayush ta fito da d’aurin towel a kirjinta tayi using da hot water domin jikin ta ya samu ‘kwari.

“Ayush en mata anyi wanka kenam, Bari na za6a miki ‘karamar riga wanda zakifi jin dad’in zama da ita”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button