Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 11

Sponsored links

Duk da gilashin da ya raba sun tsaf yake iya hangota kwance samɓal, illahirin jikinta da zahirinsa ke a bayyane zagaye da na’urori kala-kala da suka kasance sirrin aikin likitoci. Idanun ya sake lumshewa ya buɗe akan fuskarta dake fayau sai hasken data ƙara mai tsananin ɗaukar idon mai kallo. Tabbas akwai abin faɗa a lips ɗinsa, sai dai ƙasaita da ƙarfin jinin iko mai yawo a jijiyoyin jikinsa ya jagorancesa ga haɗiyesu kawai dan barin kaza cikin gashinta kamar yafi alkairi ga mai kiyo.

Tun isowar labarin abinda ya faru da Iffah a wancan daren take jin ranta fes, sai dai zuciyarta na son sanin wanda ya aikata koma miye dan ta tabbatar masoyinsu ne. Cikin zumuɗi tai yunƙurin kiran number ƴar uwarta domin ta sanar mata amma ta gagara samunta. Hakan bai mata daɗi ba, amma dai bata damu sosai ba dan tasan itama komai zaije gareta. Da wannan farin cikin ta kwana a wannan ranar har zuwa jiya da Iffah bata dawo hayyacinta ba.

 

A yanzu kam cikin harzuƙa da ɓacin rai take neman Malikat Bushirat ɗin dalilin labarin sake zuwan Daneen Ammarah sashen Tajwar Eshaan a yau, amma babu alamar zata sameta, tana a cikin wannan ɓacin ran labarin maida Iffah sashen Tajwar Eshaan ya sake riskarta. Cikin tashin hankali ta wancakalar da wayar tayo waje, batare da jiran driver ba ta nufi sashen Malikat Bushirat ɗin..

Hadima Banou dake tafe a ɗan gaggauce dan cika umarnin aiken da Malikat Haseenat tai mata tabi Jasrah da ke fitowa a mota rai ɓace da kallo. A hankali ta lashe laɓɓanta tana mai haɗiyar yawu. Ta jima tana kawaici akan cikin nan na Jasrah saboda shakkar Iffah, amma a yau kam ga dama ta samu. Sake haɗiye tsinkakken yawunta tayi tana gyara tsaiwa. Gabb sukai karo da Jasrah da alamu suka nuna idonta rufe suke da ɓacin rai, itako Hadima Banou duk da tayi ne ta biyu sai ta zube ƙasa cikin rawar jiki tana neman afuwa da rantsuwar bata lura da tahowarta ba har da ƙoƙarin dafa ƙafafun ta, Sake ɓaci ran Jasrah yayi, cikin rufewar idon ta ɗaga hannu ta sauke mata lafiyayyen marin da ya saka sauran hadiman dake ɗan kai kawo shiga razani. Maruwa dai kam Hadima Banou ta maru, dan har sai da tayi ƴar a dunguren da duk wanda ke a wajen yaji tausayinta. Amma a gareta hakan ma nasara ce dan ta samu abinda take so. Fuuu Jasrah ta tsallaketa ta wuce zuwa cikin sashen Malikat Bushirat rai a ɓacin, sai dai cikin girmamawa hadiman ƴar uwar tata suka sanar mata saƙon data bari na bata buƙatar ganin kowa. Watsa musu mummunan kallo tai taja tsaki da shigewarta…….

Fitowarta kenan da ga toilet da alamun wanka tayo dai-dai da shigowar Jasrah ɗakin. Malikat Bushirat ta zuba mata ƙyawawan idanunta kawai cike da mamakin ganin yanda ta ingizo ƙofar gashi ko sallama batai ba. Jasrah da gaba ɗaya idonta ke lulluɓe da tsantsar ɓacin rai ga dunƙulewa da ɗan cikinta yay waje guda ya ƙulle mata mara ta zube a kan gado yarab. Malikat Bushirat da har lokacin ke binta da kallo ta ƙaraso gareta da sassarfa tana ambaton sunanta. Bata iya ta amsa mata ba har ta ɗagota jikinta.

“Jasrah! Are you ok?”.

Ina Jasrah bata iya ta amsata ba saboda yanda mararta ta ƙulle tamau. Hankalin Malikat Bushirat yay ƙololuwar tashi ganin tana jan numfashi da ƙyar. Dole ta shimfiɗeta tai amfani da telephone wajen kiran clinic. Cikin ƙanƙanin lokaci doctor… ta iso, kamar an saita tana shigowa jini na ɓallema Jasrah..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button