Hausa Novels and Stories

Idon Naira 44

Sponsored links

Musamman ga mace shiyasa duka Yan barikin dake gidansa aduk lokacinda aka cutatar dasu shine yake tsaya musu sai inda karfinsa ya qare Dan haka kowace Yar barikin dake gidan Kamar babbar Yaya suka dauki Lulu akwai Respect da bin umarni sosai a tsakaninsu dashi.

Yayi tir tareda Allah wadai da jinin umma da Haj Maryamah harma da ‘dansu Aqeel Dan kuwa shima baiji ya Burgesa ba tunda jininsu umman ne.

Kai tsaye hukuma ya daukowa Mai anguwa aka kamasa suka kwasa zuwa police akan ya siyarda gidan marainiyar Dan Shi kwata kwata ya cire Haj Maryamah a lissafin gidan tunda tafi karfinsa ga wadda ke buqata Nan Dan inganta rayuwarta data marainiyar ‘yarta Dan haka duk ubanda yakeda saka hannu a cinye gidan saiya fito

Rigimace ta balle a gurin hukuma lokacinda aka kawa zainab ta Fadi ita wacece Mai anguwa yayi tsalle yace wlh qaryane ita ba ‘yar marigayin bace Dan baisantaba…hasalima ita Yar marigayi malam adamu din itace da mahaifiyarta suka bada gidan aqara ayi masallacin da aketa kokarin ginawa a anguwar tin shekarun dasuka gabata.

Zainab najin haka jikinta yayi mummunan nauyi ta kasa cewa komai Dan kuwa Kai tsaye aka aibata sunanta daba Yar mahaifinta ba..

Riqe hawayenta tayi tana kallon Lulu Dan ya janye rigimar Amma yace wlh bazai janyeba tunda bacin suna yashigo ciki Kuma.

Case tun Yana qarami sai gashi ya girma yazama babba Dan kuwa hukuma babba tashigo ciki sbd sunan Mande ds daya fito a matsayin shine Wanda ya siya gidan.

Fitar zancen yasa rikicin yaqara girmama Dan kuwa tuni mutuncin DS yafara rawa Dan kota Ina yada zancen ake qarya da gaskia…

Ran DS yayi mummunan baci gashi tunda yaji Lulu a zancen yasan lulun bazai tsayaba saiya Gama lalata Masa suna da mutunci Dan haka take ya saki kudi aka fara neman rufe case din Amma tini Lulu ya juyar da case din zuwa gurin manyan hukuma ba Bata lokaci saiga zancen yashiga kotu.

Hankalin Zainba ya tashi sosai Dan kuwa Bata taba tunanin zata shiga rigima irin wannanba.

Ta bangare daya Sharia akeyi akan gidan mahaifinsu

Bangare daya Kuma duk masu shedan sun tabbatarda zainab din ba ‘yarsa bace yarsa dasuka sani Haj Maryamah Kuma da kansu suka bada.

Ds yayi amfani da karfinsa da dukiya akan shariar sai gashi an wankesa tareda Kama Lulu da zainab akan kokarin Bata Masa suna..

‘daga qara Lulu yayi sbd a wanke zainab da aketa aibatawa da fadin ba ‘yarsa bace..

Daqa qarar tasu yasa komai ya qara lalacewa sbd tambarin sunan karuwa daya qara hawan zainab sbd alaqarta da Lulu da siddi daketa dawainiya da MARYAMAH cikin so da kauna da kulawa Dan a hannunta Dole suka barta suna wannan yawon.

Kamasu akai aka yanke musu zaman gidan yari na wata biyu Dan tashin hankali da barnar sunan dasukaiwa DS hakama su Mai anguwa sun tsaya sun murzawa idonsu toka sukace basusan wata Yar malam adamu ba bayan haj Maryamah.

Alfarma daya aka Samar musu bayan baqar wuyar da zainab Tasha a kulle sbd Shi Lulu ya Saba

Shine zaa Kira Haj Maryamah ta bada tabbacin idan Zainab din Yar uwartace da mahaifinsu ya Haifa.

Sakon gayyata kotu Haj Maryamah tasamu Wanda ya kusan kasheta da mamaki da tashin hankali tareda wani irin firgici,

Meya hadata da zuwa kotu Kuma?

Lauyanta takira shine yayi Mata bayani Kai tsaye cewar wani Dan daudu da karuwarsa aka Kama shine akan rikicin gida tace ke Yar uwartace mahaifinku daya.

Kusan yanke jiki Haj Maryamah tayi zata Fadi Saida tayi saurin zaunawa tana Jan numfashinta dake sarkewa.

Bata taba tunanin kowa sai zainab

Haka Bata taba tunanin zainab zata zaba wannan rayuwar ta sabon Allah ba akan ta bawa umma yarta..

Umma takira muryarta ko fita batayi sosai sbd azabar da zuciyarta keyi Mata,.

Cikin ciwo da baqin ciki Mai tsanani tayiwa umma bayanin komai.

Umma ma kasa cewa komai tayi sai data Gama zaunar da zancen cikin zuciyarta tace”

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button