Hausa Novels and Stories

Idon Naira 45

Sponsored links

Lauyanta takira shine yayi Mata bayani Kai tsaye cewar wani Dan daudu da karuwarsa aka Kama shine akan rikicin gida tace ke Yar uwartace mahaifinku daya.

Kusan yanke jiki Haj Maryamah tayi zata Fadi Saida tayi saurin zaunawa tana Jan numfashinta dake sarkewa.

Bata taba tunanin kowa sai zainab,

Haka Bata taba tunanin zainab zata zaba wannan rayuwar ta sabon Allah ba akan ta bawa umma yarta..

Umma takira muryarta ko fita batayi sosai sbd azabar da zuciyarta keyi Mata,.

Cikin ciwo da baqin ciki Mai tsanani tayiwa umma bayanin komai.

Umma ma kasa cewa komai tayi sai data Gama zaunar da zancen cikin zuciyarta tace”

Rayuwar da zainab din ta zaba kenan akan ta bamu yarta ko????

Tunda ta zaba bariki Allah ya kyauta,

‘yar tata ma saita tashi da rayuwar datafi wadda take tunanin zamu Bari tayi anan ta lalacewa…

Idan ta lalata mutuncinta da sunanta to meyasa zatayi kokarin lalata Miki mutunci da suna ta hanyar cewa ta sanki?

Taje tayi rayuwarta Ina ruwanki aciki da zaa nema zubarda mutuncinki Dana familyn Mahaifin Aqeel harma Dana mijinki ayanxu Dan dukkaninsu sai mutuncinsu ya tabu idan sunanki ya bayyana a kotu.

Babban bacin Rai da tashin hankali suka shiga daga Haj Maryamah din har umma Dan kuwa yanda dangin mahaifin Aqeel suke neman hanyar cin mutuncinta suna Jin abinda zai faru zasu tarar Mata gabaki dayansu.

Umma kuwa ta tsinewa zainab yafi so ashirin tana aibatata da ‘yarta akan wannan abin,

Ita Haj Maryamah baqin ciki da damuwa ya hanata tunanin komai qarshe a gadon asibiti taqare.

Kwanciyarta asibitin yasa aka daga zaman kotun Amma dai daga baya haka aka juya lamarin lauyanta yakai takarda kotu cewar Haj Maryamah batada alaqar komai da zainab rashin lafiya bazai barta tazo kotun ba.

Dayake kotun kusan dai qaramace sai aka karanto bayanin sako daga Haj Maryamah tace batada alaqa da zainab da Lulu.

Tunda zainab take Bata taba mutuwar tsaye da mamakin Haj Maryamah ba da umma sai wannan karon,

Kasa motsi tayi sbd lamarin ya Gama shallake tunaninta,

Hawaye takeson Yi Amma takasa zuciyarta nauyi da bushewa takeyi.

Suna umma ta bada wato mahaifiyar Haj Maryamah din a gabanta aka Kira umma itama ta fada abinda haj Maryamah din tafada tareda qarin cewar ‘yar malam din ce Amma su basuda alaqa da ita,

A taqaice batai bayanin gamsashsheba

Dama jira kawai akeyi a tozartasu akan zalinci sai kawai aka yanke hukuncin komawa dasu gidan yari su Gama zaman hukuncinsu na batawa ds da Haj Maryamah suna idan sun fito zaa bawa zainab nata kason haqqin gadon Wanda Haj Maryamah ce zata Bata kudin gidan gabaki daya tunda sun bada ne ayi masallaci basuma tsaya sun bincika ko anyi dinba gashinan Mai anguwa ya Saida ya cinye kudin.

Lulu yayi baqin ciki da Dana sani matuqa na daga zancen sbd halin dayaga zainab din tashiga na wani irin quntataccen baqin ciki da nauyin zuciya,

Gabaki daya ta Dena gane komai bayan daskarewa da zuciyarta tayi Bata iya tunanin komai…

Rungume ‘yarta tayi cikeda kauna da kunci da baqin ciki da damuwa,

Tabbas a yanzu taga wani bangare na rayuwa Mai matuqar wuyar koya….

Siddi tayiwa godiya da ido sbd magana ma ayanxu wuya take Mata sbd shock daya Gama sakar da rayuwarta.

Sidda ta kula da MARYAMAH sosai tamkar ‘yarta hakama Koda yaushe itace take ziyartarsu gidan yarin har suka fito

Tunda suka dawo Shi Kansa Lulu sai rayuwarsa tayi sanyi Dan Jin kamar shine ya lalatawa zainab Yar sauran rayuwar tata da nufinln nema mata ‘yanci..

Kokarin nemawa zainab din wani gurin zama can wata anguwar daban yayi sbd taje tayi rayuwarta mai kyau itada ‘yarta.

Ranarda suka samu wani qaramin gida Mai daki daya da Palo qarami sai bandaki da kicin..

Kudinsa bai cikaba Dan haka Dole suka hakura suka dawo gida,

Kulawa da kaunarda Bata taba samu daga jinintaba Lulu yake Basu itada MARYAMAH,

Dukkanin kokarinsa yanzu akansu yakeyi sbd yakasa daukewa Kansa shine sanadin quncinta a yanzu Wanda yafi na baya,

Ta bangare daya har cikin Ransa kaunarta yakeyi a matsayin Yar uwa jininsa sbd mahaifiyarsa.

Ita kanta tasan bayan Mijinta da Aqeel to Lulu ne mutum na uku dayake kaunarta fiyeda komai Kuma yake shirye dayayi komai da inganta rayuwarta data ‘yarta.

Fafutikan nema kudi Lulu yafara sbd hadawa a kamawa zainab din can tabar Nan sbd gabaki daya Takoma Kamar dutse batada walwala da komai,

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button