Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 110

Sponsored links

Daneen Waheeda ta fada cikin zabura da ga fasa zaman da tai niyyar yi da ga can. “Wait! Wait wait Ashwaq wai nikam mi kike son fada minne haka. Jasim Akhi namu kike nufi yake shirin kashe Eshaan din komi? Ni Wihy gaba daya ma kin rikitamin lissafi”.

“Bake lissafinki ke a rikice ba, ai kowa ma yau a masarautar nan lissafinsa a rikice yake wallahi

Tiryan-tiryan ta kwashe komai na zaman kotu a yau ta fada mata kamar yanda ta saba kai mata gulmar duk wani motsin yan masarautar musamman Malikat Bushirat. Wani irin irin tashin hankali Daneen Waheeda ta shiga tana zungura manya-manyan zagi dan ita dama can mace ce masifaffiya mai zafin tsiya. A wani lokutan akance tafi kowa gado mahaifinsu a kaf yayan Tajwar Abdul-majeed. Daga can ta ce, “Gobe ki tsumayi zuwana RUMAN yar uwa wannan dambarwar ba’ayita babu ni kusa ba. Amma karki fadama kosu Mammah. Shin yaya bakar dagarki tayi ne za’a kashe mata tilon dan gwal din ta da take hura muku hanci”.

“Uhm-iuhm ai labarin kam dai babu dadin ji, amma tunda kince kina tafe ke dai kwantar min da hankalinki sai kin iso kawai”.

“Okay bara kiga naje na fara shiri ma tun yanzu. Amma da mutuniyarki zan taho dan wannan karon kam inaga sai na nunama Eshaan kwanji akan Iftihal dan ko yaki ko yaso sai ya aureta tunda dai matan sun daina mutuwar”.

“Ina tare da ke dari bisa dari kuwa. ALLAH ya kawo ku lafiya”.

Da ga haka sukai sallama Malikat Ashwag na faman sakin murmushi, dan itafa ranta fari kal da abinda ya faru a yau din.

(Ina fatan kun gane matsayin Daneen Waheeda dai. Itace kanwa ga Daneen Ammarah da Tajwar Haysam mahaifin Tajwar Eshaar ta uku ga Malikat Haseenat da mukace tana aure acan yankin larabawa. Kawace sosai ga Malikat Ashwaq, kuma yar uwa, dan kusan ma itace tai ruwa tai tsaki wajen gain Malikat Ashwag din ta auri Tajwar Haysam duk da shima dai ya sota a karan kansa. Tare sukai karatu dan haka akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu da har take tayata kishin Malikat Bushirat. A duk sanda ta sami wani sabon labari musamman akan koma bayan Malikat Bushirat sauri take taga ta sanar ma Daneen Waheeda. Shiyyasa a randa hadimanta sukazo mata da bayanin Malikat Bushirat taje wajen Malikat Haseenat akan kara auren Tajwar Eshaan tai azamar kiranta ta sanar mata dan tasan babban burin Daneen Waheeda din shine hada auren babbar diyarta da Tajwar Eshaan da suke kusan sa’anni. Ta matukar mutuwa a kansa amma shi ko kallo bata ishesa ba. Hakan yasa ita Daneen Waheeda din taso a hada auren amma Malikat Bushirat taki bada hadin kai. Dan ta fahimci so Daneen Waheeda keyi Tajwar Eshaan ya auri yarta su koma juya akalarsa data mulkin kasar ruman din. Ga kuma sharadin da UWA ta gindaya mata na karta yarda Tajwar Eshaan ya auri wata da ga cikin zuri’ar masarautar sam. Yin hakan gagarumin abune da zai rusa komai da yake komai a hanunsu. @) ALLAH yasa kun gane)

Dan daburcewa uwa taso yi, dan bata so akazo wannan gabar da wuri haka batare data Karmala shirinta ba. Anya kuwa batayi babban sakaci akan ta-kurya ba. Itama fa itace tsanin cikar nata burin data dauki tsawon shekaru tana bi matakala-matalaka domin maida murtani ga ahalin wanna masarauta baki daya.…… Ganin irin kallon da ta-kurya ke mata ne ya sata hadiye komai ta dai-daita yanayinta. Fuskarta ta sake tsukewa da gyara zaman kasaitarta. “Ta-kurya ban boye miki domin wani dalili ba, sai dan kareki da ga shagala kan al’amarin sa, amma ki sani na jima biye da Jasim da hana makircinsa tasiri kan Ajlaan. Shin bakiyi mamaki ba ne yau? Bakiyi mamakin faruwar abinda ya faru din ba ne? To bari na kaiki inda baki sani ba. Nice nan da kaina na budewa Jasim aiki yau, kuma na fara ne tun a randa ya kai kayan asiri fadar Ajlaan. Ban miki maganar bane ba dan ina son sai an kai karshe. Kuma duk abinda ya farun yau a kotu nima ina tare da ku”.

Wata irin wawuyar ajiyar zuciya Malikat Bushirat ta sauke. Gaba daya sai taji abinda ya tsaya matan a makoshi ya fada a cikin cikinta.Dari bisa dari ta yarda da zancen uwa, dan bata taba mata karya ba (hummmm). Fuskarta dauke da murmushi ta sake gurfana a gabanta. “Yanzu kam na fahimta, na fahimci komai uwa. Dama ni nasan bazaki bari na fadì ba. Amma naso ace kin sanar min tuni, da sai na daidaita rayuwa jasim,sai na kafa tarihi akansa irin wanda harara wani bazai sake kwatantawa ga Saiful- malik dina ba a wanna masarautar”

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button