Hausa Novels and Stories

Idon Naira 41

Sponsored links

Haj Maryamah na tsaye na kallonta cikeda zafi da dacin zuciya da wani mummunan nauyi a zuciyarta zainab din ta fice daga gidan rungume da yarta,

Babah dake gefen Haj Maryamah tsaye cikin shirinta tsaf na tafiya Cameroon duk jikinta neman mutuwa yakeyi da ganin samu da Rashi Dan kuwa da anbata ‘yar saita Gama biye biyenta inda takeson zuwa kafin ta Isa Cameroon din.

Masu gadin gidan dasuka San zainab tun kuruciya da girma suna kallon wannan tashin hankalin zuciyoyinsu na kunci ta tafiyarta da ‘yarta,

Babban tashin hankali da tsoronsu har ita Haj Maryamah din dawowar Aqeel ba zainab babu ‘yarta Amma Kuma zuciyarta ta rinjayeta komai ya lalace tsakaninta da qanwarta.

Zainab kuwa tafiya kadan tayi aka fara Kiran sallar asuba Duk da hakan bata tsayaba tafiya takeyi batareda tasan inda take jefa qafafuntaba sbd rufewar ido Dana zuciya.

MARYAMAH dake goye bayanta tanajinta ba bacci takeyiba sbd tashin hankalin tuni ya tadata bacci gashi babah tsabar son tafiyar yasa Ana fara rikicin ta dauketa ta tsala Mata wanka da ruwan sanyi.

Har akai sallar asuba aka fito gari yafara haske tafiya takeyi batareda tasan inane gurin zuwantaba

Idanuwanta kuwa sun kada sunyi jajir sun bushe Dan kuwa kukanta tuni ya tsaya harna zuci.

Tafiya taci gaba da Yi har asalin anguwarsu na gidan ubansu Wanda daqyar takawo kanta harta gane saidai tana shogowa layinsu Bata hango alamar gidansuba Dan kuwa wani mahaukacin gida take hangowa Mai girman gaske dayake nuni da gidan manya ne,

Anguwar gabaki daya ta canza tazama kamar anguwar Yan shiyasa sbd kalar samari da mutanen datake gani marasa kamun Kai sai Yan siye da siyarwa dasukai yawa

Kofar qaton gida data tabbatarda Nan ne gidan ubanta harma da kusan gidajen hudu da aka hade akai gida daya dasu take kallo da idanuwanta dasuke qara rinewa da tsananin qunci da radadin zuciya.

Batada komai batada kowa sai wannan gidan na ubanta Wanda takeda gado acikinsa,

Saidai Kuma wannan tsarin data tadda yasa tarasa Duk wani Dan kuzarin datake ganin ta hangowa kanta.

Guri tasamu daga gefen gidan ta zame ta zauna tareda rintse idanuwanta wani zazzabin sabon tashin hankaline yarufeta.

Wa zata tinkara da zancen Ina aka Kai gidan ubansu?

Wayema ya santa?

Maryamah da umma Kawai aka sani barema duka gidajen data sani na maqotansu babu gabaki daya anguwar ta zama kamar kasuwa kamar dandalin siyasa, ta Ina zata Samu mutumin arzkin da zata tambaya???

Shiru tayi tareda sunkuyar da Kai tana rasa tunanin kamawa,

MARYAMAH dake bayanta lafewa tayi a bayan nata sbd zazzabin wanka ruwan sanyin da babah tayi Mata tun kafin asuba hakama tagansu a inda Bata taba ganin sunzo ba Dan kusan MARYAMAH din Bata taba fitaba kullum suna gida Kamar mayu.

Ta Jima agurin zaune har Saida ta Dan dawo hayyacinta kadan kafin tafara kokarin miqewa sai kawai taji ihu da hayaniya ya gauraye koina

anguwar take ta dauki ihu anata gudu….

A tsorace take kallon mutane dake gudu ta miqe tana neman hanyar tsira saidai tuni anguwar ta dauki wani irin yamutsin fada na Yan ta’addar siyasa harda makamai dasu tiya gas.

Jefarda kayanta tayi tana neman hanyar gudu Amma babu Dan kuwa sare sare akeyi sosai

A rikice tasamu ta fada gidan dake kusada babban gidan masu gidan na neman tufewa ta fado suka rufe sunata masifa da zage zagen wannan masifa dataqi qarewa kullum haka suke a anguwar.

Itadai shirun tayi bayan babbar kofar jikinta babu inda Baya rawa sbd tashin hankali da quncin wannan rayuwar data samu kanta aciki Kuma.

Tana tsaye agurin itada wasu da yawa wainda da alama baqi ne a anguwar suma Dan hankalinsu duka a tashe yake saidai su dukkaninsu daga cikin gidan suka fito sabanin ita da shogowa tayi.

Harbe harben bindigar da akeyine yasa zuciyarta qarasa daskarewa sukuwa sauran sake shiga tsoron suka sbd tsoron kada ayi Kamen harna cikin gida tunda hukuma ce tazo ake harba bindigar.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button