Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 43

Sponsored links

A zuciyarsa ya amsa amin ɗin. Bata damu ba ta cigaba da faɗin, “Abubuwa da yawa da ke faruwa suna sake rikitamun kai, sai dai basu ne suka kawoni ba a yanzu. Yaya maganar shari’ar da aka fara?”.

“Tana nan Ammie, za kuma a ƙarasata”. Ya faɗa a hankali cikin taushin harshe.

Ajiyar zuciya ta ɗan sauke sai kuma ta ambaci sunansa. Dara-daran idanunsa ya sake saukewa a kanta da ƙyau. Itama kallonsa take cike da so da ƙauna. “Ina son tattaunawa da kai mai muhimmanci, sai dai ba’a nan ba Bin Haysam Abdul-majeed”.

Idanunsa ya lumshe ya buɗe a hankali, sunan data kirasa na ratsashi matuƙa, cike da girmamawa a gareta ya furta, “Ki yanke duk lokacin da kike buƙata ni mai jiran umarninki ne a koda yaushe”.

Ƙasaitaccen murmushi ta saki ƙaunarsa na sake ratsata. Cikin gyaɗa kai ta furta, “ALLAH ya cigaba da karemun kai, ya lulluɓeka da tarin albarka da rahamominsa marasa yankewa. Duk sanda na yanke zaka jini na barka lafiya”.

Kansa ya ɗan rissinar alamar girmamawa, kafin ya furta, “A huta lafiya”.

Bayan sallar magrib duk wani mai alaƙa da shari’ar ya kimtsa kansa a katafaren falon da akai wancan zaman farkon. Shine ƙarshen shigowa kamar a wancan zaman. Kan kowa rissine har ya zauna a inda aka tanada masa, tuni ƙamshinsa ya gama danne duk wani turare mai ƙarfi a wajen. Sai da ya gama binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya ta ƙasan ido na tsawon wasu mintuna kafin ya mula dan kansa yay gyaran murya. Dake nutsuwa kowa yay da maida hankalinsa garesa. Nan ma ya sake jan wasu mintuna biyun kafin ya ɗaura da faɗin,

 

“Naso yanke hukunci a zaman ƙarshe na Shari’ar nan a yau, sai dai masu hannu a al’amarin sun nuna mana su basa buƙatar hakan. Bazan tambayi dan mi akai yunƙurin kasheta ba a karo na biyu, sai dai zan sanar da duk wanda ya aikata ya sake shiri akan wanda yake da a baya. Kamar yanda kuka kawo ƙarar neman hakkin yunƙurin kisan jininku da tayi, nima zan shigar da ƙarar neman hakkin kashe min mata da akayi. Kamar yanda nai alƙawarin nema muku haƙƙinku matsayina na shugaba, itama zan nema mata nata hakkin Insha ALLAHU a matsayina na shugaba bayan ta samu lafiya”.

Kan babbar buta kenan, ai ba wanda suka shigar da ƙarar ba hatta masu goyon bayan Iffah kalaman Tajwar Eshaan ɗin sai da sukai musu tsawar saukar aradu na wucin gadi. A hankali Malikat Haseenat ta saki wani ƙayataccen ɓoyayyen murmushi, a zahiri kam ta katse suman zaunen da jama’ar wajen sukai ta hanyar faɗin, “Hukuncinka adalcine ga kowa koda son zuciya ta rufe idanun kowa. ALLAH ya ƙarama Zawjata-almilk lafiya, ya tona asirin wanda sukai mata wannan aikin koda a cikinmu ne”.

 

“Shugaba ya amsa tare da godiya ga Uwar masu gida abin al’faharin ƴaƴan ƙwarai. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsohon rai mai albarka baya goya marayu”. Wannan kalamai sun fito ne da ga bakin Sayeed Fayzul-haq mai yawun faɗa da yawun Tajwar Eshaan kasancewar yanzu tamkar amintaccensa yake. Babu dai wanda ya motsa a zahiri, dan tamkar duk sun tafi suman wucin gadi ne, hakan yasa ya cigaba da faɗin, “Wannan kotu mai adalci ta bada umarnin sakin Zawjata-almilk da alƙawarin bata kariya har zuwa sanda za’a yanke mata hukuncin daya dace da ita. Ta kuma saki amintattun hadiman da har yanzu bata kama da laifin komai ba, zakuma su cigaba da aikinsu da ga yau. Ta bada dama ga duk mai ƙorafi akan wannan hukunci ya faɗa a zama na gaba”.

 

Tabbas sun gama yarda cewar Tajwar Eshaan tsohon makirin kansa ne. Sannan hatsabibancin da suke jifansa da shi fa sun tabbatar da shi ɗin a tattare da shi yau. Rai ɓace kusan kowa ya fita a falon bayan fitarsa, kowa bakinsa fal da magana sai dai babu damar yinta anan kuma gudun abinda zaije ya dawo…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button