Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 116

Sponsored links

Haka suka haɗu suka lalata rayuwar yarinyar daga ƙarshe ta rasa ranta, a cikin masarautar suka bizneta har a yau kuma babu wanda ya san hakan sai ɗauka da ake yarinyar ta ɓata ne a taron bikin al’ada. Wannan shine sanadin zamowarsu inuwa ɗaya dan wannan ya basu ƙofar dinga kawoma juna mata, sai dai Miran Jasim yafi Miran Arshaan ƙwarewa a harkar, dan shi har order mata yomasa ake daga wasu ƙasashen ma🤦). Wanda ya gane na tayasa murna, wanda bai ganeba ya tsallake kawai😂🥱.

Kamar yanda su Barrister ke zaman tsammani a yau sai ga kira daga Sayeed Harun Al-rashid, sun tattauna sosai ciki harda yarjewar fita da su Babiy zuwa wata ƙasa da kuma tsananta bincike wajen gani maɓoyar Barrister Abdallah Aas kamar yanda Barrister suka tsara musu. Abu mafi saka Barrister a ƙololuwar farin ciki shine damƙa fita da su Babiy ɗin a hannunsa, amma a zahiri sai ya nuna hakan ba aikinsa bane, shifa ya bada shawara ne kawai.

 

A ɓangaren su sun nuna masa sufa sun yarda da shine, bayan shi kuma bazasu iya bama wani aikin ba gudun abinda zai je ya dawo. Bayan dai ɗan cigaba da tirjewa da ga ƙarshe Barrister ya amsa. Hakan ya musu daɗi suma, dan a nasu ɓangaren sun bashi aikinne domin ƙullama rayuwarsa, acewarsu koda ta tashi salin alin zasu zare hanunsu su barsa a ciki.

 

 

Barrister da ya gama fahimtar su da ƙudirinsu duk da basu fito sun faɗa ba yay murmushi yana mai girgiza kansa da mamakin mutanen wannan duniya mai cike da rikici. “Son kai shine tushen rugujewar kawunan mu a wannan duniyar. Mai mulki kansa kawai ya sani. Mai arziƙi kansa kawai ya sani. Talaka kansa kawai ya sani. Mai ilimi kansa kawai ya sani. Jahili kansa kawai ya sani. Iyaye kansu kawai suka sani. Matasa kansu kawai suka sani. Yaro kansa kawai ya sani. Kowa akan buƙatarsa kansa kawai yake iya kallo. Duk shaƙuwa irin ta ma’aurata akan son kansu kowanne zai iya aikata komai. Duk shaƙuwa irin ta ɗa da iyaye akan son kansu zasu iya komai. A wannan duniyar yanzu samun cikakken amini sai an tona, ka gama yarda da mutum amma akan son kansa zai iya komai. Son kai dai! Son kai dai ya rabbi. Ƴan uwa son kai fa na kawo abubuwa da yawan gaske. Yana gina hassada a zuciya, ƙyashi, zalunci, raunana imani, ƙarya, munafunci, kai komai ma wlhy, hatta shirka tana iya shiga a cikin son kai batare da mun sani ba. Ya rabbi ka ganar damu gaskiya tun kan ta nisanta a kunnuwanmu da idanunmu

 

………..Babu kwanciyar hankali gasu Kaka, dan har yanzu basu sami bakin zaren jin komai ba game da wadda aka rasa a cikin matan Shahan-shan. Ga tashin hankalin ɓatan Barrister dan sun je har gidansa amma a rufe alamar iyalansa ma dai basa nan. Acewar makwafta kuma dai anzo an

kwashesune a cikin dare, yau kusan kwanaki takwas kenan. A lissafinsu kuma ya kama randa Barrister ya ɓata kenan. Zuciyar kaka ingizashi take kan abubuwa masu yawan gaske amma yana gocewa, dan duk tsanani yayi alƙawarin dogaro ga ALLAH majiɓincin al’amuran bayi a kowane tsanani da sauƙi. Kwanansa ɗaya ya juya ƙauyen Jumna, dan yasan ya baro su Iyyani a tashin hankali.

Ilai kuwa koda ya koma sai ya samesu a birkice, dan suma dai zuwa yanzu labarin halin da ƙasar ke ciki ya isa har kunnuwansu. Ummu tayi kuka har hawaye sun daina zuba. Ta gama sadakarwa ta rasa autarta itama. Dama ta jima da fidda rai ga su Babiy tuni. Kaka rasa ma mizai ce da su yayi, dan shima dai nasa kan a zafafe yake. Sai kawai ya shige ɗakinsa ya rufe kansa yana mai safa da marwa…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button