Hausa Novels and Stories

Idon Naira 26

Sponsored links

Ayau Aqeel ya tabbatar Mata da Bayan shi batada kowa sai rayuwa dazata samu gaba a gidan wannan auren wanda take fatar ya zamar Mata alkhairi sbd yanda su umma da Haj maryamah suka juya Mata baya tareda ficewa daga rayuwarta suka juya mata baya a lokacinda yakamata ace sune suka tsaya mata.

Ayau data shiga sabuwar rayuwa Mai girma ‘danta ne kawai tareda ita..

Batai kukaba saida Aqeel din yayi Mata wasu maganganu masu Kama da nasiha.. kenan shine zaiyi mata nasihar aurenta..danta?

Wanda aka Haifa gabanta?

Wani kukan mara sauti takuma saki zuciyarta na sake nauyi..

Babu Wanda yasan menene qaddarar dake jiransa agabansa,

Babu Wanda yasa menene sanadinsa na alkhairi ko sabaninsa,

Ashe Aqeel shine sanadinta na matsawa da Isa ga wani matakin na rayuwa Bata saniba,..

Tana fatar yanda ya zama Sila Kuma sanadin shigarta wannan rayuwar ta aure

Allah yasa wannan auren ya zama Sila Kuma sanadin nasa farin cikin da Lada Mai girma tareda girban alkhairin Hakan a gaba.

Sabuwar Mai aikin gidan Zainab tabarwa komai Tunda Haj maryamah din Bata gari Kuma tayita Kiran wayoyinsu daga ita har umma Amma Babu Mai daga kiranta,

Har gwara umma Tana dauka wani lokacin Amma Bata amsa Mata cikin dadi saidai fada.

Aqeel da Kansa ya dauketa a motarsa duk da Babu wani nisa da anguwar yakaita qaramin gidanta da Malam din ya Kama haha Mai Palo daya daki daya sai bandaki da babban palon karatu Wanda mutanensa zasu ringa daukar karatu sbd yanzu kam bazaije gidan kowaba bada karatun saidai azo Tunda Daman rashin iyali ga malami kamarsa yasa bayason ana zuwa gunsa din daukar karatu saidai yaje can yabada.

Barema tun rasuwar Mai dakinsa Yana qarqashin kulawar Alh Asad Dan haka tuni a anguwar yake zaune qaramin boys quarters din da aka Gina Masa ta wajen gidan

Yanzu Kuma gurin bazai zaunu da iyaliba Dan Babu sakewa sosai.

Yanzu anan din hayace ya Kama sbd Zainab tasamu kanta a sabon guri ko zatayi saurin sakewa tayi rayuwa kamar kowa cikin walwalarta da kwanciyar hankali.

Koda suka Zo Malam sanda din Yana palon karatunsa da wasu baqin Anguwar dasukazo su gaisa sbd sun Dan San juna

Aqeel din bai shigaba Yana ajiyeta yajuya ya tafi sbd baisan mezai shiga yayiba Dan ko kawowar wani irin nauyin lamarin yakeji to Amma Tunda baida Wanda zai Mata Dole shine zaiyiwa Mamin tasa.

  1. Zainab tasamu kyakkyawar tarba da kulawa irin dattijon dayasan Kansa daga mijinta Malam Sanda,

Da farko taso tsorata da lamarin Amma Kuma ganin Babu gudu ba ja da baya Tunda sukai Kuma daga shidai ba qaramin mutum bane hakama itama ba qanqanuwar yarinya bace Dan haka ta cire komai aranta ta Bari Kai tsaye ya maidata sahun Mata batareda wahalarwaba.

Shi Kansa malam Sanda sosai tasake shiga ransa ya Yaba da nutsuwarta Dan kuwa komai nata na nutsuwa ne,

A macenta cikakkiya ya sameta duk da ta jima gida hakama ga aikin wahala Amma still dai mutuncinta na Nan koba kamar na budurwa danya sharaf ba.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button