Hausa Novels and Stories

Furar Danko Page 3 Hausa Novel

Sponsored links

Ƙyakykyawan saurayi ne chocolate color mai cikar kamala da nutsuwa. Baida hayaniya a yanayinsa na zahiri bai kuma da fara’a sam akan fuska. A halittar jiki da cikar kamalar fuska mai nuna barazana ko maƙiyinsa dole ne ya yarda yaci wannan suna na *_Smart_*. Maimakon kallon wadda yaron yay nuni da kira Aunty Lulu sai ya ɗaga shi cak ya sauke ƙasa kawai tamkar ma baiji ba. Da gudu kuwa yaron ya nufeta cikin farin ciki da ihun kwakwazo yana mata oyoyo Aunty Lu.

 

A hankali ta saki murmushi daya ƙara ƙawata ƙyawun fuskarta a karo na farko tana mai tsayawa cak har yaron ya ƙaraso gareta. Yana dab da zuwa gareta ta ajiye laptop ɗinta a saman akwatin dake ɗayan hanunta ta tarbi yaron. Dai-dai nan MM Atik Kumo da ya biyota ya ƙaraso wajen. A hankali murmushin dake a saman fuskarta ya fara ɓacewa, cikin ƙanƙanin lokaci fuskarta ta koma asalin yanda take. Cikin fushi da tsananin ɓacin rai ta watsa masa kallon nan nata na raini da wulaƙanci. A fusace ta furta, “Halan kai babu zuciya a ƙirjinka? Nifa a duniya na tsani wasu *_MAYUN MAZA_* wlhy”.

 

 

_(Mayun Maza!!!)_ Kalmar tai wani irin amsa kuwwar maimaita kanta a cikin kunnensa duk da bashi aka faɗawa ba. A hankali ya ɗago fararen idanunsa masu girma karan farko ya saukesu a kanta. Dai-dai nan itama cikin tsiwa ta nuna MM Atik Kumo da yatsanta mai ɗauke da farce data ƙara a duk farautan hannuwan nata biyu da ƙafafu. Ɗauke idanun nasa yay da sauri wani irin sukar baƙin ciki na tokare ƙirjinsa, a duniya ya tsani mace irinta da zata iya saka kowane irin kaya ta fita kamar yanda take, tun daga samanta har ƙasa babu suffar mace musilma bahaushiya a tare da ita. Siririn tsaki yaja yana sake tamke fuska sai dai kunnensa na garesu.

Itako da bata san yanayi ba yi take kamar zata tsole ma MM Atik Kumo ido da yatsanta data nunashi da shi. A cikin kaushin murya take faɗin, “Wlhy! wlhy! idan ka sake gigin zuwa gabana a karo na uku saina wulaƙantaka a wajen nan, mafi munin wulaƙanci, na yaga maka rigar mutunci kuma, danni *_FURAR DANƘO CE, A SHEKARA ANA DAMU BA FARAU-FARAU!!._* Mtsowww ban san damuwa ok”. Fuuuu ta figi hannun yaron da ya tsaya kawai yana kallonsu tare da lap-top ɗin ta tai gaba batare data ja akwatin ba.

 

 

Babu alamar gargaɗin nata ya zafi MM Atik Kumo, dan wani murmushin ma ya saki da bin ƙugunta da kallo a ransa yana maimaita kalmar _(Furar danƙo a shekara ana damaki baki farau-farau)._ Wani shegen yawu ya haɗiye yana lumshe idanunsa da suka wani ƙanƙance tare da lashe lips ɗinsa.

 

A gaban motar da Uncle Smart ya ke tsaye taja birki, cikin hucin takaici tai masa kallon sama da ƙasa fuska a yatsine. “Kai kuma malam haka ake aiki a garinku? Kana kallon mutane da kaya bazakaje ka amsa ba!!?”.

 

Idan motar nan ta motsa to shima da ke jingine a jikinta ya motsa. Wani irin baƙin cikine ya sake turniƙe mata zuciya, “Kai sakarai kai waye da har ina maka magana zaka ɗauke mun kai? kan bala’i…..!”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button