Hausa Novels and Stories

Idon Naira 29

Sponsored links

Da asuba ma jikin nasa tashi yayi sosai

ciwon cikin Mai tsanani ya dawo Dan haka Dole tasamo abun Hawa suka Kuma komawa asibitin saidai Basu samu ganin likitaba haka suka dawo sbd kamar kada su nufa asibiti ciwon cikin yakoma ya kwanta.

Suna dawowa itama zazzabin takeji sbd yanayinta na juna biyu ga damuwa da tashin hankalin ciwon mijinta.

Ganin Yana ciwon ciki yasata dama kunun tsamiya ta zuba a flask saita dafa farar shinkafa kawai da Mai da Dan yaji sbd ita kanta batada wani apatite na cin abinci

Haka ya wuni a kwance Yana bacci Mai nauyi sosai sai yamma ciwon yakuma tadashi daqyar yayi sallolinsa yasha kunun kadan Amma Sam bai zauna a cikinba ya amayar duka take qarfinsa yayi qasa sosai.

Duk inda hankalin Zainab yake ya tashi Dan haka ta zauna gabansa bayan kuka Mara sauti Babu abinda takeyi sbd Babu wata mafita.

Batasan me zatayiba Kuma

Aqeel ne gatanta harma Dana malam din Amma Kuma batason lalata Masa komai tsakaninsa da mahaifiyarsa,

Idan takirasa komaima faruwa zaiyi Dan haka saita zauna tanaci gaba da kukanta sbd duka maganin da aka rubuto Babu Wanda Basu sayaba hakama babu Wanda bayasha

Gashi sunkoma asibitin Amma Basu samu ganin likitaba ance sai emergency patient kawai zaa iya gani,

Su ankasa yarda da emergency dinne.

A wunin azabar ciwon yafi na kullum Dan haka take malam din gabaki dayansa ya sauya lokaci daya kamaninnsa duk suka sauya.

Tsananin tsoron dake zuciyar Zainab yasa kukan natama ya tsaya qarfe itama zabgewa Tai lokaci daya.

Dare nayi jikinsa yayi tsananin da bazata iya kasa Kiran Aqeel ba sai gashi Tana Kira wayar tasa a kashe

Take jikinta ya dauki rawa Tana fashewa da wani irin kuka.

Da Kansa ya kamashi Mamin tasa ta Kama Masa suka kaisa mota yaja motar suka nufi Babbar private asibin kakarsa Haj Kaka

Suna Isa asibiti aka karbesa da gaggawa sbd yafara nisa sosai.

Waje aka koro Aqeel din da Maminsa suka zauna kowannensu hankali tashe

Bayan fata da adduar samun saukinsa Babu abinda kowannensu yake kitsawa cikin ransa.

Zainab gabaki daya jikinta yagama saki da komai

Zuciyarta ta riga tayi nauyi Jin take kamar kirjinta bazai dauki nauyin zuciyar ba.

Zainab Tunda ta zaunar da duwawunta kan gurin zama ta sunkuyar da kanta Bata sake motsiba bare iya magana

Zuciyarta ta Dena harbawa da qarfi sbd rashin kuzarin jikinta dayayi sanyi matuqa da Hakan tayi shiru Tana jiran hukuncin Allah akansu.

Aqeel ma kallo daya yayi Mata ya fahimci tsananin sanyi da sarewar datayi Dan haka shima ya kasa magana suka barwa Allah komai.

Haj maryamah daketa faman kiransa a waya bai dagaba sbd wayar ya Barta a mota da Haka take Hankalinta ya tashi itama sbd taji fitar motarsa da daddaren.

Takira Haj Kaka Amma ance baya can gidan Dan Haka Kai tsaye insha Allah Yana gurin Zainab.

Wurgi tayi da wayarta kan gado tareda Dan rufe ido Tana dafe goshinta qaramin tsoki na fitowa bakinta

A asibiti kuwa komai ya lalacewa su Zainab da likitoci sukaita fada akan rashin kawosa asibiti da wuri yaga likita

Zainab dai Bata iya cewa komaiba saidai AQEEL dinne kawai yake iya Basu hakuri Yana sanar musu da shima bai sani rashin lafiyar tasaba.

Tun suna saka ran Jin wani bayani daga likitoci bayan tarin magani da allurai da drips dasuka rubuta aka siyo Babu abinda suka sanar musu sbd malam din dai su kansu Basu samu ya farfadoba Amma dai suna saka ran farfadowar tasa Koda tsakiyar dare ne

Anan suka cinye Daren zaune kofar dakin emergency babu Mai iya doguwar magana acikinsu…

Qarfe biyar na asuba Allah ya karbi ran malam Umar sanda Bayan ya bude idanuwansa akan Zainab Aqeel dake gefen.,

Kallonta kawai yayi tsawon sakanni kamarma baisan meyake kalloba sbd kwata kwata baya hayyacinsa na lafiya,

Wurgi tayi da wayarta kan gado tareda Dan rufe ido Tana dafe goshinta qaramin tsoki na fitowa bakinta.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button