Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 67

Sponsored links

Takun da baifi uku ba Kaka ya juyo ya bisa da kallo, kamar a bazata saurayin ya tsinkayi muryarsa na faɗin, “Jumna zanje”.

Yi yay tamkar bai jisa ba. Hakan yasa Kaka sake ɗaga murya amma ya cigaba da sharesa shima. Yana ƙoƙarin shiga motarsa Kaka daya biyosa a baya yace, “Haba ɗan nan baka jini bane?”.

“Sarai na jika Baba. Na fahimci ba tafiyar zakai ba, ba kuma hurimina bane tilastaka”.

A karan farko kaka ya saki murmushi. “ALLAH sarki, to ayima tsoho haƙuri ɗana”.

“Baba kamin laifin komai ba ALLAH, ai aikina ne. Dama naji kana sanarma wancan ne ni kuma hanyatace shiyyasa ma naje gareka. Zanje ƙauyen Yamanu ne dama”.

“A Alhamdullah, lallai hanyarmu ɗaya Bara na ɗakko kayana.”

Mutum biyu kawai saurayin ya ƙara ɗauka bayan kaka suka ɗauki hanya. Hakan baisa kaka ya ji wani zargi game da shi ba. Sai ma hira da suka dingayi kai kace sun san juna. Bayan sauke mutum biyun daya ɗakko har ƙofar gida ya kai Kaka. Yaji matuƙar jin daɗin wannan karamci dan haka yay masa tayin shiga ciki yasha ruwa. Saurayin ya ɗan nuna tirjewa amma Kaka ya janye ra’ayinsa a dole ya bisa suka shiga, sai dai dama a ransa hakan yake fata.

Ummu na zaune a tsakar gida ita da Iyyani, ta rame matuƙa tayi duhu irin na wanda ya shiga damuwa. Tamkar an sare gwiyawun Kaka ya ƙarasa shiga idanunsa akan Ummu data tsurama bayansa ido. Iyyani ma jiki a sanyaye ta miƙe dan tasan komai tunda kullum sai sunyi waya da Kaka. Itace tai ƙarfin halin masa sannu da zuwa. Ya amsa a sanyaye yana waiga bayansa.

“Yaro shigo mana”.

Kaka ya faɗa domin samawa Ummu nutsuwa. Da sallama saurayin ya shiga. Ummu tai ƙasa da kanta a hankali.

Bayan sun gama zama a tabarmar da Iyyani ta shimfiɗa musu saurayin ya fara gaishe da Ummu. Bata amsa ba, hakan ya sakashi shan jinin jikinsa yay shiru a sanyaye. Iyyani data sake kawo musu ruwa ce ta amsa masa da “Bata magana yaro”.

“ALLAH sarki” ya faɗa cikin sauke ajiyar zuciya ita ya gaisheta. Da kulawa ta amsa masa dukkan hankalinta a kan Kaka dake kallon Ummu tamkar ya samu television. Ummu da hawaye suka cikama ido ta miƙe a hankali, ɗaki ta shige duk suka bita da kallo. Kaka baice komai ba hakama Iyyani data zarce kitchen sai gata da kwanon abinci…

Tamkar raƙumi da akala haka Iffah ke tafiya bisa jagorancin Malikat Haseenat. Kasancewar dare ne babu yawaitar hadimai masu hidima. Sai dai masu tsaro tako ina kai kace zasu iya kare ran wanda suke tsaye a dalilinsa daga ziyartar mutuwa. Tsirarun hadiman da suka samu nata zubewa kwasar gaisuwa, Malikat Haseenat ce kawai ke iya jinsu da ganinsu. Iffah dake ta faman sauke ajiyar zuciya da al’ajabin dukiyar dake narke a wannan gini ji take komai ya ƙwace mata. Ta kasa fasalta komai ta kasa auna komai a ma’aunin rinjayen aikin zuciya dana ƙwaƙwalwa….

“Bismillah”.

Malikat Haseenat ta katse mata ɗimuwar da take ciki ta hanyar nuna mata ɗaya daga cikin kujerun katafaren falon mai cike da abubuwan da bazasu lissafu ba. Da gaske Iffah bazata ma iya tantance yanda akai ƙafarta tazo nan ɗin ba.

Komai Malikat Haseenat batace ba, dan ta gama karance ɗimuwar dake jagorantar fitar numfashin Iffah. Amintattun Hadiman dake a falon na uku suka zube gaban Malikat Haseenat kawunansu a ƙasa. Hannu kawai ta iya ɗaga musu. Babu buƙatar sai ta faɗa abinda tazo dan shi, shugaban hadiman dake a wannan falon ya miƙe zuwa ga landline domin isar da saƙon zuwanta…

“Tsahon rai da lafiya su tabbata ga Uwa a garemu, shugaban na tsumayen isarku a falon sama”.

Shiru malikat Haseenat batace komai ba. Yayinda Iffah da zuciyarta ke luguden ke saurarensu cikin juyewar tunaninta da har yanzu bai dawo dai-dai ba. Kusan mintuna uku Malikat Haseenat taima Iffah nuni data miƙe, ita kuma ta birka wheelchair ɗinta suka shiga lifter. Mintuna biyu ne kacal suka iso da su katafaren falon da yafi kowane falo ƙawatuwa a kaf daular ma da sashen kawai ba. Iffah tai ƙoƙarin danne harbawar ƙirjinta sakamakon tozali da wanda ke zaune a falon cikin zama na ƙasaita da izzar masu mulki. Tafiya take tamkar hawainiya saboda tsabar kasala da sanyin gaɓɓai. Zuwa yanzu wannan fuskar bata aljani take fassarata ba, neman ƙarin bayani take a kanta a dalilin ganinta a waje biyu da basu da alaƙa da juna a zahirin rayuwa…

Tajwar Eshaan da ke kishingiɗe bisa ƙayataccen kujera mai kama da wani madaidaicin gado gabansa butar shayi ce da ƙaramin kofin da alamu suka nuna yasha ko zai sha, idanunsa ya janye daga kan television da yake kallo ya ɗan waigo garesu. Akan Iffah dake tafiya tamkar hawainiya ya fara saukewa, fuskarta a sakaye take, hanunta dake riƙe da rigar jikinta ne ta ƙasa kawai a bayyane. Janye wa yay ya maida ga Malikat Haseenat. Ta ɗan hararesa da salon kulawa da nuna damuwa. Idanun ya janye a sannu daga kanta itama yana sakin kasaitaccen murmushi….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button